- Gudu da mai ruwa, ba ya hana jin ƙishirwa.
- Hankali alƙalin jiki.
- Kulkin da aka hori giwa da shi, idan aka hori san gida da shi sai yanka.
- Duk gyangyaɗin kunama, ba da garaje akan kai hanu a taɓa ta ba.
- Gurgu yana gani akan sari ice a buge shi da shi.
- Farar riga ba ta shafa wa 'yar'uwarta shuni.
- Ko biri ya zama wawa, ba ya yi wasa da itaciyar ƙaya ba.
- Da kaɗa-kaɗan matankaɗi kan shiga gora.
- Karen aro karen banza ko an iza shi ba ya kama nama ba.
- Girma ya faɗi raƙumi ya shanye ruwan kaji, ya ce ba girma ba ne ya faɗi ba a dai kyauta ba ne.
- Tsaurin ido, neman bashi wurin wanda ke binka ba shi.
- Duk girman ido, ba ya kallon ƙeyansa.
- Hanci bai san daɗin gishiri ba.
- Rumbun kwaɗayi, da baƙin ciki yake cika.
- Duk son a saya na ɗan ga-ruwa, ba ya bi layin da ake gobara ba.
- Ba abin murna ba ne, kaza ta ga ana jan hanjin 'yar'uwarta.
- Zama kusa da rumbu, ba ya kawo ƙoshi.
- In giya biyu na faɗa, ciyayin wurin ake tausayi.
- Furar danƙo a shekara damu ba ko farau-farau.
Babi Na Ɗaya Waƙoƙin Baka Mandawari (2004) ya nuna cewa, waƙoƙin da ake da su na Hausa sun rabu gida biyu; akwai waƙa sanan akwai waƙe. Ya bayyana waƙa da cewa, “Ita waƙa dai wata aba ce wadda mawaƙa ke rerawa da nufin nishaɗantar da mai saurare tare da taimakon abin kiɗa kamar kalangu ko gurmi ko kuma kuge da sauransu”. Matsayin Kiɗa A Waƙar Baka Duk inda ka ji kiɗa, ana neman a wataya ne, watayawa kuwa ɗaya ne daga cikin dalilan da ke sanyawa a yi waƙar baka, saboda haka, duk inda aka yi kiɗa so ake yi a ɗan sarara. Kiɗa kuwa yana sauya “waƙe” daga “waƙe” zuwa waƙa. Da farko dai mawaƙa kan kwatanta kiɗansu gwargwadon yadda zai dace da launin waƙar da suke yi, wani loakci ma ka ji kamar kana iya fassara abin da kiɗan yake nufi, musamman ma irin kiɗin masu amfani da tsarkiya da busa. A waƙar baka ta Hausa, makaɗa suna alamta abubuwa da yawa da kiɗa. Da fari wasu kan alamta cewa ga waƙa za a fara ta hanyar jinjina ganga, kowa ya ji kaɗan kafin a furt...
Comments
Post a Comment