Aiki da hankali ya fi aiki da agogo:
Akwai wani baƙo da ya taɓa ziyartar wani Sarki, sai kullum ya zo fada ya zauna in an tashi ya tashi ya tafi. Rannan sai Sarki ya ce da shi wai kai meye aikin ka? Sai baƙo ya ce shi aikinsa, shi ne aiki da hankali!
Sarki ya ce ni ko ina so ka yi mani aiki da hankali. Baƙo ya ce shi ke nan. Aka kwashi watannan Sarki bai ga ya ce da shi komai ba, har Sarki ya gaji ya tambaye shi. Sai mai aiki da hankali ya ce, idan na yi ma aiki da hankalina za ka sa akashe ni ne! Sarki ya ce aikin banza daga kawai ka yi abin da na saka sai in sa a kashe ka? Ina nan ina jirar ka ka yi aikin da hankalin naka.
Sarki ya takura wa ma aiki da hankali sai mai aiki da hankali ya ce, to, a tara malamai. Sarki ya rantse da cewa duk abin da ya faɗi ba zai yi masa komai ba. Sarki ya sa aka tara Malamai ya yi rantsuwa a kan cewa duk abin da mai aiki hankali ya faɗi bai da wata uƙuba.
Sai mai aiki da hankali ya ce, ran nan muna zaune ka sa an je an sayo dawakai har guda ɗari, amma da aka kawo sai dai kawai ka faɗi yadda kake so a yi da su amma har aka raba ba ka je ka ga yadda suke ba bare kalarsu.
Sannan rannan kana cikin gida sai ga shi za a wuce da sa za a je da shi kwata a yanka, da jin ihun yara ka fito ko da ka yi arba da saniyar sai ka ce wannan san girmar banza ne da shi amma ba zai yi nama ba, haka ko aka yi da aka yanka san bai yi wani nama ba.
Sai kuma rannan aka ƙara zuwa da wani san za a wuce, shi ma nan da nan ka fita da gani san sai ka ce, duk da rashin girmarsa, san zai yi mai da nama, na bi, kuma tabbas abin da ka faɗi gaskiya ce.
To, aiki da hankalin da na yi a nan, shi ne, duk yadda aka yi kai ba ɗan Sarki ba ne ko kuma kai ba ka gaji sarauta ba, don ba yadda za a yi wanda ke da nasaba da sarauta ya sa a kawo dawakai amma ya kasa zuwa ya ga yadda suke, sai dai ya faɗi yadda za a yi da su, amma da jin za a wuce da saniya ya yi zumut ya fita ya gani, ni a aiki da hankalina, ka fi nasaba da fawa ko sarkin fawa.
Da jin wannan jawabi sai Sarkin ya harzaƙa amma ya yi damo ko da ya shiga gida ya sami mahaifiyarsa ya faɗa mata abin da ya faru ya kuma taƙura mata kan ta faɗa masa gaskiya, sai ta ce masa shi ɗan Sarkin Fawa garin ne, don ainihin Sarkin da yake ganin shi ne babansa baya haihuwa amma bai sani ba, shi ne idan baya nan sai ta riƙa zuwa wurin sarkin fawa.
Comments
Post a Comment