29/11/2019
Duk wanda ya ɗauki namiji uba, zai mutu maraya.
Duk wadda ta ɗauki namiji uba, za ta mutu marainiya.
Duk wanda ya ɗauki namiji uba, za ta mutu ba a mata gara ba.
Namiji ba ɗan goyo ba.
Salon Tsari Na Karin Maganar
Duk waɗannan karin maganganu ne na Hausawa kuma sun hau kan tsari. Idan aka duba za a ga karin magana ce mai ɓarayi biyu:
Sashen farko: Duk wadda ta ɗauki namiji uba, = gaɓoɓi 11
Sashe na biyu: Za ta mutu mareniya. = Gaɓoɓi 8
Duk wadda ta ɗauki namiji uba/ za ta mutu marainiya. 11/8
Wannan salo ne da zubi na karin maganar Hausa, wani lokaci za a ga sashen dama ya fi yawan gaɓoɓi, wani lokaci kuma hagu ya fi yawa, a wasu wuraren kuma su zama ɗaya, amma kuma za a ga ma’ana ta tafi yadda ake so ba tare da ta ɓaci ba.
Yadda Ake Amfani Da Karin Maganar
Mata su suka fi amfani da wannan karin maganar, kuma suna amfani da ita ne a lokacin da namiji ya yi masu ba daidai ba, sai su faɗi wannan karin maganar da nufin su nuna masa cewa, ai da ma suna sane da cewa zai aikata masu wani abin da ba zai yi musu daɗi ba. Haka kuma, idan mace ta ga ’yar’uwarta na ƙoƙarin shige wa namiji, a nan ma sukan yi wa junansu matashiya da cewa, namiji fa ba ɗan goyo ba ne, don haka ba a ɗaukarsa uba. Watau ta rage abubuwan da take yi.
Za a iya fassara wannan karin maganar da karin maganganu irin su: “Duk yadda ka yi da jaki sai ya ci kara” ko “Mai hali ba ya barin halinsa”.
Sassauƙar Ma’ana:
Wannan karin magana ce da mata ke amfani da ita domin su nuna cewa namiji ba shi da kirki a kowane lokaci, kuma koman daren daɗewa sai ya yi wa mace rashin kirki. Ƙarshen rashin kirkin ɗa namiji a wajen ’ya mace shi ne ya yi mata kishiya ko ya sake ta ko ya mayar da ita bora. Watau ya daina kyautata mata.
Zuzzurfan Ma’ana
Ma’anar ɗaukar namiji uba shi ne, yadda mace za ta dage ta yi wa mijinta biyayya da yi masa hidima da ƙarfinta da dukiyarta da duk wani abin da ta mallaka da sunan yi don Allah da neman lada da sakamako a wurin Allah. Wani lokaci ma da nufin a zauna lafiya kar ya yi maganar kishiya ko kar ya rabu da ita watau ya sake ta.
Wata ma za ka ga ’yar mai kuɗi ce ko ’yar sarauta ce za ta ga wani talaka ta so shi, amma da ya murmure ya ga ya taka ƙasa sai ya yi mata kishiya. To, su mata wannan shi ne butulcin ɗa namiji, kuma da shi ne suke cewa namiji ba ɗan goyo ba ne. Watau ba a mara masa baya, saboda duk yadda ka taimake shi sai ya yi maka butulci, sai ya watsa maka ƙasa a ido.
Wata Ma’anar Kuma
Wannan karin maganar tana nuna cewa, al’ummar Hausawa sun yarda da auratayya, kuma mace tana kyautata wa mijinta, sai dai yadda mazan ke tu’ammuli da matansu ne, matan ba su godewa. Kuma akwai batun kishiya da saki a karin maganar, duk da cewa ba su fito ƙarara ba, amma a wurin mata kishiya da saki shi ne abin da suka ƙi a wrin namiji, kuma shi ke kawo saɓani a tsakaninsu. Sannan akwai batun maraici -watau wanda ubansa ya mutu- a ƙasar Hausa. Haka kuma a ɗaya karin maganar akwai batun gara wadda ake yi wa mace in ta yi aure ko in ta haihu. Watau al’ummar Hausawa masu ƙoƙarin taimaka wa wanda yake da buƙata ne, miji hidima ce ta same shi don haka sai a taimaka masa da gara.
Siyasar Rayuwa
Idan kuma an koma ga siyasar rayuwa, wannan karin maganar tana koya mana cewa, akwai wasu nau’o’in mutane da idan mu’amala ta haɗa ka da su, to, ka yi shiri da taka tsantsan, kuma ka kwana da sanin cewa duk yadda ka yi ƙoƙari wurin kyautata masu sai sun ɓata maka, don haka tun wuri ka ci maganin zama da su.
Comments
Post a Comment