Babi Na Ɗaya
Waƙoƙin Baka
Mandawari (2004) ya nuna cewa,
waƙoƙin da ake da su na Hausa sun rabu gida biyu; akwai waƙa sanan akwai waƙe.
Ya bayyana waƙa da cewa, “Ita waƙa dai wata aba ce wadda mawaƙa ke rerawa da
nufin nishaɗantar da mai saurare tare da taimakon abin kiɗa kamar kalangu ko
gurmi ko kuma kuge da sauransu”.
Matsayin Kiɗa A Waƙar Baka
Duk inda ka ji kiɗa, ana neman
a wataya ne, watayawa kuwa ɗaya ne daga cikin dalilan da ke sanyawa a yi waƙar
baka, saboda haka, duk inda aka yi kiɗa so ake yi a ɗan sarara. Kiɗa kuwa yana
sauya “waƙe” daga “waƙe” zuwa waƙa.
Da farko dai mawaƙa kan kwatanta
kiɗansu gwargwadon yadda zai dace da launin waƙar da suke yi, wani loakci ma ka
ji kamar kana iya fassara abin da kiɗan yake nufi, musamman ma irin kiɗin masu
amfani da tsarkiya da busa. A waƙar baka ta Hausa, makaɗa suna alamta abubuwa da
yawa da kiɗa. Da fari wasu kan alamta cewa ga waƙa za a fara ta hanyar jinjina
ganga, kowa ya ji kaɗan kafin a furta amshin waƙar ko tirkenta. Makaɗa irin su
Musa Ɗanƙwairo da su Barmani Coje da sauransu suna amfani da irin wannan salo.
Wani lokaci kuma da tashin
kiɗan da waƙar suna tashi ne tare ne, kana daga baya sai a ɗan sassauta kiɗan,
sai waƙa ta biyo baya.
Wasu maɗan kuma ba su faye ba
kiɗa mahimmanci ba, in suna waƙa sai ka ji kiɗan can baya-baya ake jin sa,
kamar su Narrambaɗa suna amfani da wannan salo.
Makaɗan baka sukan alamta wani
wuri da suke so su nuna matuƙar yabo ta hanyar yi wa makaɗansu ishara cewa su
jinjina ganga jinjinawa ta musamma, ta yadda za ka ji kiɗan ya yi sama domin
tsima wanda ake yabo. Suna da kalmomi na musamman da suke amfani da su domin yi
wa masu kiɗansu ishara. Wani lokaci sukan ce “ku ba mu tambura” ko “ku jinjina
mana…” ire-iren waɗannan kalmomin suke amfani da su.
Mawaƙa suna amfani da kiɗa
domin nuna irin mutumin da ake yi wa waƙa. Idan kiɗan fada ne, kai da ji za ka
gamsu da cewa wannan waƙar fada ce, haka ma kiɗan maza ko na ’yan bori ko
malamai da makamantansu, duk da jin launin kiɗan da ake yi za ka shaida haka.
Sannan mawaƙa suna amfani da
kiɗa domin su nuna waƙa ta zo ƙarshe, wani lokaci za ka ji an yi kiɗin ya yi
ƙasa-ƙasa ko wani salo na daban, ko ma ka ji waƙar ta ƙare sai a ɗan buga
gangan na wani ɗan lokaci shi ke nan an gama.
Matsayin Tirke A Waƙar Baka
Tirke shi ne musabbabi ko
dalilin da ya sa aka yi waƙa. A rubutacciyar waƙa ana kiran tirke da jigo. A
waƙar baka mawaƙa suna yin waƙoƙinsu ne a kan mabambata tiraku. Wata waƙar da
ji ka san tirken yabo ce, wata zuga wata zambo, wata ta’aziyya, wata tarihi
take bayarwa, wata kuma waƙa ce ta soyayya. Wata faɗakarwa, wata tirkenta na
addini ne, wata kuwa mai ita ne ke wasa kansa da kansa.
Wasu mawaƙan suka ambaci tirkensu ne kafin a shiga waƙa, wasu kuwa
amshinsu shi ne tirken waƙar da suke yi. Sai dai akwai ƙananan tiraku a kowane
waƙa. Misali a waƙar fada, ana cikin yabo, sai kuma a gauraya da zambo ko
godiya ga wasu da ba su ake yi wa waƙar ba.
Matsayin Gindin Waƙa Ko Amshi
A waƙar baka da ke da amshi,
gindin waƙa, shi ne amshin nan da ’yan amshi ke maimaita shi a duk lokacin da
uban waƙa ya nufasa ko ya ba su daman yin haka. Amshi shi ke shiga tsakanin ɗan
waƙa da ɗan waƙa domin ya rabe su.
Amshi shi ma’auni ne na layukan
waƙar baka. Don haka, kowane layi na waƙa yana bin irin raujin da amshin waƙar
ya bi ne.
Amshi : Bābbān jīgō nǎ Yārǐ,
: Ǔbān Shāmǎkǐ
: Tūrě hāushī.
Jagora : Kai ita gaskiya,
: Gaskiya ce,
: Tun da ilimi ya ɗaram ma jahilci,
: Alferi ya ɗara mugunta,
: Mai tsafta ya ɗara ƙazami.
To irin haka mawaƙi ke ƙoƙarin
tsarewa, duk yadda ta kai ta kawo shi dai ta riƙa bin raujin amshinsa.
Matsayin Amshi A Waƙar Baka
A waƙoƙin baka na Hausa, amshi
abu ne na musamman, wanda mutane na musamman ke yi domin taimaka wa uban kiɗi
wurin rarrabe tsakanin ɗiyan waƙa. Mawaƙa sukan yi alfahari da ƙungiyar waƙarsu
har ma suna ambata yadda tafiyar su ke kasancewa.
Jagora : Idan na ɗauki kiɗan gangata,
:
Ga makaɗana ga ’yan amshi,
:
Duk da maroƙa na biye baya,
:
In na ɗau waƙar ɗan Musa,
:
Muhamman wai hat tausai yaj ji.
(Shata: Waƙar Sarkin
Daura Mamman Bashar)
Sannan
aikin masu amshi a wurin wasu mawaƙan
yakan zarce amshi
ya kai ga karɓi da karɓeɓeniya da ma taimakawa wurin ƙulla ɗiyan waƙa, kamar yadda Ɗanƙwairo ke alfahari da
ƙungiyar masartansa na waƙa.
Jagora : Duk makaɗan da a’ Tsahe na shahe,
: Hab
baƙi ha’ ’yan gidan su duka,
Karɓi : Babu mai shirya waƙa kamar tawa,
Jagora : Duk makaɗan da a’ Tsafe nai jam’i,
: Hab baƙi ha’ ’yan gidan su duka,
Karɓi :
Babu mai ƙulla waƙa kamar tawa,
Jagora :
Ga makaɗi ya ƙulla wakatai,
Karɓi : Sai a amsa mashi ba a ƙara mai,
Jagora : In na’ ƙulla waƙa a ƙara man,
Karɓi : Mu huɗu duk azanci garemu,
: Shin a’a mutum guda za ya yarde mu,
: Shirya kayan faɗa mai gida Tsahe,
: Ali ɗan Iro ba ka ɗauki raini ba.
(Ɗanƙwairo: Waƙar
Ali Mai Tsahe)
Comments
Post a Comment