Skip to main content

Posts

Ranar Hausa

Recent posts

An kashe ma Baga mazurunai

An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. Mis sa kunka canye naman ba ku ’yam min ba, Suka ce sun ci sun ji naman zad daɗi. An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. Da sunka canye naman ba ku ’yam min ba, Sunka zo da hanunsu zam masƙi. An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. Da sunka canye naman ba ku ’yam min ba, Sunka ɗora tutun shi zaw wari, An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. Ko da na’ ishe har sun yi kawa, Ga kitse shina ba da ɗab ɗab ɗab, Can cikin wuta ya ɗora con con con. An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. Ya sato gari ya kawo, Na ci nai ƙiba kuma nai ƙarfi, Baga ga shi an kashe mini mazuruna, Baga ga ni ba ƙiba kuma ba ƙafi, Ku dubi duk awazzaina fili. An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. Jafaru Baga Gumi 1993 Science Farfaru Sokoto

Alheri Jifa Ne Ka Yi Shi A Baya Ka Tsince Shi A Gaba

Idan Ba Ka Ji Tsoron Allah Ba Za Ka Ji Tsoron Halittarsa Ma’aikaciyar jinyar da ta ɗauki wannan hoto ta bayyana cewa, kwana biyar ke nan da wannan tsohon ya iso asibitin nan yana jinya; amma duk tsawon kwanaki biyar ɗin nan ba wani daga cikin ’yan'uwa ko abokai na wannan tsoho da ya zo duba shi ballantana su zauna tare da shi. Shi kaɗai yake; su kuma hakan mamaki yake ba su, a ce ga mara lafiya kuma tsoho amma ba wanda yake zuwa ganin shi. Sai dai wani abin mamaki tsawon kwanakin nan da wannan tsoho ya yi a asibiti, wata tantabara takan zo a kullum ta shigo ta windo ta sauka a kan gadonsa ta zauna tare da shi kamar suna hira, ta zuba masa ido na ɗan wani lokaci sai ta tashi ta tafi abin ta. Daga bisani ma’aikatan asibitin sai suka gano cewa lokacin da wannan mara lafiya yake da lafiyarsa yakan zauna a wani wuri da jama’á ke taruwa, to, wannan tantabara a wurin take; kuma kullum ya je yana ba ta abinci. To, wannan shi ne dalilin da ya sanya ita kuma kullum take ziyar

Idan Sarki Ya Yi Maka Zalinci Ba Me Bi Maka Kadi Sai Allah

IDAN ZANCE BAI BI DA KAI BA AIKI ZAI BI DA KAI A wani lokaci mai tsawo, an taɓa yin wani maƙetacin sarki wanda ba shi da yafiya a rayuwarsa. Sarkin nan yana da wani bagire da ya killace wasu kuraye guda goma, ya kiwata su ƙwarai. Buƙatarsa wannan sarki shi ne, a kullum wani daga cikin bayi ko mutanen gari ya yi masa laifi, komai ƙanƙantarsa, to, shi burinsa ya cikia; sai ya sanya a bar waɗannan kuraye sai ji yunwa sa’arnan sai a ɗauki mai laifin nan a jefa masu shi, kafin ka ce me, kurayen nan sun yagalgala shi sun cinye. Ina ya-alla-babu ya-alla, wata rana ana zaman fada sai ɗaya daga cikin fadawa ya yi wata katoɓara, ya yi magana ba daidai ba. Nan da nan sarki ya harzuƙa, ya yi kira ga wasu bayi ya ce maza a je a jefa wannan bafade mai katoɓara wa kurayen nan. Ba shi da wani amfani in ban da ya zama abincinsu. Bafaden nan, nan da nan ya faɗi yana ahi, yana cewa rankai daɗe ka yi mini rai, shekara goma ke nan muna tare da kai, ban taɓa yi maka kuskure ba, na tuba ka yafe mini. S

Ba sata ke da ciwo ba, a maida mutum wawa:

Ba sata ke da ciwo ba, a maida mutum wawa:  Wani mahaukaci ne ya samo dawonsa guda biyu irin wanda ake mulmulawar nan da girma ya ajiye ko me yake jira oho, ya ɗan dai fita.  To, kafin ya dawo sai wani mara tsoron Allah ya zo ga dowon sai ya sace ɗaya, ɗayan kuma da ya bar masa sai ya raba biyu ya mulmula kowane sai suka zama biyu amma fa ƙanana, ya tafi abinsa.  Ko da mahaukacin nan ya dawo ya ga abin da aka yi masa sai ya tsaya shuru. Yana faɗin, “Ni dai ba satar da aka yi mani ba wayau da aka raina mani shi ya fi ciwo.”  Watau ana ganin kamar bai san abin da ya ajiye ba ne.

“Allah Ya yi Allahu Nasa, Bamaguje ya ishe biri ya mutu a gonarsa.”

“ Allah Ya yi Allahu Nasa, Bamaguje ya ishe biri ya mutu a gonarsa.” Ƙabilar Maguzawa mutane ne mafarauta kuma cikin abin da suka fi so su farauta har da birai, to, yawan farautarsu da suke yi ya sa har biran sun gudu su shiga daji inda ba kowa ba ne zai iya zuwa wurin.  Ka san ba yadda Allah bai iya ba, wata rana ya daɗe rabonsa da ya farauci biri sai ya je gonarsa gewaya kawai sai ya samu biri matacce a gonar, wanda shi a nasa ɗabi’ar zuwa farautarsa yake yi sai ga shi banza ta faɗi, don haka cikin irin murnar da zai yi shi ne yake cewa: “Allah Ya yi Allahu Nasa.” Da yake lokacin Musulunci ya bayyana a ƙasar; ya ɗauko kayansa ya kawo gida suka sha dabge.  Mutane kuma da suka ji wannan labari sai duk wanda irin wannan abin farin ciki ya sama na ba zata sai shi ma ya ce, “Allah Ya yi Allahu Nasa.” Sai ka ji waɗanda suka san labarin suna ƙarasa masa da cewa, “Bamaguje ya ishe mushen biri a gonarsa.” Akwai magana, an mari ɗan Bamaguje. Ana ta Maguzawanasali wa yaketa su Ciwak

LABARIN KARIN MAGANA: A Sa A Baka Ya Fi A Rataya

A sa a baka ya fi a rataya:  Kura ce yunwa ya sa ta shiga gari da dare, da za ta shiga sai ta wuce ta wani rugar filani amma sun tashi, ta duba ba ta samu komai ba sai wani ɗan ƙaramin akuya, mara lafiya, sun ɗauka ma ya mutu ne, suka bar shi.  Kura ta yi tsaki ta wuce tana tunanin gaba za ta samu mai mai  kuma ta raina wannan da ta samu. Ta shiga gari ta ƙaraci yawonta ba ta samu komai ba, sai ta dawo za ta koma, ta ma manta da ta yi gamo a farkon shigowarta. Ko da ta zo ta wuce rugar sai ta tuna da ta yi tsintuwaa da. Sai ta juyo ta samu wannan ɗan maraƙin tana faɗin a sa a baka ya fi a rataya.