Adam A. Zango
Sarkin Zazzau Hanjin Jimina
Sanƙira : Gyara kimtsi,
: Gaba salamun baya salamun.
: Hadari sa gabakanka inda kake so Yariman Mawaƙa,
: Mu je zuwa, aha!
Jagora: Adam Zango mai gari,
: Yaro ne adon gari,
: O’o o, o’o o, oo,
Sanƙira: Toh, toh, to!
Amshi: Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora: Ga mai darajar farko matsayi,
: Sarkin Zazzau hanjin jimina,
Karɓi: Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka daban babban sarki.
Jagora: Kai duk tsananin ramar doki,
Karɓi : Kofato na nan bai ramewa,
: Haka Rabbi yake aje hikimarsa,
Jagora: To ga Sarkin Zazzau,
: Shehu Idiris mai takalman ƙare,
: Toh,
Amshi: Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora: Ga mai darahar farko matsayi,
: Sarkin Zazzau hanjin jimina,
Karɓi: Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka,
Jagora: Um!
Karɓi : Daban babban sarki.
Jagora : Ga mai ƙarfi Dagacin mutuwa,
Karɓi : Sankace da maciji dauji kar,
: Sarkin Zazau tafiya sannu,
Jagora : Um!
Karɓi : Ga gamji mazajen alfarma,
Jagora : Farko da na sauka garin Zazzau,
: Na yi ado na sa kubta,
: Na hau doki na sarauta,
Rawani kuma an muni mai kima,
Karɓi : Toh,
: Za shi gidan babban sarki.
Jagora : Kai Tasi’u saurara ka jiya,
: Da na sauka garin Birnin Zazzau,
: Na ga kalar matan Zazzau,
: Da ado tamkar matan Makka,
: Ga shi ina son mu yi hira,
: In ji labari na gidan sarki,
Karɓi : To amma kuma sam ba dama,
: Musulunci bai yarje ma ba.
Jagora : Um!
Karɓi : In ka bi ta zancena.
Jagora : Me ya sa na ga matan Zazzau,
: A ado sun zarce sun kera,
Karɓi : To ko tarihin tafi ɗauko,
: Sarauniyar Zazzau a Arewa,
: Ba wanda ya kai ta ajin girma.
Jagora : To gani gaban fadar sarki,
: Sarkin Zazzau mai alfarma,
: Toh,
Amshi : Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora : Ga mai darahar farko matsayi,
: Sarkin Zazzau hanjin jimina,
Karɓi : Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka,
Jagora : Um!
Karɓi : Daban babban sarki.
Jagora : Farfesun kunama sun san ka,
: Matsayinka daban babban sarki,
Karɓi : Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka,
Jagora : Um!
Karɓi : Daban babban sarki.
Jagora : Yau ga ni gaban gidan sarki,
: Ina tafiya ta cikin ƙawa,
: Wai ni da zan shiga fada,
: Kamar ɗaki na ka ji wawa,
: Ko da na zo bakin ƙofa,
: Sai fadawa suka miƙe,
: Sadaukai da ido jajaye,
Karɓi : Kai gyara kimtsi bi a sannu,
: Gidan sarki ba shigifa ba,
: Jihar can Sakkwato nai zance,
Jagora : To a cikinsu akwai wani ma,
: Da babbar riga ga rawani,
: Sai na ji ya ce kai yaro,
: Ya daka mani tsawa nar ruɗe,
Karɓi : Sai munka kowa zazzaune,
: Yana mai martaba bar ka dai,
: A zatonsa kamar sarki yaz zo.
Jagora : Sai mutumin nan yam miƙe,
: Yac ce mini yaro kai taso,
: Me za kai a gidan sarki?
Karɓi : Mai martaba munka taho mu gani,
: Mun ji yanda yake adalcinsa,
Jagora : To kai yaro ya sunanka,
: Kuma kai ɗan wanne gari ne?
Karɓi : Kai Adam Zango ake ce ma,
: A Kaduna kake muka amsa mai,
Jagora : Kai Tasi’u da ba don kai ba,
: Ni ban san me zan furta mai ba,
: Toh!
Amshi : Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora : Ga mai darajar farko matsayi,
: Sarkin Zazzau hanjin jimina,
Karɓi : Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka,
Jagora : Um!
Karɓi : Daban babban sarki.
Jagora : To sun ƙyale duk sun yarje,
: Na shiga hanya na miƙe,
: Zan je fadar mai Zazzau,
Karɓi : Sai dai kuma ba ka san hanya ba,
: Gidan sarkin da akwai girma.
Jagora : Sai na ga al’umma zaune,
: Sun sha kaya na mutunci,
: Na yi tunanin baƙi ne,
: Ashe duka bayin sarki ne,
Karɓi : To ya riƙe daraja kimarsu,
Jagora : Um!
Karɓi : Kamar ma ba bayi ne ba.
Jagora : Da na je ni gaba na gaishe su,
: Su kuma duka sun amsa,
: Bayan kowa ya yi shuru,
: Sai na ciro magana ƙwara,
: Ni dai farko baƙo ne,
: Na zo fadar sarki ne,
: Shin ko ku ne ’yan fada?
: In kuma ku ne ’yan fada?
: Ya za a yi sarki in gan shi?
Karɓi : A’a ba mu ne fada ba,
: Ga fadar can gefen hauni,
Jagora : Sarkin Zazzau mai girma,
: Ɗawisu adon tafiya kai ne,
: Toh!
Amshi : Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora : Ga mai darajar farko matsayi,
: Sarkin Zazzau hanjin jimina,
Karɓi : Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka,
Jagora : Um!
Karɓi : Daban babban sarki.
Jagoa : To ga ni cikin fadar sarki,
: Wazirin Sarki na zaune,
: Ga Hakimai duka na zaune,
: Ga Fadawa na zaune,
: Sai na ga wani ɗan dattijo,
: Mai siffa kamar Balarabe,
: Ya ci ado da alkyabba,
: Ga ƙamshi mai tashin ƙawa,
: Toh!
Karɓi : Allah kare sarki,
: Ɗan Idirisa daɗo girma.
Jagora : A gaban sarki na taho na zube,
: Ina ta kirari a gabansa,
: Kura mai firgita kalbu,
: Ganga mai fatar giwa,
: Ƙarko da nagarta shi an nan,
: Fage na yaƙi sai sulke,
: Duka da bugu sai ’yan barka,
: Munjirya ka wuce kamun yaro,
: Ko babba yana shakka,
: Karya gwafa shahon ƙarfe,
: Jifa a cikin ruwa shirme ne,
: Adon sama’u kake sarki,
: Zara kake mai taurari,
: Mu dai sai sa albarka,
: Buzun bushiya ba a imma,
: Kai ni Zango a wurina,
: Duk sarakuna ai ka fi su,
: Toh
Amshi : Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora : Sarkin Zazzau mai girma,
: Ɗawisu adon tafiya kai ne,
: Toh!
Karɓi : Allah kare sarki,
: Ɗan Idirisa daɗo girma.
Jagora : Daga nan shauƙi yak kwashe ni,
: Na ci gaba da kirarin mai girma,
Karɓi : Sarari mai ƙare gudun doki,
: Tsawa sa karkarwa.
Jagora : Toh, toh!
Karɓi : Tsakar dare hana tafiya,
: Ragayar dutse ajalin yaro.
Jagora : Um!
Karɓi : Allah kare sarki,
: Ɗan Idirisa daɗo girma.
Jagora : You are the man of the people,
: You are the last man standing,
: You are the almighty king,
: Shin a Arewa kuwa dak kamarsa?
: Toh!
Karɓi : Kai Zango ka saita batunka,
: Don kana gaban sarki ne.
Jagora : Bari Tasi’u sai na ƙara,
: He is the greater than Sarakuna,
Karɓi : You are special ɗan Zango,
Jagora : Well done,
Karɓi : Turancin sai mun ɗana.
Jagora : Rabi kare Sarkin Zazzau,
: Mai martaba ubana babba,
Amshi : Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora : Ga mai darajar farko matsayi,
: Sarkin Zazzau hanjin jimina,
Karɓi : Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka,
Jagora : Um!
Karɓi : Daban babban sarki.
Sanƙira : Gyara kimtsi,
: Gaba salamun baya salamun.
: Hadari sa gabakanka
: Yariman mawaƙa mu je zuwa
: Ahah!
Jagora : Adam Zango mai gari,
: Yaro ne adon gari,
: O’o o, o’o o, oo,
Comments
Post a Comment