Babi Na Ɗaya
Gabatarwa
1.1
Shimfiɗa
Waƙa, walau ta baka ko rubutacciya, wani muhimmin ɓangare
ne na adabin al’umma. Masana sun yi nazarce-nazarce da dama kan jigo da salo,
da kuma zubi da tsarin ire-iren waƙoƙin da ake da su na Hausa. Ta fuskar irin
waɗannan nazarce-nazarce ne aka gano saƙonni da salo da kuma zubi da tsari da
ma wasu abubuwa na daban da suka ƙunsu a cikin waƙoƙin baka na Hausawa. Wannan
nazari ya ɗora ne a kan ire-iren nazarce-nazarcen da aka yi kan waƙoƙin baka na
Hausawa, inda aka ɗauki jerin sarƙe aka nazarce shi.
An ga yadda yadda maimai ke taka rawa wurin haifar da jerin
sarƙe nau’o’insa. Jerin sarƙe, zance ne wanda aka sarƙa a falan biyu ko
fiye, wato inda aka samu daidaito na sunaye ko yankuna ko kalmomi ko aka samu
wani irin zubi mai burgewa, da aka samu ɓuraɓusai a cikinsa. An yi bayanin nau’o’in jerin
sarƙe da suka haɗa da “Cikakken Jerin Sarƙe” da kuma “Ragagge Jerin Sarƙe”,
tare da la’akari dadalilan da suke haifar da su. An nuna cewa, “Cikakken Jerin
Sarƙe” shi ne a samu daidaito a gefen dama da na hagu, ta yadda za a samu zubi
iri ɗaya, sannan aka bayyana “Ragaggen Jerin Sarƙe” da cewa shi ne a samu zubi
iri ɗaya amma a samu saɓanin wasu kalmomi a cikinsa. An nuna cewa yawan ɓuraɓusai
a cikin ɗan waƙa yana daga cikin alamomi ko abubuwan da ke hana a samu daidaito
a “Ragaggen Jerin Sarƙe”.
Haka kuma ƙoƙarin bayyana wani abu ko wani labari yana sanya mawaƙa
amfani da jerin sarƙe, misali:
Jagora: A zamanin nan Sarki na da
rai,
Idan watan Azumi ya kwan tara,
Sai a aiko Sarki na kira,
Sai ko in je Ƙaraye gurin Garba,
In na je ya kai ni masaukina daban,
Kuma masaukin yarana daban,
A masukina an yi shirye-shirye,
Ga tuwo mai nama in ji na Amadu,
Ga ruwan sha in ji uban Bello,
Ga fura mai nono in ji uban Daje,
Yo ga ruwa sanyi Garba ya aje,
Yo ga gasasshen nama ya ajiye,
Ya ajiye yaji a waje ɗaya,
Mu tashi cin naman mu baɗa masu.
(Audu Wazirin Ɗanduna: Sarkin Ƙaraye Abubakar)
An ga yadda bayar da labari ya sanya Wazirin Ɗanduna
ya yi amfani da ɓuraɓusan “sai” da
“idan” da “ya” da “a” da “na” da “ko” da “in” da “kuma” da “an” da “ga” da
“mai” da kuma “mu” wurin sarƙe jumlolinsa. Aikin bai tsaya nan ba ya nazarci
nau’o’in jerin sarƙe na sautuka da na jumloli da na ma’ana. Da aikin ya nazarci
jerin sarƙe na kalmomi an ga yadda mawaƙa ke amfani da kalmomi iri ɗaya amma
ma’ana ta sha bamban, ko kalmomi daban-daban ma’ana ta zo ɗaya da sauransu.
1.2
Dalilan Bincike
Nasarin
salo a waƙa, ya zama abu ne da ko’ina ana gabatar da shi, tun daga kan kundayen
digiri na farko har zuwa na uku. Marubuta irinsu, Jakobson (1966) da Ɗangambo
(2007) da Yahya (1997 da 2001) da Mukhtar (2004) da Sarɓi (2007) duk sun
gabatar da nazari a kan salo, sai dai duk da haka ayyukan da suka gabatar sun
bambanta da wannan aiki da ya gudana, misali:
Muhammad (1977) ya bayyana
“Jerin Sarƙe” a balagar magana, ya ruwaito daga abin da Jakobson (1966) ya faɗa,
inda shi Jokobson ɗin ya ce “jerin sarƙe” shi ne gwama mabambanta rukunoni na
ilimin kimiyyar harshe da suka haɗa da, tsarin sautuka da tasrifin ma’ana da
tsarin ginin jumla da sauransu, ta yadda
za su samu jituwa”. Muhammad (1977) ya bayyana yadda “jerin sarƙe” yake a
rukunin sautuka ya nuna yadda mawaƙa ke zaɓen sautuka ko haruffa irin ɗaya su
jujjuya su a cikin layuka ko ɗangwayen waƙoƙinsu. Ya ba da misali da baitin
waƙar Aƙilu Aliyu:
Saba da samo gaskiya duk nisa,
Sarari da ɓoye idan ka so bunƙasa.
Nazarin
Muhammad (1977) ya taƙaita ne a kan rubutacciyar waƙa, shin za a iya samu jerin
sarƙe a waƙar baka? Idan za a iya, to yaya yake?
Muhammad
(1980) ya bayyana abin da Ɗan’anace ya yi, a lokaci da yake yi wa gwaninsa
Shago waƙa, inda ya gwama yabon Shago da yabon kansa a wuri guda. Muhammad
(1980) ya kira wannan salo da “jerin sarƙe na jigo”.
Jagora:
’Yan
dambe na ganin laihinai,
Wandara ’yan dambe na
ganin laihinai,
Arne ya ci moriyaƙ
ƙullinai,
Ni kau makaɗi suna ganin
laihina,
Ni kau na ci moriyar
bakina,
Gabas da Yamma dama da
hauni, Kudu da Arewa,
Mutum ba inda bai ji
waƙata ba,
Kai jama’a!
Duw wanda bai ga damben
Shago ba,
Yana da sauran kallo,
Mutum shina da aiki
baya,
Ya dai zaka duniya kamar
bai zo ba,
Kamar dai zuwan kare ga
karofi,
Ko dai ya ƙaura ba a
gafarta mai.
A
waɗannan ɗan waƙa da Ɗan’anace ya yaba wa gwaninsa Shagon Bakura ne, amma an
samu jerin sarƙe na jigo, inda Ɗan’anace yana cikin yabon Shago, sai shi ma ya
sa yabon kansa, ya nuna ’yan dambe na jin haushin Shago saboda irin ƙarfin da
yake da shi, har ma yake nuna cewa ya ci moriyar ƙullina (irin naɗin hannunsa),
daga nan kuma sai Ɗan’anace ya dawo yana yabon kansa, yana cewa, shi ma ’yan
dambe na ganin laifinsa saboda irin waƙoƙin da yake zuba wa Shago. Saboda haka
Muhammad (1980) ya nuna yiwuwar samun jerin sarƙe a waaƙar baka tun da ga shi
har ya kawo misali.
Fagge
(2012:100) ya bayyana cewa, “jerin sarƙe shi ne a samu zubi iri ɗaya a jumloli
ko wasu kalmomi ko yankuna da ganga”, cikin misalan da ya kawo akwai, “Ana so
harshe ya bunƙasa, ya haɗu da sauransu”. Da wannan misali an gane cewa ana
samun jerin sarƙe a magana ta yau da kullum, to, amma ya abin yake a waƙar
baka?
Da
aka bi nazarce-nazarce magabata, an samu da yawa sun nazarci jerin sarƙe ne a
rubutattun waƙoƙi da kuma magana na yau-da-kullun kamar yadda Fagge (2012) ya
kawo misali. Saboda haka an gabatar da wannan bincike domin tabbatar da da’awar
Muhammad (1980) cewa akwai jerin sarƙe na jigo a waƙar Shago Bakura da
Ɗan’anace ya yi, sannan kuma aka tattauna waɗannan batutuwa:
a) Tabbatar da samuwar jerin sarƙe a waƙoƙin baka na Hausa, saboda yawancin
ayyukan da suka gabata an kawo misalai ne daga rubutattun waƙoƙi.
b) Bin diddigi cewa ko za a samu sauran nau’o’in jerin sarƙe a waƙoƙin baka na
Hausa, kamar yadda aka samu a rubutattun waƙoƙi.
1.3
Hasashen Bincike
Wani abin lura dangane da jerin sarƙe shi ne yadda yake
iya mamaye ilahirin waƙa, wato a samu nau’o’insa. An gano cewa ana iya raba
jerin sarƙe zuwa manyan gidaje biyu wato “Cikakken Jerin Sarƙe” da kuma
“Ragaggen Jerin Sarƙe”. Sannan binciken ya ƙara gano cewa a ƙarƙashin waɗannan
kaso ana samun jerin sarƙe na sautuka da na jumloli da kalmomi sannan ana samun
jerin sarƙe na ma’ana.
1.4
Muhimmancin Bincike
Wannan
bincike gudunmawa ce ga masu nazarin waƙa, musamman wajen faɗaɗa tunani da
zurfafa nazari a kan salo, domin za su riƙa sanya jerin sarƙe a aikinsu, da aka
riƙa shiru a kansa. Sannan binciken gudunmawa ce ga masu nazarin kimiyyar
harshe, ta yadda aka gano yadda mawaƙa ke iya zaɓin kalmomin da suka dace yayin
shirya waƙa.
Haka
kuma binciken taska ce ga masu shirya ƙamus, saboda za su samu kalmomi
daban-daban da aka takace su a cikin nazarin. Masu nazarin ma’ana ma za su
amfana da aikin, domin an nazarci nau’o’in jerin sarƙe da ma’ana take haifarwa.
Haka kuma, masu nazarin adon harshe da adon magana su ma, nazarin zai zame masu
hujja saboda salo aka nazarta kuma adon harshe na cikin salo.
1.5
Farfajiyar Bincike
Farfajiyar wannan bincike ta taƙaita a kan waƙar baka da
jerin sarƙe, wato binciken ya yi nazarin yadda nahawu da zaɓin kalmomi suke
haddasa maimai na yanki ko ɗango a ɗan waƙa. Haka kuma, binciken yana da jiɓi da
salo amma duk da hakan an tsayar da ƙafa a kan jerin sarƙe, inda aka nazarci
cikakken jerin sarƙe da ragaggen jerin sarƙe, kana aka nazarci tasirin maimai
na kalma ta fuskoki mabambanta da kuma yadda jumla take maimaita kanta a ɗan
waƙa domin samar da jerin sarƙe.
1.6 Hanyoyin Bincike
Wannan bincike ya yi hirarraki da masana, domin samun
haske kan yadda za a gano yadda za a gudanar da aikin. Sannan an duba kundaye
da bugaggun littattafai da kuma maƙalu, masu alaƙa ta kusa ko ta nesa da wannan bincike, domin a samu dacewa da abin da ake nema.
Haka kuma an nazarci littattafai da aka shifci waƙoƙin
baka, kuma an saurari wasu waƙoƙin da aka rera a faya-faye ko CD ko wanin haka,
domin tantance ɗiyan waƙoƙin masu ɗauke da jerin
sarƙe.
1.7 Naɗewa
Babi na ɗaya shimfiɗa ce ga aikin da aka gabatar, bayan
shimfiɗa, an bayyana dalilan bincike da hasashen bincike da muhimmancin bincike
da arfajiyar bincike da hanyoyin bincike daga nan aka naɗe babin.
Comments
Post a Comment