Skip to main content

RAGAGGEN JERIN SARKE A KARIN MAGANR HAUSA

Ragaggen Jerin Sarƙe A Karin Magana
Yadda Adabin Yake
JINKA YA FI GANINKA: Karin magana ce da aka yi amfani da salon sarrafa harshe wajen gina ta. An yi amfani da kalmar “ji” da “gani” waɗanda dukkansu suna iya zuwa da ma’anarsu na asali, haka kuma, suna iya zuwa da wata ma’ana ta daban. Zancen karin magana ce, ko shaguɓe, ko ma a ce habaici da ke iya zama wani abu na alheri ko akasi ga wanda aka yi wa ita. Misali akwai wani mai hannu da shuni da idan ’yan’uwansa suka zo masa da goron gayya na wani sha’aninsu, yakan kada baki ya ce da su, “Ƙafata kuke so ta so, ko hannuna kuke so ya za?”, idan suka ce ƙafa, to, zai ciko motoci da mutane su zo wurin bikin amma ba abin da zai ba su, amma suna cewa hannu, shi ke nan, zai yi masu sha tara na arziki ya yi masu fatan alheri ya ce zuwansa zai yi wuya.
Haka kuma a kaikaice, karin maganar tana iya nufin wanda aka gaya wa ita, ba a son sa, wato dai ya yi zamansa a nesa ba sai an gan shi ba, an fi son amonsa daga nesa. Ko in yana nesa an fi kwanciyar hankali da shi amma da ya zo kuwa sai an ɓata.  
Kyawun gwani, a gan shi a raina, wannan ma tana iya fassara karin maganar, wato, yawanci idan aka ce wannan mutumin gwani ne ko jarumi, kilan ka gan shi da wata irin sifa ta rashin gwanintar ko rashin jaruntakar da har za ka iya tunanin kai wannan ko ba shi ba ne ake ta gwarzanta shi ba, amma da ranarsa ta zo sai ka ga ana ta mamakinsa kan irin waibuwarsa da gwanintarsa. 
Sannan kalamar, “Matso kusa ka sha kunya” tana iya fassara karin maganar, wato wani abu ne da a nesa za a yi ta ganin kyawunsa amma da ka zo kusa da shi sai ka ga ba mai kyawun ba ne. Kamar dai wata hula da ake ce wa hakan, ana saƙa ta ne da zaren ulu a yi ta kamar ƙube, in ka hango ta daga nesa ta burge ka, amma ta an zo da ita kusa sai ka ga ƙarya ce ba ƙuben ba ne.
Da kyau kwali idan bai jiƙe ba, wannan ma na iya fassara karin maganar, saboda idan ka dubi kwali, yadda aka yi shi sai ya burge ka, amma da ya sha ruwa sai ya laƙwame ya zama wani abu daban mara kyau saɓanin yadda ka san shi.
Yadda Abin Yake A Nahawu
Jinka ya fi ganinka: An yi amfani da a alamci wurin gina wannan karin maganar, in da aka yi amfani da kalmomin “ji” da “gani” wurin alamta yanayi ko halin da ake so a kwatanta mutum ko abin da ake so a nuna illarsa ko alherinsa. An kuma yi amfani da “JERIN SARƘE” wurin sasanta kalmar “ji” da “gani” aka kuma maimaita wakilin suna tuhumau “ka” a kowane sashe domin dirkewa. Aka kuma yi amfani da madanganci /-n/ domin nuna dangantaka tsakanin kalmomin ji da kuma gani wanda kowannensu yankin suna ne. Sai wani abin burgewa da aka samu yankin aiki a tsakiya “ya fi” wanda shi ya zama gada ko mahaɗin jumla ta farko da kuma ta biyu.
Karin maganar ragaggen jerin sarƙe ne, saboda zubin gaɓoɓi na sashe da sashe nata ba su dirke juna wato gefen farko an samu gaɓoɓi biyu, a ɗayan gangar kuma aka samui uku. /Jin1/ /ka2/ ya fi /ga1/ /nin2/ /ka3/ 2/3. Amma idan aka bayyana yadda jumlar take sosai sai a ga an samu daidaito a jerin sarƙen kamar haka: /A1/ /ji2/ /ka3/ ya fi /a1/ gan2/ /ka3/ = 3//3. Wanda in a waƙa ce aka samu wannan saɓani ka ji ana cewa an samu “ILLA” ko “ZIHAFI”.
Bishiyar Li’irabi
Jinka ya fi ganinka!
J =  YS + YA
YS = Srƙnsb
Srƙnsb = Sn + Mhɗ + WS
Srƙnsb = Ji + (-n) + ka 
YA = GA + YS
GA = LS + LL + A
GA = ya + a + fi
YS = Srƙsn
SrƙSn = Srƙnsb
Srƙnsb = Sn +Mhɗ + WS       
Srƙnsb = gani + (-n) + ka

Muhammad Bello Falama
17/09/2017
A yi hakuri na yi zanen bishiyar amma ban san yadda za a yi in yi paste dinsa a facebook ba, ko na yi bai fitowa

Comments

Popular posts from this blog

RABE-RABEN KARIN MAGANA

Rabe Rabe Karin Magana  Karin magana lokacin maguzanci  Karin magana bayan saduwa da Larabawa  Karin magana bayan zuwan Turawa  Karin magana bayan bariki ya bunkasa  Karin magana zamanin siyasa  Falama 2016 (Hausa Karin Manana)

HAUSA KARIN MAGANA:YARO

1) Yaro yaro ne.  2) Yaro man kaza in ya ji rana ya narke.  3) Yaro bari murna karenka ya kama zaki.  4) Ta yaro kyau take ba ta karko.  5) Yaro ko ya yi tuwo ba ya yi miya ba.  6) Abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba ya hango ba.  7) Don kana da tsawo da karfi, ba ka rankwashin yaro.  8) Inda yaro ya tsinci wuri,  nan ya fi saurin tunawa.  9) In ba a kwado da yaro,  a ba shi gishirinsa da daddawarsa.  10) Yaro fadi a watse.  11) Yaro,  yaron gobe.  12) Yara manyan gobe?  14) Abokin wasan yaro,  wanda ya ja shi.  15) Yaro nemi kudi tun abin saye bai zo ba.  16) Yaro ba ya sanin yaro ne shi sai ya yi aure an fid da shi gandu.  17) Daya matar yaro.  18) Yaro na bayan uwatai.  19) Koko abokin yara.  20) Dan yau ba a shaidarsa.