Skip to main content

Camfi Da Hikimomin Da Ke Cikinsa

Wasu Hikimomin Da Ke Cikin Camfin Hausawa 

“Duk Wanda Aka Shere Shi, Zai Rasa Mata!”

Camfi wata dabara ce ta tarbiyya da Hausawa ke amfani da ita wurin shiryar da ’ya’yansu ba tare da sun faɗa masu madogara ba, saboda ganin cewa su yara ne, ko gaya masu madogarar ba ta da wata fa’ida, ko kuma in an gaya masu ƙwaƙwalwarsu ba za ta ɗauka ba.

Camfi shi ne a ce, idan abu kaza ya faru, to, lalle ne abu kaza shi ma ya faru. Misali: “Duk wanda ya yarda aka share shi, zai rasa mata”.

Tunanin da ke cikin wannan chamfin shi ne, a da aure na da wahala, shi ya sa ma Bahaushe ke cewa, “Ba neman aure ke da wuya ba, a shiga a fito”. A wasu wurare sai ka yi noma ko ka kai wa iyayen matar da kake nema gayya, wato ka tara abokanka ku je ku nome wa iyayanta gona. 

Bayan wannan sai ku nemi aure ku goma sha, a ce a ciki ne za ta fitar da guda da za ta aura. Daga nan fa an riƙa kai toshi ke nan ba iyaka. Wannan ya kai nasa, wancan ma ya kai. In wannan ya ga alamar wancan ya fi shi tagomashi a wurin budurwar ya jefe shi ko ya yi masa asirin da zai nakasa shi, ko ya haukata shi. Wani lokaci kuma amaryar za a yi wa tasau a ce ba za a ɗaura auren ba sai an biya duk wani abin da ta ci na saurayi, har ma abin yakan kai ga alƙali.

Ita kuma shara da aka danganta abin da ita, da farko dai shara in ana yin ta akwai abubuwa da yawa a cikinta da ido ke iya gani, sannan akwai wanda bai iya gani. Ga guba ga ƙura wanda mai lalura idan ya tsaya a wurin da ake sharar nan, tana iya tashi.

Saboda haka, maimakon a zo ana ce maka matsa ana faɗa da kai, wani kuma girman kai ne ko haushi zai hana ya matsa daga inda ake shara. Shi ne, sai akwa kwatanta yadda kowa ke son mata in kuma mace ce miji, sai aka ce za ka rasa matar ko za ki rasa mijin.

In kuma har ka kuskura aka share ka, to akwai makari, shi ne a yi maka azaba, wato sai ka ciji tsintsiya, wanda kuma wulaƙanci ne. Ita ma ƙazama ce tsintsiyar, don ba irin abin da ba a sharewa da ita.

Da wannan sai abin ya zama da sauƙi, kai mai shara sai a ba ka wuri ka yi shararka, kai mara shara kuma an tsare lafiyarka cikin hikima. Don haka ba kare bin damo.

Muhammad Bello Falama

Comments

Popular posts from this blog

RABE-RABEN KARIN MAGANA

Rabe Rabe Karin Magana  Karin magana lokacin maguzanci  Karin magana bayan saduwa da Larabawa  Karin magana bayan zuwan Turawa  Karin magana bayan bariki ya bunkasa  Karin magana zamanin siyasa  Falama 2016 (Hausa Karin Manana)

RAGAGGEN JERIN SARKE A KARIN MAGANR HAUSA

Ragaggen Jerin Sarƙe A Karin Magana Yadda Adabin Yake JINKA YA FI GANINKA: Karin magana ce da aka yi amfani da salon sarrafa harshe wajen gina ta. An yi amfani da kalmar “ji” da “gani” waɗanda dukkansu suna iya zuwa da ma’anarsu na asali, haka kuma, suna iya zuwa da wata ma’ana ta daban. Zancen karin magana ce, ko shaguɓe, ko ma a ce habaici da ke iya zama wani abu na alheri ko akasi ga wanda aka yi wa ita. Misali akwai wani mai hannu da shuni da idan ’yan’uwansa suka zo masa da goron gayya na wani sha’aninsu, yakan kada baki ya ce da su, “Ƙafata kuke so ta so, ko hannuna kuke so ya za?”, idan suka ce ƙafa, to, zai ciko motoci da mutane su zo wurin bikin amma ba abin da zai ba su, amma suna cewa hannu, shi ke nan, zai yi masu sha tara na arziki ya yi masu fatan alheri ya ce zuwansa zai yi wuya. Haka kuma a kaikaice, karin maganar tana iya nufin wanda aka gaya wa ita, ba a son sa, wato dai ya yi zamansa a nesa ba sai an gan shi ba, an fi son amonsa daga nesa. Ko in yana nesa

HAUSA KARIN MAGANA:YARO

1) Yaro yaro ne.  2) Yaro man kaza in ya ji rana ya narke.  3) Yaro bari murna karenka ya kama zaki.  4) Ta yaro kyau take ba ta karko.  5) Yaro ko ya yi tuwo ba ya yi miya ba.  6) Abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba ya hango ba.  7) Don kana da tsawo da karfi, ba ka rankwashin yaro.  8) Inda yaro ya tsinci wuri,  nan ya fi saurin tunawa.  9) In ba a kwado da yaro,  a ba shi gishirinsa da daddawarsa.  10) Yaro fadi a watse.  11) Yaro,  yaron gobe.  12) Yara manyan gobe?  14) Abokin wasan yaro,  wanda ya ja shi.  15) Yaro nemi kudi tun abin saye bai zo ba.  16) Yaro ba ya sanin yaro ne shi sai ya yi aure an fid da shi gandu.  17) Daya matar yaro.  18) Yaro na bayan uwatai.  19) Koko abokin yara.  20) Dan yau ba a shaidarsa.