Skip to main content

Tarjamar Siyasar Soyayya Da Ke Ƙunshe A Waƙar Jarumar Mata Ta Hamisu Breaker

https://youtu.be/Cq_Gz7f0rgU

Tarjamar Siyasar Soyayya Da Ke Ƙunshe A Waƙar Jarumar Mata Ta Hamisu Breaker
Muhammad Bello Falama (Sarki Falama)
mbfalama@gmail.com
Ɗalibin Digirin MA A Sashen Harsuna Da Al’adun Afirka‚
Jami’ar Ahmadu Bello‚ Zariya
Asabar 27/06/2020

1.1 Waƙar Jarumar Mata (Laraba 24/06/2020 08:27pm  –  Asabar 27/06/2020 11:38pm)
Kafin waƙar jarumar mata‚ waƙar auren Sambisa ta Ibrahim Yamu Baba wadda ya taske ta a tashar 3sp TV a YouTube ke tashe. Duk ta cika gari kuma ana sanya ta a wasu tashoshi na talabijin; ta sami karɓuwa sosai tun ma ba a wurin yara ƙanana ba da suka hardace ta; samari da ’yammata kuwa duk suna da ita a waya‚ ita ke tashe‚ ita ake yayi‚ har ma an yi ta na ɗaya na biyu har zuwa uku‚ amma ko da sawun giwa ya zo sai ya take na raƙumi. Don haka‚ da jin irin bidiri da cakwakiyar da ke cikin waƙar jarumar mata sai yayin ya koma kanta aka manta da waƙar auren Sambisa.   

Ko da na ji waƙar da abin da ke faruwa a kanta ban yi wani yunƙuri na in tofa wa ƙulli tofi ba‚ sai kamar kwana uku ko huɗu da suka gabata da wani aboki ya zo yake ce mini ya kamata ka nazarci waƙar jarumar mata saboda yadda ta cika gari ga shi har ana ƙorafin wasu har sun saki matansu a kanta. 

To‚ da wannan ne na sami karsashi da sha’awar ina so in ga waƙar in kuma san abin da waƙar ta ƙunsa. A kan haka ne na nemi waƙar na saurara kuma na fara shiftar ta‚ amma sai na ga kamar wadda na samu ba ta cika ba‚ saboda haka‚ sai na neme ta a YouTube na kuma samu‚ aiki kuma ya ci gaba. 

Ina cikin bincike ne sai na ci karo da aikin da Baba Gusau – kamar yadda ’yan ajinmu suke kiran sa a lokacin muna digiri na farko idan mun je sayan littattafa ko mun shiga ɗakin karatu muna neman littattafansa – ya aika wa BBC News Hausa ran 20 Yuni 2020. Bayan bitar da na yi wa aikin farfesa sai na lura da ya yi ma waƙar ɗibar manya‚ da wannan kuma na fahimci cewa mawaƙin ya fi kusa da mu yara‚ sai na ce wananan aikin baban yara ne kuma abin da babba ya hango ne‚ don haka bari wani matashi na kusa da su Hamisu Breaker ya wakilci tunanin matasa. 

Duk da cewa na fi son mu’amala da waƙoƙi na dauri don ko a kundin didiri ɗina na farko tsofoffin waƙoƙi na taɓa‚ amma kuma ga wani aikin da nake ciki tsundum ba damar gudu. Da wannan ne kuma na duƙufa a kan aikin.  

Sa’ar da na sami waƙar‚ na same ta ne a YouTube Channel ɗin mawaƙin mai suna Hamisu Breaker da yake da mabiya kusan dubu caa’in da ɗaya da dubu ɗari uku da ’yan kai. Waƙa ɗaya ce amma bidiyon irin biyu da suna iri biyu. Wadda aka yi amfani da ita ce ta farko da ta zo da suna: Hamiu Breaker – Jarumar Mata (Officiall audio) 2020 wadda wata biyar da suka gabata aka sanya bidiyon a YouTube. 

Kusan mutum miliyon ɗaya da dubu ɗari suka kalli bidiyon a lokacin da na same ta‚ har da ni ke nan. Haka kuma‚ kusan mutum dubu ɗari huɗu ne suka yaba da bidiyon. Kuma kusan mutum ɗari uku suka yi tir da bidiyon. Waƙar ta sami tsokaci guda ɗari huɗu da sha huɗu a lokacin nazarin. Mafi yawa‚ tsokaci ɗin yabo ne sai ’yan kaɗan waɗanda suka zama akasi.

1.1.1 Dabarun Da Aka Yi Amfani Da Su Wurin Nazarin Waƙar
An gabatar da wannan nazarin ne bisa ga abin da kunne ya ji kuma ya saurara na waƙar gami da abin da ido ya gani a lokacin da yake samo waƙar a YouTube‚ ba a yi la’akari da abin da yake faruwa a gari ba irin na husuma ko tattaunawa da ake yi na waƙar a duniyar Hausawa ba. Haka kuma ba a kula da mawallafin waƙar ba. Waƙar kawai aka nazarta ta hanyar amfani da tunanin Bahaushe da kuma yanayin da ya jawo har waƙar ta shahara‚ sai lafuza da aka yi amfani da su wurin bayyana zurfin ƙaunar da mawaƙin yake yi wa masoyiyarsa.

2.0 Salon Zubi Da Tsari Na Waƙar Jarumar Mata  
Mawaƙi: Hamisu Breaker
Sunan Waƙa: Jarumar Mata
Tsawon Waƙa: 3:15
Amshi: Waƙar ba ta da amshi
Ɗiya: Akwai ɗiya 31 a waƙar an kuma yi amfani da kiɗan kwamfyuta a waƙar. Ya shirya waƙar layuka bibiyu kamar rubutatta. Sai a ɗa na 13 da na 14 da kuma na 31 tsarinsu ya saɓa‚ 13 da 14 sun zo da layuka hurhuɗu ne amma na 31 da ya zo a ƙarshe sai ya zo da layuka uku. Wannan wani tsari ne da wasu waƙoƙin yau suka keɓanta da shi‚ watau idan aka zo abin da ya yi kama da tsakiyar waƙar sai a sauya salo domin a nuna an zo ƙololuwa ko tozo na waƙar. Mawaƙan yau suna kiran haka interlock/intermission watau abin da ya haɗa sashe na farko na waƙar da sashe na biyu. Za a ji da murya da salon waƙar duk sun sauya. Sannan ƙarshen waƙar ma aka sami wani salo da ya nuna an zo ƙarshe.

Karin Waƙar: Kamar a ce mustaf’ilun ce ta Larabci Hamisu ya ɗauka yake maimaitata sau biyu da rabi. 

Buɗewa Da Rufewar Waƙar
Mawaƙin‚ kai tsaye ya buɗe waƙa tare da faɗin damuwarsa‚ amma wurin rufe waƙar sai ya yi kamar yadda Narambaɗa ke yi‚ watau yana maimaita tirke ne ko gindin waƙa‚ shi ko Hamisu ya rufe nasa ne ta hanyar maimaita wasu kalmomi ko a ce ɗan waƙa.

Hamisu ya buɗe waƙarsa ta hanyar bayyana tunaninsa da damuwarsa a kan soyayyarsa. Haka kuma‚ ya bayyana irin dabaru da kwanciyar ɗaukar rai da zai yi a lokacin da yake fata ya sami soyayya. Sannan ya bayyana yadda zai kasance idan ya sami rinjaye a soyayya‚ ya rufe waƙar ta hanyar ba wa samari da ’yammata wasiyyar cewa‚ duk wahalar da aka sha a bar tuna baya tun da gyartai ya ci sarauta.  

Wannan waƙa‚ waƙa ce ta zamani  da ta fi kama da waƙar baka. Ba ta da tsayayyen amsa-amo a ƙarshen layukanta in ba na kari ba da ya fi zuwa sama sama. Ba ta kuma da amshi. Tana kuma da rauji ƙwarai da rausayawar murya. 

Mawaƙin ya yi amfani da wasula iri uku a ƙarshen ɗiyan waƙar. Wasalin /a/  ita ya fi bayyana‚ ta zo a ɗa na 1 – 4 da ɗa na 5 – 12 da kuma ɗa na 14 – 26‚ sai wasalin /e/ da ya zo a ɗa na  13 da 31‚ sai wasalin  /i/ da ya bayyana sau 4 a ƙarshen ɗa na 27 da 28 da 29 da kuma 30 .

Har wa yau‚ Hamisu ya yi amfani da gaɓoɓi iri biyar ko shida a waƙar. Daga ɗa na 1 – 4 gaɓar -ba. Daga 5 – 12 an sami gaɓar –sa.  Daga 14 – 26 an sami gaɓar –na. Daga 27 –28 an sami gaɓar –ki. Daga 29 – 30 an sami gaɓar –ƙi. Ɗa na 13 da 31 kuma aka sami aka gaɓar –ne.    

2.1 Jigon Waƙar Jarumar Mata
Hamisu Breaker ya yi zurfin ciki wurin bayyana jigon wannan waƙa inda sai a ƙarshenta ne ya bayyana. Jigon wannan waƙa wasiyya ce Hamisu Breaker yake ba samari da ’yan mata cewa duk abin da ya faru a soyayya matuƙar an kai gaci to a yi haƙuri domin masoyi yana da rana. 
A bisa wannan zurfin ciki na Breaker za a iya cewa da za a ɗauki ɗiyan waƙa biyu na ƙarshe a dawo da su farkonta da abin ya zauna kuma ya yi. Sai su zame mata tamkar mabuɗi. Misali:
29) Samari mui haƙuri‚ 
Idan har mun samu so mu sa sauƙi.
30) ’Yam mata mui haƙuri‚ 
Idan har mun samu so mu sa sauƙi
31) Masoyi yana da rana ne‚
Masoyi yana da rana ne‚
Masoyi yana da rana ne.

Ashe da rai nake son ki‚
Jaruma ba da zuciyata ba.

Komai ruwa da iska‚ 
A kanki ba za ni daina kewa ba.

Idan na samu zarar samunki‚
Ba za ni tanka kowa ba.

Kamar a ce haka ne‚ amma sai Hamisu ya bar wa cikinsa sai da ya kai ƙarshe sannan ya bayyana manufarsa.

2.2 Siyasar Soyayya A Waƙar Jarumar Mata
A wannan bagire ne mawallafi Hamisu Breaker ya warware ƙananan jigogin waƙar. Ya faɗakar da masoya‚ musamman matasa kan yadda ya kamata soyayyarsu ta kasance. Ya Bayyana cewa a soyayya akan wahala‚ akan biɗi taimakon masoyi‚ idan kuma an dace an sami abin da ake so, to, ban da waiwaye ban da tuna baya. Haka kuma ya nuna a kuma riƙa ƙyaliya da yafiya a harkar soyayya. Duk wannan ya bayyana su a ɗan waƙa na 21 da 29 da 30 da kuma abubuwan da a yi bayaninsu a 2.2.2.

2.2.1 Muhallin So A Waƙar Jarumar Mata
Mawaƙin ya zaɓi ya buɗe waƙarsa ta hanyar wani abu mai kama da fargar Jaji. Hamisu ya daɗe yana soyayya amma sai daga bisani ya farga yake yanke hukunci cewa rai shi ne muhallin soyayya na gaskiya. Saboda rai yana gaba da zuciya duk da cewa akan ce‚ “Na so ta zuciya ɗaya.” Amma yaushe ake kuɗin ƙasa‚ idan babu rai komai ya tsaya. Hamisu ya tabbatar da haka a ɗan waƙa na 1 da na 12 da kuma na 27: 
1
Ashe da rai nake son ki‚
Jaruma ba da zuciyata ba.
12
Sam ba batun na fasa‚
Ko za a ce min im ba da rai fansa.
27
So na faranta rai da ruhi‚
Mai sa ka zam kamar sarki.

Da waɗannan ɗiyan waƙar, Hamisu ya bayyana muhallin so da kuma irin abin da za ka yi a yarda cewa soyayyarka ta haƙiƙa ce. A ɗa na 12 Hamisu ya nuna cewa a duk lokacin da aka yi nisa a soyayya watau aka fahimci juna‚ to‚ ba batun a fasa‚ sai dai a bayar da rai a madadin soyayya ko da kuwa za a rasa shi. A ɗa na 27 ya nuna cewa a duk lokacin da so ya samu‚ to‚ ba abin da ya kai shi daɗi‚ shi ne ya kwatanta abin da sarki.     

2.2.2 Sadaukar Da Kai Yayin Biɗar Masoyi
A wannan gaɓa Hamisu na ƙoƙarin wayar da kan samari cewa‚ su suka fi wahala a harkar soyayya. Ita mace ba ruwanta‚ tana iya mutuwa da so ba ta sanar ba. Amma kai saurayi da Allah ya ɗora ma wannan hidima dole ka yi haƙuri dole ka sadaukar da kai a yayin da kake neman so a wurin mace. Wannan ƙaramin jigo ya bayyana a mafi yawan ɗiyan waƙar. Misali: a ɗa na 2 da na 4 zuwa na 8 da na 10 da na 12 da 13 da 17 da 21.
2
Komai ruwa da iska‚ 
A kanki ba za na daina kewa ba.
4
Ni ban ga mai harara ba‚
Bare na waiwaya ba.
In dai a kanki ne za na jure‚
Wahalar zuwa garin nisa.
6
Da an taɓa ki a jira ni don ko‚
Tilas na zo na ɗau fansa.
7
Jimirin jiranki nai don ki zo‚
Na kalle ki Gimbiyar Hausa.
8
Sirri na rayuwata ke ce‚
Kamar kin kira da na amsa.
10
In dai a kanki ne na yi nisa‚
Don ba kiran da zan amsa.
12
Sam ba batun na fasa‚
Ko za a ce min im ba da rai fansa. 
21
Yau gani har ruwa kusa da kada‚
Zo ki ceci ƙarkona.

Tun a ɗan waƙa na biyu Hamisu ya fara bayyana irin hatsari da wahalar da ke cikin soyayya. Hamisu ya bayyana yadda ake rainon soyayya cikin matsanancin hali‚ ya yi kinayar irin wahalar da ruwa da iska‚ watau irin yanayin nan da saurayi zai je gidan su yarinya amma ya same ta da wani ko ya aika amma ta ƙi fitowa duk da ta san ya san tana gida‚ ko yana tare da ita wani nata zai zo ya kore ta ko ya kore shi‚ ko wani saurayin ya zo ta bar shi‚ amma hakan ba zai hana gobe ko an jima ya dawo ba. Don haka‚ kewaye (kewa) ko dawara a kan lamarinta ba zai ƙare masa ba har sai ya cimma abin da Hamisu ya ambata a cikin ɗan waƙa na uku.
Daga ɗa na huɗu zuwa na shida ya nuna cewa duk wani magauci watau wanda ya kira da mai harara bai damu da shi ba balle abin da yake yi ya dame shi. Haka kuma ya bayyana cewa‚ shi bai damu da doguwar mata ba‚ wadda ya sifanta ta da garin nisa. Bahaushe ya ce‚ “Garin masoyi ba shi nisa.”

Haka kuma daga ɗa na 6 – 8 da kuma 10. A ɗa na 6 Hamisu ya bayyana yadda giyar soyayya ta sanya masoyi yake ganin kamar ya fi kowa‚ har yake ganin ya sami nasara a kan ko ma waye ya taɓa masa gimbiya. Don haka‚ da an taɓa ta fansa kawai zai zo ya ɗauka. Ɗa na 7 kuma‚ ya bayyana yadda yake da haƙuri a kan masoyiya‚ duk yadda za ta daɗe ba ta zo ba‚ to‚ zai daure ko da kuwa idan ta zo kallonta kawai zai yi ta koma. 
A ɗa na 8 ya ƙara fito da ƙawa zuccinsa da yake cewa da ya ga alamun za ta kira shi zai amsa don yana ƙawa zuccinta kuma yana son kasancewa tare da ita. A ɗa na 10 Hamisu ya bayyana cewa‚ in dai a kan masoyiya ce ya yi nisa ya sadaukar da kansa gareta ba zai amsa ma kowa ba.

A ɗa na 12 da na 21 a nan ne jarumin ya kai kansa ga mahalaka‚ inda ya bayyana cewa‚ shi ba batun ya fasa soyayya ko da zai bayar da ransa don ya fanshi gimbiyarsa. A ɗa na 21 ya nuna inda soyayya ta kai shi tsakiyar magauta da suka fi ƙarfinsa‚ wanda ya kira su ruwa da kada watau sun fi ƙarfinsa‚ don haka‚ ba kunya yake neman ta zo ta fanshe shi tun kafin ya rasa ƙarkonsa‚ wanda fansar ita ce ta so shi. 

2.2.3 Bayyana Soyayya Ga Wadda Ake So   
Bayyana wa masoyiya soyayya wani ƙaramin jigo ne da ya ratsa wannan waƙa‚ misali: ɗa na 1 da na 3 da 5 da 7 zuwa 15 da 17 zuwa 20 da 22 zuwa 24 duk ɗiya ne da suke bayyana so ga wadda ake so.

2.2.3.1 A ɗa na 1 da na 3 da na 5 ya bayyana soyayyarsa ne ta hanyar amfani da salon da zai ƙara zaburar da masoyiyar ta so shi‚ shi ne yake bayyana cewa ashe tuntuni da rai yake son ta ba da zuciya ba. Sannan idan ya samu kutsawa ko da‚ da ƙarfi ne shi ba zai damu da abin da ya wuce ba. Kuma duk nisa na garinsu zai je komai wahalar da ke akwai. A ɗa na 7 ya ambaci irin haƙurin da zai yi na jira don kawai ya kalle ta. Ɗa na 8 ya kuranta ta da cewa ita ce sirri na rayuwarsa watau duk wani kumari ko jin daɗi da walwala da aka ga yana ciki ita ce saboda ta ba shi zumar soyayyarta ya sha. 

2.2.3.2 A ɗa na 13 – 15 nan ne ya miƙe ya fi faɗin son ransa‚ zubi da tsarin waƙar ma suka sauya ya ƙara wa ɗiyan waƙar yawa maimakon bibiyu da ya koro da su sai da suka zama hurhuɗu. Hakan ma bai isa ba  har sai da ya aro harshen Larabci kai tsaye ya sanya a ƙarshen ɗa na 14.  

A ɗa na 13 ya yabi diri na gimbiyar ya nuna ta cika goma kilan ma sha biyu‚ sannan wannan tsari nata kai tsaye ya kama zuciyarsa. Ba abin da ya kai zuciya ko mafarki ƙawata wa mutum son rai ko wani abu mai daɗi da har zai ji ba ya so ya farka‚ don haka‚ ya katanta abin da mafarki wanda a ɗa na 23 yake ta ƙoƙarin ya yi wa kansa linzami yake cewa ya ɗauko abin da ya fi ƙarfinsa. 

In ba ka da masoyi ka yi kuka‚ Hamisu a ƙarshen ɗa na 13 ya bayyana so da wani mataki kuma abin buƙata a rayuwa. A ɗa na 14 ta babban mahaukaci Hamisu ya yi‚ ya nuna shi bai gani ba kuma ba abin da zai dame shi matuƙa yana ganin masoyiya a kusa da shi. A ɗa na 15 farin ciki ne da shelanta cewa shi ya gane masoyiyarsa tana tausayinsa‚ tausayi kuma mataki ne na so‚ don haka masoyiyarsa tana son sa.

2.2.3.3 A ɗa na 17 zuwa na 20 sai abin ya ƙasura‚ saboda abin ta kai ga cewa Hamisu ya shiga neman magautansa ko waɗanda ba su son sa da masoyiyarsa da ya kira da maƙƙiya, domin ya sanar da su abin da yake ciki na yadda yake samun damar iya sarrafa zuciyarsa wurin bayyana soyayyarsa.

A ɗa na 18 ya nuna cewa duk abin da yake gabatarwa a kan soyayyarsa da shiri yake yi. Daga zuciya yake shirya komai daga nan kuma sai ya sanar da masoyiyarsa da kuma waɗanda ya tabbatar suna fahimtarsa.  

A ɗa na 18 ɗimaucewa ya yi yana tambayar da babu amsa yana cewa idan babu ita ina kuma zai je‚ saboda shi bai san wata ba balle ya je ya sami sanyin zuciya. A ɗa na 20 yake sanar da cewa kowa fa da nasa amma shi gimbiyarsa ita ce cikar burinsa.

2.2.3.4 A ɗa na 22 da na 23 da kuma na 24 watakila amsa yake bayarwa ta tambayar da ya yi a sama da yake cewa in babu ita ba inda za shi‚ shi ne ya dawo yake cewa‚ komai na da mafita amma shi mafitarsa ita ce kullam ta bari ya zo wurinta kuma su yi hira har su ƙare sannan ta yi masa bankwana. Abu na gaba ya kambama gimbiyar ce ta hanyar nuna mata cewa ita matsayinta na da yawa kuma yana sama da nasa amma ya zai yi da soyayya‚ shi ne yake ce mata son ta ya fi ƙarfinsa‚ watakila ɗawainiya da ita sai dai ta yi haƙuri da abin da ya samu tun so ya shiga tsakani.  

2.2.4 Idan Buƙata Ta Biya A Soyayya
Hamisu Breaker a fagen soyayya jarumi ne shi‚ mai kasada kuma mutum ne shi mai yanke hukunci cikin sauƙi ba tare da ya tsanantawa ba. Ya nuna haƙurinsa a ɗa na 7 da ya ce zai yi jimirin jira‚ ya nuna jarunta a ɗa na 5 ya ce komai nisan gari da wahalar da za a yi kafin a je shi ya ɗauka. Har gazawarsa sai da ya nuna a ɗa na 21 ya ce ga shi a ruwa wanda hatsari ne ga kuma kada a ruwan‚ nan ma babbar damuwa ce. Amma da ire-iren waɗannan matsi da damuwa tun a farkon waƙa Hamisu ke yanke hukunci cikin sauƙi‚ ɗa na 3 ya ce ba zai tanka kowa ba idan ya same ta. A ɗa na 4 ya ce bai ga mai harara ba bare ma ya tanka masa. A ɗa na 11 da ya ga ya sami kai ya ce yadda aka gan su haka za a bar su.

Ɗungurungum‚ a ɗa na 29 – 31 a nan ne yake bayyana wasiyyarsa ga samari da ’yammata cewa idan buƙata ta biya a soyayya a yi haƙuri a kuma sa sauƙi a lamurran da suka wuce ko waɗanda ake fuskanta‚ saboda soyaya tana daɗi takan sa mutum ya zam kamar sarki kamar yadda ya faɗa a ɗa na 27.  

3.1 Zaɓen Kalmomi Da Jumloli A Waƙar Jarumar Mata
Cikin abin da ya ƙara bambanta waƙa da zance na yau-da-kullum shi ne zaɓen kalmomi‚ wanda Hamisu Breaker ya yi iya ƙoƙarinsa wurin ganin ya zaɓo kalmomi da za su yi nagarta kuma su yi tasiri a zukatan masoya da masu sauraro na waƙar jarumar mata.

3.1.1 Zaɓen Kalmomi Da Jumloli Wurin Nuna Jarunta
A yayin da Hamisu yake nuna jaruntarsa a waƙar ya zaɓi wasu zantuka da za su nuna isarsa da jaruntarsa. A ɗa na 2 ya yi amfani da “komai ruwa da iska” domin ya nuna jajircewarsa a kan irin kewar da yake yi wa masoyiyar‚ sannan ita kanta kalmar “kewa” zaɓaɓɓiya ce da ya yi amfani da ita domin ya nuna juyayinsa da begenta da yake yi a lokacin da ya zama shi kaɗai.
A ɗa na 4 ya yi amfani da kalmar “garin nisa” ya kuma yi amfani da kalmar “jure” da “wahala” saboda ya nuna matuƙar sadaukar da kai da ya yi wurin neman soyayyarta komai nisan gari komai wahala ya ɗauka zai yi zai je.

A ɗa na 6 ya faɗi “tilas na zo na ɗau fansa” wannan ma zaɓaɓɓiya ce domin ya nuna cewa shi dai ba kanwar lasa ba ne da har wani zai zo ya taɓa masoyiya kuma ya tafi siddan ba abin da ya faru‚ don haka‚ fansa ce a kansa da sai ya biya.

A ɗa na 7 da na 12 ya yi amfani da “jimirin jira” nan ma don ya nuna matuƙar jaruntarsa na haƙuri. Ya kuma kira ta “Gimbiyar Hausa” don ya nuna isarta da ɗaukakarta. Kalmar Hausa a nan yana nufin ƙasar Hausa ga ba ɗayarta ita ce gimbiyarsu – wannan zulaƙe ne. Amma dai ita masoyiyar za ta ji daɗi tun da masoyi ne ya gaya mata haka.

A ɗa na 26 masoya ya yaba‚ amma haƙiƙanin abu kansa yake nufi. Ya ambaci kalmar “jurau amma fa a gurina” don ya jawo hankalin masoyiyarsa ta fahimci irin jarunta da halin da yake ciki.

 3.1.2 Zaɓen Kalmomi Da Jumloli Wurin Nuna Yabo
A wannan gaɓa ɗan waƙa na 13 da 14 sun ishe mu misali‚ saboda ya yi wannan yabo har sai da ya sauya ƙa’idar ɗiya na waƙar daga layuka bibiyu zuwa hurhuɗu ya yabi dirinta da irin yadda ta mamaye zuciyarsa‚ a ɗa na 14 kuma ya nuna ba shi da wata matsala in dai tana kusa da shi.

3.1.3 Zaɓen Kalmomi Da Jumloli Wurin Bayyana Jigon Waƙar
A nan shi ne yadda ya yi amfani da jerin sarƙe wurin yin wasiyya ga samari da ’yammata‚ ya zaɓi jumloli da ba su da wahalar faimta a ɗa na 29 da 30 da kuma 31 da ya yi ta maimata faɗin “masoyi yana da rana.”

4.1 Tattauna Batutuwa A Waƙar Jarumar Mata
Waƙar jarumar mata‚ waƙa ce wadda za a iya cewa ta karɓu a cikin al’umma‚ kuma masu kushe ta ba su da yawa. Hamisu Breaker ya yi matuƙar ƙoƙarinsa wurin bayyana tunaninsa da yadda yake yanke hukunci cikin sauƙi a lokacin da ya kai gaci na soyayya. Sai dai‚ idan aka kwatanta yadda Bahaushe yake kallon abubuwa‚ za a ga abin da sake tun da an ba mai kaza kai. 

A yayin soyayya Hamisu ya nuna kaiwa maƙura a kan gwagwarmayarsa wanda shi Bahaushe ba ya so a wuce makaɗi da rawa. Misali a ɗan waƙa na 2 da na 12 ya nuna cewa komai ruwa komai iska ba zai daina kewar masoyiyarsa ba. Ɗa na 12 kuma ya ce ba batun barin masoyiya ko da zai bayar da ransa a matsayin fansa gare ta. A ɗa na 6 kuma ya nuna cewa duk wanda ya taɓa masa masoyiya tilas ne ya zo ya ɗauki fansa. A ɗa na 19 ya ce idan ba ta watau idan ta mutu‚ bai san yadda zai yi ba watau ya ɗebe tsammani wanda Bahaushe cewa ya yi ba a ɗebe tsammani ga Allah – watau kullum ka sa rai cewa wani abu mai kyau zai zo maka daga Allah.
Dangane da waɗannan ɗiya da aka ambata a sama‚ Bahaushe na cewa duk abin da za ka yi‚ ka yi shi “Kadaran-kadahan” kar da ka tsinana kar da ka kaifafa‚ ko mai gina ramin mugunta ma cewa aka yi ya gina shi daidai ƙwabri kilan shi zai faɗa don haka ya fi saurin fitowa. Don haka‚ shi Bahaushe duk taurin ranka duk kasadarka bai yarda ka yi abin da za ka halaka ba‚  shi ya sa ya ce‚ “Idan so cuta ne‚ haƙuri magani ne”‚ kuma idan wata ta ƙi ka nemi wata. Sannan batun bayar da rai fansa ba ta taso ba‚ so duka so ne a wurin Bahaushe amma son kai shi ya fi. 

Ka ma duba soyayyar da ke tsakanin ɗa da uwa‚ amma da aka mari uwar rago‚ sai y ace ita ce ta ja‚ sai abin ya tsaya a kan mari kawai. Kilan da ya matsa da abin sai ya wuce mari‚ “Uwar rago ake wa jaje.” Haka kuma Bahaushe na cewa sese- sese ƙarfi bai bi jiki ba‚ a kan haka shi komai ɗan abi a hankali ne‚ saboda mari tara ba ya haɗa faɗa sai in ba haƙuri. Game da sha’anin duniya da yadda ake gabatar da soyayya ga irin abin da marigayi Sani Sabulu yake bayar da shawara ga ɗaukacin al’ummar Hausa a waƙarsa ta‚ “Sha’anin Duniya Wuya Ag Garai”:

Sha’anin duniya wuya ne da shi‚ 
In anka iya daɗi garai‚
In an yi kure akwai ’yar wuya.
    
Ka san sha’anin duniya wuya ag garai‚
In ka ga mutum kana ra’ayi nai malam‚
Kafin ku zan jiki kai da shi‚
Na so ka yi bincike nai kaɗan.

Ka bar dubin fuska da kaurin jiki‚
Na so ka yi binciken zuciya‚
Da irin halin da duk ag garai.

Ka san cinikin ɗan Adam wuya ag garai‚
Ko am bar ma sulai goma na‚
A cikin Naira rage sulai biyar‚
Watakila kana zaton faɗuwa.

Ka san hikima‚
Ka san sha’anin duniya wuya ag garai.

Sani Sabulu Kanoma          

5.1 Kammalawa 
Waƙar jarumar mata ta mawaƙi Hamisu Breaker‚ waƙa ce da ta ja hankalin duk wanda ya ji labarinta‚ saboda an wayi gari da ita a Facebook a daidai ana bikin salla ƙarama da kuma zaman killace kai yayin annobar kurona (Covid-19) magidanta na gida kuma iyalansu sun ƙara samun shaƙuwa da su a wannan yanayi inda aka ga wasu mabambanta magidanta da iyalansu suna ta tiƙa rawa da waƙar. 

An nazarci waƙar inda aka dogara da abin da kunne ya saurara na waƙar da kuma abin da aka ci karo da shi a lokacin da aka samo waƙar a YouTube an kuma nazarci waƙar bisa ga la’akari da tunanin Bahaushe. 

Dangane da zubin waƙar‚ an lura tana da ɗiya 31‚ tana da amsa amon kari na sama. Mawaƙin ya yi amfani da gaɓa –ba da –na da –sa da –ne da kuma –ki/ƙi a matsayin ƙarshen gaɓa na ɗiyan waƙar. A nazarin an nuna cewa wasiyya da ya yi wa samari da ’yammata da yin haƙuri idan an ci nasara a soyayya‚ ban da gayya ko ramuwar gayya  ita ce jigon waƙar. A wurin tattauna batutuwa a kan waƙar‚ an nuna cewa a irin hange na Bahaushe ba a so haka ba‚ don Bahashe bai yarda ka yi duk wani abu da za ka ƙure kanka ba‚ komai za ka yi ka yi shi tare da lura kada ka yi abin da za ka halaka kanka. So duka so amma son kai ya fi.

Waƙar ta yi ma’ana sosai‚ ta faɗakar ta kuma zama abin da Bahaushe yake cewa‚ “In kunne ya ji‚ gangar jiki ya tsira.”


Godiya Ta Musamman Ga:-
Dakta Hauwa Muhammad Bugaja da ke Sashen Harsuna Da Al’adun Afirka da ta bayar da lokacinta wurin duba aikin da kuma yin gyara cikinsa. ta kuma nuna cewa in har za a yi amfani da aikin ne a fagen nazari irin na makarantu ya kamata aikin ya bitar ayyukan magabata. 

Ina kuma godiya ga Malam Zakariyya Abdul’aziz na Makarantar Duniyar Computer Institute‚ Kaduna da shi ma ya bayar da lokacinsa wurin duba aiki da kuma wasu shawarwari a kan yadda aikin zai yi nagarta. 

Haka kuma ina godiya ga abokin da ya ba ni ƙwarin gwiwar yin nazarin‚ Ibrahim Usman da aka fi sani da Matashin Dattijo a masana’antar shirya fina-finai ta KANYWOOD. 

Ina godiya ga yaron da ya fara ba ni waƙar‚ Abubakar da ake yi wa laƙabi da Ɗangwari‚ 

Sai kuma godiya ga YouTube channel ɗin Hamisu Breake wanda a nan ne na sami cikakkiyar waƙar. 

Ina kuma ƙara godiya da shi Hamisu Breaker da ya samar da waƙar da kuma magidantan da suka tallata waƙar a Facebook har na sadu da ita. 

Manazarta
CNHN (2006). Ƙamusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello Printin Press Ltd.
Ɗanambo‚ A. (2008). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Zaria: Amana Publishers.
Gusau‚ S.M. (2020). Feɗe Waƙar Jarumar Mata Ta Hamisu Breaker Bisa Gadon Nazarin Waƙar Baka Bahaushiya. Da ya aika wa BBC Hausa.   

https://youtu.be/Cq_Gz7f0rgU


Comments

Popular posts from this blog

RABE-RABEN KARIN MAGANA

Rabe Rabe Karin Magana  Karin magana lokacin maguzanci  Karin magana bayan saduwa da Larabawa  Karin magana bayan zuwan Turawa  Karin magana bayan bariki ya bunkasa  Karin magana zamanin siyasa  Falama 2016 (Hausa Karin Manana)

RAGAGGEN JERIN SARKE A KARIN MAGANR HAUSA

Ragaggen Jerin Sarƙe A Karin Magana Yadda Adabin Yake JINKA YA FI GANINKA: Karin magana ce da aka yi amfani da salon sarrafa harshe wajen gina ta. An yi amfani da kalmar “ji” da “gani” waɗanda dukkansu suna iya zuwa da ma’anarsu na asali, haka kuma, suna iya zuwa da wata ma’ana ta daban. Zancen karin magana ce, ko shaguɓe, ko ma a ce habaici da ke iya zama wani abu na alheri ko akasi ga wanda aka yi wa ita. Misali akwai wani mai hannu da shuni da idan ’yan’uwansa suka zo masa da goron gayya na wani sha’aninsu, yakan kada baki ya ce da su, “Ƙafata kuke so ta so, ko hannuna kuke so ya za?”, idan suka ce ƙafa, to, zai ciko motoci da mutane su zo wurin bikin amma ba abin da zai ba su, amma suna cewa hannu, shi ke nan, zai yi masu sha tara na arziki ya yi masu fatan alheri ya ce zuwansa zai yi wuya. Haka kuma a kaikaice, karin maganar tana iya nufin wanda aka gaya wa ita, ba a son sa, wato dai ya yi zamansa a nesa ba sai an gan shi ba, an fi son amonsa daga nesa. Ko in yana nesa

HAUSA KARIN MAGANA:YARO

1) Yaro yaro ne.  2) Yaro man kaza in ya ji rana ya narke.  3) Yaro bari murna karenka ya kama zaki.  4) Ta yaro kyau take ba ta karko.  5) Yaro ko ya yi tuwo ba ya yi miya ba.  6) Abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba ya hango ba.  7) Don kana da tsawo da karfi, ba ka rankwashin yaro.  8) Inda yaro ya tsinci wuri,  nan ya fi saurin tunawa.  9) In ba a kwado da yaro,  a ba shi gishirinsa da daddawarsa.  10) Yaro fadi a watse.  11) Yaro,  yaron gobe.  12) Yara manyan gobe?  14) Abokin wasan yaro,  wanda ya ja shi.  15) Yaro nemi kudi tun abin saye bai zo ba.  16) Yaro ba ya sanin yaro ne shi sai ya yi aure an fid da shi gandu.  17) Daya matar yaro.  18) Yaro na bayan uwatai.  19) Koko abokin yara.  20) Dan yau ba a shaidarsa.