Skip to main content

YADDA SARKI FALAMA YA RASA DALOLINNSA NA YOUTUBE I


YADDA SARKI FALAMA YA RASA DALOLINNSA NA YOUTUBE I

Tambaya: Za mu so mu ji sunan baƙon namu duk da cewa sananne ne?

Falama: Sunana Muhammad Bello Falama wanda aka fi sani da Sarki Falama a dandalin Facebook ko zaurena na sarkifalamablogspot.com ko a Twitter ko a Linkedin. Ɗalibin digirin MA ne a African Literature a Sashen Harsuna Da Al’adun Afirka a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Tambaya: Sarki Falama ke nan; Digirin Em’en nan fa Masters yake nufi. 

Sarki muna yi maka fatan alheri da kuma fatan kammalawa cikin nasara. 

Ga waɗanda ba su sani ba Sarki Falama shi ne mamallakin shafin nan na Facebook da ake kira HAUSA KARIN MAGANA 

– har wa yau; shi ne mamallakin zauren nan na sarkifalamablogspot.com mai suna SARKI FALAMA da yake kawo mana abubuwan da suke na Hausa da Hausawa 

kuma kankat shi ne mamallakin tashar nan ta YouTube da ake kira FALAMA TV 
WANDA A YAU ZA MU TATTAUNA NE DA SHI A KAN WAƘOƘIN MAWAƘANMU NA DAURI DA YAKE SHIFTARSU YANA SANYA SU A TASHAR FALAMA TV; 

FALAMA DA YAWAN MUTANE SUNA MAMAKI, MUSAMMAN MA WAƊANDA SUKA SAN KA KUMA SUKE KUSA DA KAI SUKE TAMBAYAR YAYA KAKE YI KAKE WANNAN AIKIN MAI WUYAR GASKE; 
A YAUSHE KAKE SAMUN WANNAN LOKACI NA WANNAN SHIFTAR DA KAKE YI;

KUMA KAKE YIN WANNAN RUBUTU HAR KA TURA WA MASOYA;

KUMA WAƊANNE MATSALOLI KAKE FUSKANTA YAYIN WANNAN RUBUTUN. 

Amma kafin a ji amsar waɗannan tambayoyi; za mu so mu ji mene ne asalin ƙuduri ko abin da ka so nunawa a wannan tashar? 

Falama: Batun gaskiya abin da ke rubuci a YouTube shi ne a tashar ana so a nuna abin da ke da jiɓi da adabi da al’adun Hausawa. Amma ni a zuciyata so na yi in ɗauki KARIN MAGANA a riƙa tattauna ta ciki da bai.

Tambaya: To a faɗa mana yadda aka yi ka sauya ka dawo ka tare a kan shifatar waƙoƙi.

Falama: Ka san Hasawa na cewa, idan ruwanka ba zai ishe ka alwala ba sai ka yi taimarka ka tashi. Gaskiya idan aka ce karin magana abu ne mai yawa da yake buƙatar mataimaka da kuma ƙarfin aljihu – bari mu yi misali da karin maganar da Hausawa ke cewa, “Izza na Kano sarauta na Sakkwato Yaƙi na Zazzau karin magana na Bauchi!” sai kana so ka yi bayaninta, ka ga dole sai ka biɗi masana na adabi da na tarihi sun gaya maka dalilan da suka saka aka keɓance kowane gari da wani abu na musamman. 

Haka kuma, ya kamata ka tafi ziyara ta gan-da-ido domin saduwa da masarautu da masana; ka ga idan ka zo kana bayani sai ya zama ba shaidar zur kake bayarwa ba, kai ganau ne kai kuma jiyau ne. Ka ga wannan ba abu ba ne ƙarami. Ka ga har da ja-gora ko ɗan-ja-gora sai ka nema; sai kuma ka nemi sanayya; in ba haka ba; ba za ta yiwu ba cikin sauƙi ba. 

Dangane da yadda na koma shiftar waƙoƙi; a darussanmu na makaranta muna yin waƙa sosai, don haka, ban da matsala, matsalar kawai ita ce da farko da na rasa abin da zan sa a tasahar sai na zauna na kasa komai ina tunanin yadda buri zai cika. Cikin ikon Allah kuma sai tunanin yin shiftar waƙa ta zo; shi ke nan sai likkafa ta ci gaba.

Tambaya: To kun ji; a yanzu haka; tashar FALAMA TV tana da SUBSCRIBERS ɗari shidda da hamsin da tara (659) da abin da YouTube ke ce wa VIEW dubu hamsin da biyar da ɗari huɗu da hamsi da takwas; kuma tana da masu bibiyarta a gida Nijeriya da Nijar da Libiya da Saudi Arebia da Cote d’lvoire da Algeria da Ghana da Cameroon da Benin da Amerika da Germany da Gabon da Sudan da Italy da wasu ƙasashe. Duk fa waɗannan abubuwa ba su kai YouTube ta fara ce wa Tashar Falama ga na goro ba; bare na a kai ga na cin nama; don haka sai masoya sun ƙara mana SUBSCRIBERS sun kai dubu an kuma yi kallo. 

Kada kuma ka manta an buɗe wannan tashar ne tun a shekarar dubu biyu da tara amma ba ta fara gudanarwa ba sai a shekarar dubu biyu da ashirin a ƙarshen watan MAYU.

Falama yanzu kuma za mu tausa zuwa ga dalilin wannan tattaunawa tamu; watau yadda FALAMA yake shiftar waɗannan waƙoƙi masu wuyar fahimta musamman ma ga ’yan zamani! 

Wasu ma da’awar suke yi bayarwa kake yi ana rubuta maka, wasu kuwa musamman ɗaliba cewa suke yi ɓagas ce ka samu saboda duk waƙoƙin suna nan a rubuce; ko dai a littattafai ko a intaneti; wani mai ƙoƙarin ya rubuta ko kuma a cikin kundayen bincike na ɗalibai, kawai kai doronsu kake hawa.

Falama: Gaskiya ne Malam Sani; ko da haka ne; shiryasu a yadda ake ganinsu suna wucewa goye da murya ai an ɗan yi ƙoƙari. Kuma ga tafiya nemansu gari-gari; jami’a jami’a; koleji koleji. Kuma waƙa ko da an same ta a rubuce ya kamata a sake sauraronta kuma a sake rubutata saboda a sami sakakken rubutu da za a iya amfani da shi. 

Amma batun gaskiya; ni ke sauraren waƙa ni ke shiftar ta ko da kuwa na same ta a rubuce sai dai wanda aka rubuta ya yi mani wani ja-goran amma ba ya hana in saurari waƙa in yi shifata ba. 

Misalin irin waɗannan waƙoƙi da ake da’awar Falama ya samu wurin wasu akwai waɗanda ni ne na rubuta su a matsayin jinga a lokacin muna jami’a wasu kuma abokaina suka rubuta irin s Ɗayyabu Musa Kona ko Mubarak Idris ko Adamu Musa da sauransu. Akwai waɗanda na samu a wurin su Dakta Abubakar Ayuba a nan dai Jami’iar Ahmadu Bello wasu kuma a wurin Dakta Hauwa Muhammad Bugaje wasu a wurin Malam Abubukar Sarki wasu a wurin Farfesa Magaji Tsoho Yakawada wasu kuma kankat a wurin Farfesa Ɗanhatu Muhammad ya ba mu ya sa aka ba mu. 

Abin da nake so ka sani Malam; wahala ake sha wurin wannan shifta – misali waƙar Ɗangiwa Zuru ta zuwa aikin Hajji, ta Bawa Rijau shekara sha biyu na yi ina so in ji me ake faɗi don in rubuta na kasa sai a cikin shekara ta dubu biyu da ashirin ɗin da ta gabata kafin na sami damar rubutata. 

Waƙar BALA YARO SADAUKI ta MAITURARE ban san me ake faɗi ba, mamakin su Umaru Ɗari da Kabiru Baƙo nake yi in na ji suna bin mawaƙin su ma suna yi – ina son waƙar amma ban san me ake cewa ba sai da naci ya yi yawa da kuma taimakon waɗannan abokan nawa gami da su Rabi’u Ahmad da Isa Ahmad sannan na rubuta waƙar, har ma wani abin sai dai su bar ni da kayana in na je gida na saurara sai in gane abin da ake cewa.
Waƙar Mamman Raba-gardama Mamman na Sanyina da ake cewa “Ya Ci Maza Ya Hori ’Yan Rinji” da waƙarsa ta “Rugum Sai Lamiɗo Tambari Sai Sarki” wadda yake kirari; tun wuraren shekara ta dubu biyu sha shida ko da sha bakwai da Mamman na Sanyinnan ya ziyarce mu na so in rubuta waƙa ba tare da saninsa ba wai ni in burge shi; amma na kasa sai a cikin shekarar da ta gabata kafin na ɗan iya rubuta ta, wasu wuraren kuwa dole na bar su.

Haka kuma; waƙar Sarkin Taushi ta “Nufinta Wasan Gargajiya” ya fi kwana sittin ina shiftarta inda ban gane zan tashi a ƙafa in taka in tafi gidan wani abokina Adamu Ɗanmasani gidan ya kai kusan kilo mita ɗaya ko fi in je in same shi in ce wuri kaza sai ya yi min dariya ya ce ai kaza aka ce wani lokaci har in yi musu da shi daga baya dole in sakar masa da haka har na rubuta.

Zakariyya Abdul’aziz, abokina ne kuma tare muke zama a majalisarmu kuma yana cikin masu taya ni idan al’amurra sun sarƙe wurin rubutu; ya nemi in rubuta waƙar NOMA ta Muhammadu Bawa Ɗan’anace Gandi – ta GARBA NA GOƊI KUTUNKUN ƁAUNA A BAR HAƊA KA DA ’YAN DAGAJI na kasa. Na fara rubutawa amma har yanzu abin sai a hankali amma na san zuwa gaba zai warware.

A yanzu haka Malam, a kwai wani mai bibiyar waƙoƙin tashar ina tunanin Bature ne ma; da ya nemi in ƙara rubuta wasu waƙoƙin Gambu mai waƙar ɓarayi amma har yanzu na kasa sun yi mani tsauri sai kaɗan-kaɗan nake ta yi kuma duk sa’ar da na kammala zan saka a tashar. Kuma ai akwai waƙoƙin a rubuce a cikin littafin da Farfesa Muhammad Aliyu Bunza ya wallafa kuma ina da littafin amma na fi son abin da kunnena ya saurara in rubuta – shi ya sa ma a farko-farko har na fara rubuta cewa abin da kunne ya ji ake shifta sai wasu masoya suka hana suka ce in ina rubuta haka wasu ba za su so ba sai na bari. 

Tambaya: Falama; har yanzu dai za mu so ka ƙara mana haske game da wannan rubutu na waƙoƙi da kake yi; domin a duk bayaninka ka dai faɗi cewa kai ke yi amma ba yadda kake yi ba.

Falama: Na gode, ka san abu mai wahala shi ne a tambaye ka abin da ka sani. Dangane da yadda nake shiftar waƙa; da farko da radiyo rikoda nake yi da kaset mai zare wanda ya fi wahala dole ka yi gaba dole ka yi baya wani lokaci daidai inda kake so ya wuce ko da ƙyar kafin ka same shi. Kuma amo ko sauti ba lallai ba ne ya yi maka kyau, kilan shi ya sa na sha wahala ko na kasa rubuta waƙar Ɗangiwa Zuru.  

Daga bisani sai sauraron waƙa ya dawo waya; wayoyin kuma aka yi ta inganta su. Ka nemi waƙa ko inda kake so a waƙa ya zama da sauƙi.

Da fari gaskiya a takarda nake shiftar waƙa duk gyaran da zan yi sai dai in san yadda zan yi. Amma daga bisani a computer nake yi.

Bayan haka; wani abu da ya ƙara taya ni aikin shi ne igiyar saurare ta kunne. Da farko sai in nemi mai sauƙin kuɗi in saya; shi ma ba biyan buƙata; bai bayar da amon da ake so. Yahuza Soja ya ce min mai tsada za ka saya; da kuma na sami mai tsadar sai aikin ya ƙara sauƙaƙa.

Don haka; bayan na sauriri waƙa; na yi shifta a computer nakan ƙara saurara in yi gyare-gyare ko dai na wani abu da ban tantace da shi ba ko kuma gyaran ƙa’idojin rubutu. Wani gyaran ma sai in ina mayar da abin bidiyo kafin nake yin sa.

Kuma kamar yadda na faɗa; so da yawa abokai kan taimaka mani wurin saurare da fahimtar abin da mawaƙi ke faɗi wani abun kuwa dole ne in haƙura da shi. Misali Waƙar Babban Jigo Na Yari Uban Shamaki ta Alhaji Musa Ɗanƙwaro mun fi awa biyu muna tattauna wani wuri a waƙar Sani Baharu ya faɗi abin da ya fahimta Alhaji Nuhu ya faɗi nasa Isa da Rabi’u su ma su faɗi nasu har sai da magariba ta gabato sannan muka ƙyale washe gari kuma muka ci gaba.   

Tambaya: Sarki Falama shin me ke ba ka dama har kake iya fahimtar waƙoƙin nan har kake shiftarsu?

Falama: Batun gaskiya; karatu ne; duk yadda ka so ka yi; matuƙar ba ka iya ba, to, ba za ka yi ba: akwai yadda ake rubuta waƙa: idan waƙa ta solo ce watau waƙar mutum ɗaya ke yin ta ba ’yan amshi; akwai yadda ake rubuta ta; ka ga ni don ta yi min sauƙi lambobi nake sanyawa a kowace gaɓa da na tantance.

Sannan waƙa idan akwai amshi ko karɓi ko karɓeɓeniya akwai yadda ake rubuta ta; kuma hakan nake rubuta su; sai dai idan na zo sanya su a hoto dole ne na cire cewa nan wurin ja-gora nan wurin karɓi ko nan wurin amshi don murya ake ji kuma ita za ta yi maka irshadin cewa wannan amshi ne ko murya uban waƙa ce. Sai dai abin da nake yi nakan sanya alamar dagi domin raba tsakanin muryar uban waƙa da muryar masu amshi.

Sanin wasu labarurruka na al’umma ko tarihi ko wasu waƙoƙi idan kana saurara yakan taimaka maka wurin fahimtar abin da mawaƙi yake faɗi a waƙa – idan ka san gari da ya ambaci wuri ka san suna idan kuwa ba ka sani ba, ba yadda ka iya sai ka rubuta yadda ka ga dama.

Haka kuma sanin karin harshen al’umma yana ƙara taimakawa wurin fahimtar abin da mawaƙi yake faɗi duk wanda bai san wannan ba, lallai ne a sami kurakurai a rubutunsa.

Sannan sanin Hausa da ƙa’idojin rubutunta na taimaka wa mai shifta wurin shifta cikin tsafta don ya san abin da yake yi. 

Tambaya: Waɗanne mawaƙa ne ka fi samun sauƙi wurin rubuta waƙoƙinsu?

Falama: Akwai Dakta Mamman Shata shi ma ba a kullum ba don akwai waƙoƙi da yawa nasa da nake son in rubuta na kasa – misali waƙar Bawa Direba ita ma sai da taimako na kammala har na tura ta YouTube Yahuza Mohammed ya yi mini gyara a amshin don haka sai na sauke ta na gyara kafin na sake turawa. Don da farko akwai wani masani a waƙar Shata da na aika masa da tambaya sai ya yi tunanin gatse nake yi masa sai bai ba ni amsa ba, ni kuma sai na tura da kurakurai. Sani Aliyu Ɗandawo waƙoƙinsa na yi mini sauƙi, Sani Sabulu ma haka – amma Ɗanƙwairo yana ba ni wahala; Narambaɗa ma haka sai dai bai kai na Ɗanƙwairo wahala ba.

Tambaya: Shin zuwa yanzu; yadda ake batun COPYRIGHT me za ka iya cewa dangane da waƙoƙin da kake amfani da su?

Falama: Ka san akwai mutanen kirki; da ka yi maganar Copyright sai ka tuna mani wani da ke da wata tasha a Facebook da kuma YouTube ana ce wa tashar TSOHUWAR AJIYA na san abin da na sani na Copyright don Dakta Shu’aibu Hassan aji na musamman ya yi mana a kan haka da na komawa makaranta; amma da na yi nufin in yi wannan shifta sai na tambayi abokina Ibrahim Usman Matashin Dattijo a KANNY WOOD mai tashar ZUMAR AREWA game da yadda copyright yake a YouTube don yana gaba da ni; shi dai cewa ya yi in kiyayi wannan harka don ya san in mutum ya saɓa har rufe tasha ake yi duk kuwa yadda ta bunƙasa.

Daga nan sai na koma wurin mai TSOHUWAR AJIYA don shi haka kawai yakan neme ni ya ba ni shawara; na ƙyara masa abin da nake son yi na shiftar waƙa ina sanyawa a tashata; sai ya ce gaskiya akwai batun copyright amma mu a Hausa ba kowa ba ne ya damu da ya bi wannan haƙƙi; amma yanzu in zan iya yin kasada ina iyawa in saka kuma abu ne mai kyau kuma in na yi sa’a ba wanda zai biyo ni. Na yi godiya daga nan sai na fara sanya waƙoƙin da na gyara.

Ana nan sai ran nan na shiga wurin da ake cewa YouTube Stodio Dashboard sai na ga waƙoƙi kusan goma sha duk ana tuhuma ta cewa na shiga hurumin da ba nawa ba. Ko dai in sassauta muryar a bar ji sai hoto ko in cire bidion ko kuma in bari amma ba ni da komai da za a biya ni a kan wannan aiki. Ko kuma in zan iya in amsa tuhumar da ake yi na copyright.

Na shiga damuwa na rasa wanda zan tuntuɓa; can sai na tuna wani aboki mai gidan dambe da ya yi mini barazanar cewa na ɗauki waƙarsa na yi amfani da ita, na ce koma dai shi ne ya kai ni ƙara? Daga nan sai na tuna cewa wani aboki Abdul Yasayyadi mai tashar FAIDHA TUBE ya taɓa ba ni labarin cewa wani ya taɓa tuhumarsa da Copyright a kan wani LABULE da ya yi amfani da shi a wani aiki, da ƙyar ya samu ya kuɓuta. Sai kuma na tuna SAGIR TAMBUWAL mai tashar ICT HAUSA shi ma ya sami irin haka a kan wani  kiɗa da ya yi amfani da shi – daga nan sai na nemi SAGIR TAMBUWAL na gaya masa abin da ke faruwa sai ya ce da ni ai sam a waya ba za ka iya komai ba sai ka sami Computer a nan ne za ka shiga DISPUDE ka yi rubutu ya dai gaya mini yadda zan yi. 

Daga nan cikin dare na haɗa computer na yi kamar yadda ya shaida min. A washe gari sai aka turo min cewa waƙa guda ɗaya ta barranta daga copyright wannan waƙar kuwa ita ce WAƘAR JARUMAR MATA ta Hamisu Breaker. Sauran waƙoƙin kuwa aka ce sai sun kwana talatin idan mai ƙara bai ce komai ba. Daga ƙarshe dai duk sauran ma an cire su. 

Tambaya: Muna godiya ga Allah, in Allah ya so a hirar mu ta gaba za mu ji yadda Falama ya dawo da dalolinsa na YouTube.

Wanda ni Muhammad Sani Jafar na gabatarwa
Sarki Falama Da Yadda Yake Shiftar Waƙoƙi
21/01/2021

Comments

Popular posts from this blog

Ranar Hausa

Ranar Hausa Ta Duniya Inda Gizo Yake Saƙarsa: Hausa Ci Gaban Mai Ginan Tukwane Ko Ci Gaban Mai Haƙar Rijiya? 26/08/2023 Shin wannan ba son uwar dawa kawai ake yi wa harshen Hausa ba, har ma da romon baka. Akwai rubuce-rubuce da yawa da aka yi cikin harshen Hausa da suka haɗa da: Rubutattun waƙoƙin Hausa Waƙoƙin baka Rubutattun waƙoƙi na zamani Waƙoƙin baka na zamani Rubutaccen wasan kwaikwayo Wasan kwaikwayo na rediyo da na talabijin da na kuma bidiyo Wasan kwaikwai mai JERENGIYA (mai goyo ko mai dogon zango) Jaridu da mujallu na Hausa Gidajen rediyo da na talabijin da ake gudanar da su da Hausa Jami’o’i da kwalejin ilimi da na kwalejin kimiyya da fasaha da ake nazarin Hausa Sai dai wa ke karantar Hausa a mataki na JAMI’A ko KWALEJIN ILIMI ko KWALEJIN KIMIYYA DA FASAHA? Wa ke so ɗansa ya karanta Hausa a kowane irin mataki? Me ya sa a lokacin ɗaukar jarrabawar SAKANDERE yaranmu ba sa so su sanya Hausa a cikin jerin takardun da suke so su rubuta? Me ya sanya a swance ko ...

Hausa Karin Magana

29/11/2019 Duk wanda ya ɗauki namiji uba, zai mutu maraya. Duk wadda ta ɗauki namiji uba, za ta mutu marainiya. Duk wanda ya ɗauki namiji uba, za ta mutu ba a mata gara ba. Namiji ba ɗan goyo ba.  Salon Tsari Na Karin Maganar  Duk waɗannan karin maganganu ne na Hausawa kuma sun hau kan tsari. Idan aka duba za a ga karin magana ce mai ɓarayi biyu: Sashen farko: Duk wadda ta ɗauki namiji uba, = gaɓoɓi 11 Sashe na biyu: Za ta mutu mareniya. = Gaɓoɓi 8 Duk wadda ta ɗauki namiji uba/ za ta mutu marainiya. 11/8 Wannan salo ne da zubi na karin maganar Hausa, wani lokaci za a ga sashen dama ya fi yawan gaɓoɓi, wani lokaci kuma hagu ya fi yawa, a wasu wuraren kuma su zama ɗaya, amma kuma za a ga ma’ana ta tafi yadda ake so ba tare da ta ɓaci ba. Yadda Ake Amfani Da Karin Maganar Mata su suka fi amfani da wannan karin maganar, kuma suna amfani da ita ne a lokacin da namiji ya yi masu ba daidai ba, sai su faɗi wannan karin maganar da nufin su nuna masa cewa, ai da ma suna san...

JERIN SARKE A WAKOKIN BAKA NA HAUSA NA MUHAMMAD BELLO FALAMA 2015

Babi Na Ɗaya Gabatarwa 1.1      Shimfiɗa Waƙa, walau ta baka ko rubutacciya, wani muhimmin ɓangare ne na adabin al’umma. Masana sun yi nazarce-nazarce da dama kan jigo da salo, da kuma zubi da tsarin ire-iren waƙoƙin da ake da su na Hausa. Ta fuskar irin waɗannan nazarce-nazarce ne aka gano saƙonni da salo da kuma zubi da tsari da ma wasu abubuwa na daban da suka ƙunsu a cikin waƙoƙin baka na Hausawa. Wannan nazari ya ɗora ne a kan ire-iren nazarce-nazarcen da aka yi kan waƙoƙin baka na Hausawa, inda aka ɗauki jerin sarƙe aka nazarce shi. An ga yadda yadda maimai ke taka rawa wurin haifar da jerin sarƙe nau’o’insa. Jerin sarƙe, zance ne wanda aka sarƙa a falan biyu ko fiye, wato inda aka samu daidaito na sunaye ko yankuna ko kalmomi ko aka samu wani irin zubi mai burgewa, da aka samu ɓuraɓusai a cikinsa. An yi bayanin nau’o’in jerin sarƙe da suka haɗa da “Cikakken Jerin Sarƙe” da kuma “Ragagge Jerin Sarƙe”, tare da la’akari dadalilan da suke haif...