Skip to main content

SHAWARA GA MARUBUCI SCREENPLAY I

Screenplay
      FADE IN
1.   KADUNA GIDAN S FALAMA - DAY
 
 Cliphanger:
 Suspense ne da marubuci ke kokarin    sakawa a karshen episode domin ya rike 'yan    kallo. Yana da kyawu amma a duk lokacin da marubuci ya fi mayar da hankalinsa ga cliphanger labarinsa zai sami nakasu saboda ba zai yi tunanin komai ba sai wannan.
                                                                  CUT TO:
2.   KADUNA GIDAN S FALAMA  - DAY
Shawara dole ne marubuci ya zama mai kaifin basira ta yadda za rika tuna dukkan labarinsa kuma ya zama kwararre ta yadda zai iya saka cliphenger ko da a scene one ne.
                                                                CUT TO:   
3.   KADUNA GIDAN S FALAMA  - DAY
Suspense shi ne ka sanya mutane dako ko tsumaye ko jira na wani romo da ka fara dandana masu.
                                                           INTER CUT
Episode
Jerin gwanon scenes ne wanda ba lallai ba ne ya zama scene goma ko biyar ko sha biyar ba. Ana bukatar episode ya yi daidai da daidaitacciyar ka'ida ta duniyar marubuta. Watau ya zama ka yi amfani da:
Font, Courrier font 
Font size 12
Kowane episode a kalla 20 pages
MONTAGE
Wanda idan ka yi haka, kowane shafi da ka daure zai ba ka kusan minti daya ne, shafi ashirin zai ba ka kusan minti ashirin da wasu Kanawa ko Zagezage a kai.
LATTER
Yi rubutunka kai tsaye, san yadda za ka gina labarinka da yadda za ka kirkiri dan wasa ka gina shi da yadda za ka gina kowane episode kuma karda ka manta da action watau aukuwa. Duk inda ya kamata ka sanya wani motsi ko emission ko sauti ka sanya shi.

Sai wani jikon.....
Sarki Falama
FADE OUT

Comments

Popular posts from this blog

Ranar Hausa

Ranar Hausa Ta Duniya Inda Gizo Yake Saƙarsa: Hausa Ci Gaban Mai Ginan Tukwane Ko Ci Gaban Mai Haƙar Rijiya? 26/08/2023 Shin wannan ba son uwar dawa kawai ake yi wa harshen Hausa ba, har ma da romon baka. Akwai rubuce-rubuce da yawa da aka yi cikin harshen Hausa da suka haɗa da: Rubutattun waƙoƙin Hausa Waƙoƙin baka Rubutattun waƙoƙi na zamani Waƙoƙin baka na zamani Rubutaccen wasan kwaikwayo Wasan kwaikwayo na rediyo da na talabijin da na kuma bidiyo Wasan kwaikwai mai JERENGIYA (mai goyo ko mai dogon zango) Jaridu da mujallu na Hausa Gidajen rediyo da na talabijin da ake gudanar da su da Hausa Jami’o’i da kwalejin ilimi da na kwalejin kimiyya da fasaha da ake nazarin Hausa Sai dai wa ke karantar Hausa a mataki na JAMI’A ko KWALEJIN ILIMI ko KWALEJIN KIMIYYA DA FASAHA? Wa ke so ɗansa ya karanta Hausa a kowane irin mataki? Me ya sa a lokacin ɗaukar jarrabawar SAKANDERE yaranmu ba sa so su sanya Hausa a cikin jerin takardun da suke so su rubuta? Me ya sanya a swance ko ...

Hausa Karin Magana

29/11/2019 Duk wanda ya ɗauki namiji uba, zai mutu maraya. Duk wadda ta ɗauki namiji uba, za ta mutu marainiya. Duk wanda ya ɗauki namiji uba, za ta mutu ba a mata gara ba. Namiji ba ɗan goyo ba.  Salon Tsari Na Karin Maganar  Duk waɗannan karin maganganu ne na Hausawa kuma sun hau kan tsari. Idan aka duba za a ga karin magana ce mai ɓarayi biyu: Sashen farko: Duk wadda ta ɗauki namiji uba, = gaɓoɓi 11 Sashe na biyu: Za ta mutu mareniya. = Gaɓoɓi 8 Duk wadda ta ɗauki namiji uba/ za ta mutu marainiya. 11/8 Wannan salo ne da zubi na karin maganar Hausa, wani lokaci za a ga sashen dama ya fi yawan gaɓoɓi, wani lokaci kuma hagu ya fi yawa, a wasu wuraren kuma su zama ɗaya, amma kuma za a ga ma’ana ta tafi yadda ake so ba tare da ta ɓaci ba. Yadda Ake Amfani Da Karin Maganar Mata su suka fi amfani da wannan karin maganar, kuma suna amfani da ita ne a lokacin da namiji ya yi masu ba daidai ba, sai su faɗi wannan karin maganar da nufin su nuna masa cewa, ai da ma suna san...

JERIN SARKE A WAKOKIN BAKA NA HAUSA NA MUHAMMAD BELLO FALAMA 2015

Babi Na Ɗaya Gabatarwa 1.1      Shimfiɗa Waƙa, walau ta baka ko rubutacciya, wani muhimmin ɓangare ne na adabin al’umma. Masana sun yi nazarce-nazarce da dama kan jigo da salo, da kuma zubi da tsarin ire-iren waƙoƙin da ake da su na Hausa. Ta fuskar irin waɗannan nazarce-nazarce ne aka gano saƙonni da salo da kuma zubi da tsari da ma wasu abubuwa na daban da suka ƙunsu a cikin waƙoƙin baka na Hausawa. Wannan nazari ya ɗora ne a kan ire-iren nazarce-nazarcen da aka yi kan waƙoƙin baka na Hausawa, inda aka ɗauki jerin sarƙe aka nazarce shi. An ga yadda yadda maimai ke taka rawa wurin haifar da jerin sarƙe nau’o’insa. Jerin sarƙe, zance ne wanda aka sarƙa a falan biyu ko fiye, wato inda aka samu daidaito na sunaye ko yankuna ko kalmomi ko aka samu wani irin zubi mai burgewa, da aka samu ɓuraɓusai a cikinsa. An yi bayanin nau’o’in jerin sarƙe da suka haɗa da “Cikakken Jerin Sarƙe” da kuma “Ragagge Jerin Sarƙe”, tare da la’akari dadalilan da suke haif...