FADE IN
INT. KASU DAY
1. Lallai ne maruci ya rubuta duk wata aukuwa (action) da rubutata ya zama tilas a kowace fita (scene) kuma kar ya zake ta yadda zai shiga aikin darecta ko na cameraman da har zai kasance yana bayyana yadda za a yi directing ko kusurwar da camera ya kamata ta kasance, sai dai in shi marubucin ne yake sa rai shi ne daraktan da zai bayar da umurni a aikin.
2. Slug line dinka kar ka yarda ya wuce liyi daya, ka kuma saukaka shi kar ka ce sai ka fadi komai - kai dai fadi yanayi na scene INT. ko EXT. sai location sai ka fadi DAY ko NIGHT yanayin description dinka shi zai nuna safe ko yamma.
3. Description dinka kar da ya yi tsawo, ka zama kwarare ta yadda cikin layi uku ko hudu za ka iya fasalta duk wani abu da kake so ya auku amma kar da ya wuce layi biyar - ka yi sassaukan bayani da ba za a ji kyuiyar karanta shi ba.
4. Ka guji bayar da labari, aukuwa kawai ake son nunawa - maimakon - a ga Falama yana sauri za shi gida - ka rubuta - Falama yana sauri za shi gida - shi ne aukuwa.
5. Haka kuma kar da marubuci ya shiga hakkin dan wasa na ya fadi duk wani abu da ya dangance shi ko duk wani abu da zai yi - kawai ka ce Falama ya dauki ruwa kofin ya fadi, ba sai ka fadi yadda kofin zai fadi ba, wannan aikin dan wasa ne da darakta.
FADE OUT
Sarki Falama
Comments
Post a Comment