Skip to main content

Bunkasar Rubuce-Rubucen Hausa


Wasu Ababe Na Daban Da Suka Taimaka Wurin Bunƙasar Rubuce-Rubucen Hausa
Tun daga lokacin da Allah Ya ƙaddara na’urar kwamfyuta ta yawaita, sai rubuce-rubuce ya ƙara sauƙaƙa ga marubuta, ta yadda za ka ga wani ma ya mallaki tasa ta kansa, don haka, ya zauna ya tsara littafi ba wata wahala ba ce tun da, da ma rubutu da na’ura shi ne mataki na cewa an ɗaura ɗambar buga littafi. Kuma wasu ababe da suka ƙara taimakawa wurin bunƙasar rubuce-rubuce sun haɗa da:

An samun da yawa daga cikin al’umma da suka iya rubutu da karatu.

Kakkafa ƙungiyoyin marubuta daban-daban.

Samuwan kamfanoni masu buga littattafai da tallata su.

An samu shagunan sayar da littattafan da ake bugawa a ko’ina.

Gidajen rediyo da ke ware filiye na musamman domin karanta littattafan marubuta da kuma yin hira da su.

Yadda da yawa daga cikin matasa sun samu sha’awar rubuce-rubuce da kuma mayar da shi sana’a.

Yadda baƙi ke zuwa daga wasu ƙasashe domin sayan littattafan marubuta su yaɗa su.

Gasanni da ake ƙoƙarin shiryawa.
Yadda ake karrama wasu daga cikin marubuta.

Samun mabincika ta marubuta a yanar gizo da ke tallata ayyukan marubuta.
Tallafi da wasu marubuta kan samu daga wasu hukumomi ko ’yan’uwa ko masoya da sauransu.

Mayar da wasu littattafai zuwa fina-finai na kallo.

Littattafan marubuta da ake sanyawa a fayafaye na CD don ka buɗe ka karanta.
Wasu jaridu da mujallu da suke ƙoƙarin sanya littattafan marubuta a ciki, kamar Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da Aminiya.

Comments

Popular posts from this blog

Hausa Karin Magana

29/11/2019 Duk wanda ya ɗauki namiji uba, zai mutu maraya. Duk wadda ta ɗauki namiji uba, za ta mutu marainiya. Duk wanda ya ɗauki namiji uba, za ta mutu ba a mata gara ba. Namiji ba ɗan goyo ba.  Salon Tsari Na Karin Maganar  Duk waɗannan karin maganganu ne na Hausawa kuma sun hau kan tsari. Idan aka duba za a ga karin magana ce mai ɓarayi biyu: Sashen farko: Duk wadda ta ɗauki namiji uba, = gaɓoɓi 11 Sashe na biyu: Za ta mutu mareniya. = Gaɓoɓi 8 Duk wadda ta ɗauki namiji uba/ za ta mutu marainiya. 11/8 Wannan salo ne da zubi na karin maganar Hausa, wani lokaci za a ga sashen dama ya fi yawan gaɓoɓi, wani lokaci kuma hagu ya fi yawa, a wasu wuraren kuma su zama ɗaya, amma kuma za a ga ma’ana ta tafi yadda ake so ba tare da ta ɓaci ba. Yadda Ake Amfani Da Karin Maganar Mata su suka fi amfani da wannan karin maganar, kuma suna amfani da ita ne a lokacin da namiji ya yi masu ba daidai ba, sai su faɗi wannan karin maganar da nufin su nuna masa cewa, ai da ma suna san...

JERIN SARKE A WAKOKIN BAKA NA HAUSA NA MUHAMMAD BELLO FALAMA 2015

Babi Na Ɗaya Gabatarwa 1.1      Shimfiɗa Waƙa, walau ta baka ko rubutacciya, wani muhimmin ɓangare ne na adabin al’umma. Masana sun yi nazarce-nazarce da dama kan jigo da salo, da kuma zubi da tsarin ire-iren waƙoƙin da ake da su na Hausa. Ta fuskar irin waɗannan nazarce-nazarce ne aka gano saƙonni da salo da kuma zubi da tsari da ma wasu abubuwa na daban da suka ƙunsu a cikin waƙoƙin baka na Hausawa. Wannan nazari ya ɗora ne a kan ire-iren nazarce-nazarcen da aka yi kan waƙoƙin baka na Hausawa, inda aka ɗauki jerin sarƙe aka nazarce shi. An ga yadda yadda maimai ke taka rawa wurin haifar da jerin sarƙe nau’o’insa. Jerin sarƙe, zance ne wanda aka sarƙa a falan biyu ko fiye, wato inda aka samu daidaito na sunaye ko yankuna ko kalmomi ko aka samu wani irin zubi mai burgewa, da aka samu ɓuraɓusai a cikinsa. An yi bayanin nau’o’in jerin sarƙe da suka haɗa da “Cikakken Jerin Sarƙe” da kuma “Ragagge Jerin Sarƙe”, tare da la’akari dadalilan da suke haif...

WAKOKIN SUTODIYO RUBUTATTUN WAKA KO WAKOKIN BAKA?

  Babi Na Ɗaya Waƙoƙin Baka   Mandawari (2004) ya nuna cewa, waƙoƙin da ake da su na Hausa sun rabu gida biyu; akwai waƙa sanan akwai waƙe. Ya bayyana waƙa da cewa, “Ita waƙa dai wata aba ce wadda mawaƙa ke rerawa da nufin nishaɗantar da mai saurare tare da taimakon abin kiɗa kamar kalangu ko gurmi ko kuma kuge da sauransu”. Matsayin Kiɗa A Waƙar Baka Duk inda ka ji kiɗa, ana neman a wataya ne, watayawa kuwa ɗaya ne daga cikin dalilan da ke sanyawa a yi waƙar baka, saboda haka, duk inda aka yi kiɗa so ake yi a ɗan sarara. Kiɗa kuwa yana sauya “waƙe” daga “waƙe” zuwa waƙa. Da farko dai mawaƙa kan kwatanta kiɗansu gwargwadon yadda zai dace da launin waƙar da suke yi, wani loakci ma ka ji kamar kana iya fassara abin da kiɗan yake nufi, musamman ma irin kiɗin masu amfani da tsarkiya da busa. A waƙar baka ta Hausa, makaɗa suna alamta abubuwa da yawa da kiɗa. Da fari wasu kan alamta cewa ga waƙa za a fara ta hanyar jinjina ganga, kowa ya ji kaɗan kafin a furt...