Skip to main content

Dakta Mamman Shata


Shata
Ai Zaman Lafiya ’Yan Nijeriya
Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Don zama lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Don zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: In kai Yamma nan har bakin ruwa;
In kai nan Gabas har bakin ruwa;
In kai nan Gusum har bakin ruwa;
Ka yi Arewa can har bakin ruwa;
Bakin iyakan Nijeriya;
Mun addu’a har fata mukai;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Kowa ya tsaya ga aiki nasa;
Kowa ya tsaya sana’a tasa;
Don zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Sa’an Yarabawa hatta Igbo;
Hausawa su da Barebari;
Hilani har ya zuwa Tiv;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Manya da yara ƙanana duka;
Mata maza kun ji mun gargaɗin;
Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Hat Terawa hatta Tiv;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A zauna babu kwaramniya;
A zauna babu hayaniya;
Ba ƙi a zucci balle a baki;
Ba ji a kunne balle jikinka;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Kwaramniyan nan waccan ta farko;
An ce mani wannan ta wuce;
Hayaniyan nan waccan ta farko;
An ce mani wannan ta wuce;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A bar son tunani ana yar da baya;
Komi ya zo anka ce ya wuce;
To dangi ku bar to kuna tuntuna shi;
Zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A’a zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Allah taimaki ’yan Nijeriya;
Allah agaji ’yan Nijeriya;
Allah ɗaukaki ’yan Nijeriya;
Don zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Kowa ya tsaya ga aiki nasa;
Kowa ya tsaya sana’a tasa;
Mu masu waƙa mu tai mui kiɗa;
Mai sai da shanu ya tai yai ta yi;
Mai sai da goro ya tai yai ta yi;
Mai buɗe kanti ya yai ta yi;
Kai dus sana’ad da duk ka’ iya;
Riƙe ta da kyawu saka ta gaba;
Mui zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mui zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ku bar son tunani kuna yar da baya;
Abin dud da anka ce ya wuce da;
Idan ya wuce to a zucci da baki;
Zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A’a zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ai zaman lafiya ba tsaigunguma;
Don zaman lafiyan ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Saurara makaɗa tafi gun kiɗa;
Kui zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Don zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ga ma kalagan nan na faɗi;
Yara ma’ansa suna jaddawa;
Zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ku gane da farkommu Nijeriya;
Ku gane da farkommu Nijeriya;
Bacci ku farka mutanen Arewa;
Da kunka farka mutanen Arewa;
Sai nad dawo ina lallaminku;
Ina kui haƙuri mutanen Arewa;
Yanzu ko na zo ina addu’a;
Kan zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Don zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Don zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: In kai Yamma nan har bakin ruwa;
In kai nan Gabas har bakin ruwa;
In kai nan Gusum har bakin ruwa;
Ka yi Arewa can har bakin ruwa;
Bakin iyakan Nijeriya;
Mun addu’a yau fata mukai;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Kowa ya tsaya ga aiki nasa;
Kowa ya tsaya sana’a tasa;
Don zaman lafiyan ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: ’Ya’yan Yarabawa hatta Igbo;
Hausawa ku da Barebari;
Hillani har ya zuwa Tiv;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Manya da yara ƙanana duka;
Mata maza kun ji mun gargaɗin;
Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Hat Terawa hatta Tiv;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A zauna babu kwaramniya;
A zauna babu hayaniya;
Ba ƙi a zucci balle a baki;
Ba ji a kunne balle jikanka;
Zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Kwaramniyan nan waccan ta farko;
An ce mani wannan ta wuce;
Hayaniyan nan wancan ta farko;
An ce mani wannan ta wuce;
To zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A bar son tunani ana waiga da baya;
Komi ya zo anka ce ya wuce;
To dangi ku bar so kuna tuntuna shi;
Zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A’a zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Allah taimaki ’yan Nijeriya;
Allah agaji ’yan Nijeriya;
Allah ɗaukaki ’yan Nijeriya;
Kan zama lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Kowa ya tsaya ga aiki nasa;
Kowa ya tsaya sana’a tasa;
Mu masu waƙa mu tai mui kiɗa;
Mai sai da shanu ya tai yai ta yi;
Mai sai da goro ya tai yai ta yi;
Mai buɗe kanti ya tai yai ta yi;
Kai dus sana’ar da dai ka’ iya;
Riƙe ta da kyawu ka sa ta gaba;
Don zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.

Jagora: Don zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ku bar son tunani kuna waiga da baya;
Abin dud da anka yawuce da;
Ya zan ya wuce tun a zucci da baki;
Zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A’a zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ai zaman lafiya ba tsegunguma;
Don zaman lafiyan ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Saurara makaɗa tafi gun kiɗa;
Kui zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Don zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ga ma kalangan nan na faɗi;
Yara ma’amsa suna jaddawa;
Zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ku gane da farkommu Nijeriya;
Ku gane da farkonmu Nijeriya;
Bacci ku farka mutanen Arewa;
Da kunka farka mutanen Arewa;
Sai nad dawo ina lallaminku;
Ina kui haƙuri mutanen Arewa;
Yanzu ko na zo ina addu’a;
Kan zaman lafiya ’yan Nijeri.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Yanzu na zo ina addu’a;
Kan zaman;
Kan lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A’a zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Kaka ta gabato ana buɗe harka;
Kowa ya manta da zance na baya;
Kowa ya zauna a kan arziki;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A’a zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ina ƙara ƙarfin mutan duniya;
Ina ƙara ƙarfin ’yan Nijeriya;
Ba Nijeriya har ƙasashen waje;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: ’Yan tsegunguma dus su shuɗa maku;
Ku manta da su yau mutanen ƙasa;
Don zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Makaɗa ko doka a kan hankali;
’Yan amshi ku amsa a kan hankali;
Ni ko Muhamman ina addu’a kan;
Zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Komiw wuce to ya zan ya wuce;
Amanta da shi sam ya zany a wuce;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Gulbi guda ne ƙasar ma guda ce;
Kogi guda ne ƙasar ma guda ce;
Gulbi guda ne ƙasar ma guda ce;
Sunan ƙasashenmu Nijeriya;
Jiha-jiha duk mun ji an yi wannan;
Amma sunanmu Nijeriya;
To da wancan jiha hag ga wannan jiha;
Zaman lafiya babu gaba ciki;
Shi mu muke addu’a ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Zaman lafiya babu gaba ciki;
Shi muke addu’a ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ba gore-gore ba ta da hankulla;
Zama kurum;
Ai zaman lafiya;
Shi ne muke wa maza addu’a;
Shi ne muke wa mata addu’a;
Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mamman shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ƙwarya idan ka riƙa anka kama;
In kai ka ja anka ja sai ta tsage;
In ko ka ja anka sau ma guda ce;
Zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mamman zaman shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mamman zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Kowa ya zauna da harshen garinsu;
Kowa ya zauna da harshen ƙasassu;
Mui roƙo ga Rabbana;
Don zaman lafiyan ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Don zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Don zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Allah taimaki ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Kai dum mai hushi;
Sai ya huce hushin shi;
Mai haddasa sai ya bar haddasa;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A’a zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ku riƙa mu gani ’yan Nijeriya;
Ku kama mana dai ’yan Nijeriya;
Ku malamai kui ta mun addu’a;
Hai malamai ai ta yin addu’a;
Manyan ƙasa ai tai yi addu’a;
Sarakan ƙasa ai ta yin addu’a;
Mu ko mu ɗauka muna gargaɗin;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Komiw wuce to ya zan ya wuce;
Komis shige to ya zan ya shige;
Komiy ya shuɗa to ya zan ya shuɗa;
Zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Zama ba tunani shi yaf fi kyau;
Tuna baya yakan sa hargitsi;
Tuna baya yakan sa yamutsi;
Tuna baya yakan sa tunzuri;
Mu zaman lafiya shi yau yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Faɗa ma wancan ya bar raina wanca;
Ce wa waccan ki bar raina waccan;
Aikin da take ke ma yi naki;
Kai ma wancan ka bar raina wancan;
Aikin da yake ka je yi naka;
Zaman lafiya shi yau yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mui zaman lafiya shi yau yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Jiha goma sha biyu anka shirya;
Jiha goma sha biyu anka shirya;
Waccan da waccan daidai wa daida;
Waccan da waccan daidai wa daida;
Yo ba hushi ba fashin bambanci;
Zaman lafiya shi yau yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A’a zaman lafiya shi yau yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Iyamurai har zuwa Yarbawa;
Tiv kana zuwa kan Fulani;
Barebari Hausawa mu nan;
Zaman lafiya shi yau;
Mamman zaman lafiya shi yau yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: To kar ka ce ka fi wancan da wancan;
Zama lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A’a zaman lafiya shi yau yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Koz zauna hanya yana hiratai;
Yana haddasa hargitsi duniya;
Bai ɗau ɗabi’ar da ke fissai ba;
Zaman lafiya shi ne mun fi so.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mamman;
Zaman lafiya shi ne mun fi so.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mu dai zaman lafiya ba tsaigunguma;
Shi yau muke so a Nijeriya;
Ga malamai nan suna addu’a;
Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ruwa da iska dare har da rana;
Zaman lafiya shi yau yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Da ruwa da iska dare har da rana;
’Yancinmu ya samu hannunmu yau;
Don zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Zama lafiya shi ke sa;
A’a zama lafiya mai sa arzuƙa;
Zama lafiya ke sa arzuƙa;
Shi zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mui zaman lafiya mai sa lafiya;
Dum mu taru mu zauna lafiya;
Mui zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Shata Muhamman yana gargaɗi;
Shata Muhamman yana gargaɗi kan;
Zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mamman zama lafiyan ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Da farko na ce duk ku farka maza;
Da kunka farka nai godiya;
Na ce ku mu kwantad da hankalinku;
Da kunka kwantar nai godiya;
Ga shi ƙarshe nai maku gargaɗi kan;
Zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ga shi ƙarshe nai maku gargaɗi;
Kan zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Tau!
A’a zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: To ni ba ni so in ji kar in gani;
Ni ba ni so in ji kar in gani;
Ban son ina jin ɗan yamutsi;
Ban son ina jin ɗan hargitsi;
Ai zama lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Kowa ke sana’a ya hau kan sana’arsa;
Don lafiyan ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Yau kui zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A’a ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Yawan son tunani ka sa hargitsi;
Yawan son tunani ka sa yamutsi;
Yawan tuna baya ka sa tunzuri;
Ai zama lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mamman zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ko bacci nike yi idan anka tasan;
An ce yi waƙa ta Nijeriya;
In na buɗe baki ina kaifafawa;
Zaman lafiya;
In ce zama lafiya shi ne naf fi so.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mamman zama lafiya shi ne naf fi so.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Bakim matuƙar mai hankali;
Bakin matsayin mai hankali;
Shi da mai nema yai arziki;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi so.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mu faɗo maganaƙ ƙasashen waje;
Da maƙwabtammu da na can nesa;
Balle fa mu ’yan Nijeriya;
Duz zama lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Nijeriya ga ta mai kwar-jini;
Nijeriya ga ta mai kwar-jini;
Farin-jini na a Nijeriya;
Ga kwar-jini nan a Nijeriya;
Ga arziki nan a Nijeriya;
Amma cikar arzikin nan ƙasar;
Kana cikar kwar-jinin nan ƙasar;
Kana cikar arzikin nan ƙasar;
Mui zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Sai an zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Ko ni Muhamman Shata na Yalwa;
Ko ni Muhamman Shata na Yalwa;
Nai gargaɗi gun jihahen Gabas;
Nai garhaɗi gun jihahe na Yamma;
Nai gargaɗi gun jihahen Gusum;
Nai gargaɗi gun jihan nan Arewa;
Zaman lafiya;
Dangi zaman lafiya shi yau yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A’a zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Farin jini na a Nijeriya;
In zaman lafiya Mamman;
Ah; in zaman lafiya ya zauna mata.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mu daure a zucci mu daure a baki;
Mu daure a kunnemu;
Kai ’yan’uwana; 
Zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A’a zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Kai ’yan’uwana ina gargaɗi;
Jiha goma sha biyu anka shirya;
Da wancan da wancan jiha sun yi daidai;
Waccan da waccan jiha ta yi daɗi;
Waccan da waccan jiha ta yi garɗi;
Zaman lafiya shi ke kawo haka.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: A’a zama lafiya shi ke sa haka.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Zama lafiya ’yan Nijeriya;
Zaman lafiya ’ya Nijeriya;
Yakan sa ilimi na bayyan;
Yakan sa arziki na ƙaruwa;
Yakan sa lafiya a cikin ƙasa;
Don zaman lafiya ’yan Nijeya.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.
Jagora: Mata maza ’yan Nijeriya;
Mata maza ’yan Nijeriya;
Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau.
Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Ranar Hausa

Ranar Hausa Ta Duniya Inda Gizo Yake Saƙarsa: Hausa Ci Gaban Mai Ginan Tukwane Ko Ci Gaban Mai Haƙar Rijiya? 26/08/2023 Shin wannan ba son uwar dawa kawai ake yi wa harshen Hausa ba, har ma da romon baka. Akwai rubuce-rubuce da yawa da aka yi cikin harshen Hausa da suka haɗa da: Rubutattun waƙoƙin Hausa Waƙoƙin baka Rubutattun waƙoƙi na zamani Waƙoƙin baka na zamani Rubutaccen wasan kwaikwayo Wasan kwaikwayo na rediyo da na talabijin da na kuma bidiyo Wasan kwaikwai mai JERENGIYA (mai goyo ko mai dogon zango) Jaridu da mujallu na Hausa Gidajen rediyo da na talabijin da ake gudanar da su da Hausa Jami’o’i da kwalejin ilimi da na kwalejin kimiyya da fasaha da ake nazarin Hausa Sai dai wa ke karantar Hausa a mataki na JAMI’A ko KWALEJIN ILIMI ko KWALEJIN KIMIYYA DA FASAHA? Wa ke so ɗansa ya karanta Hausa a kowane irin mataki? Me ya sa a lokacin ɗaukar jarrabawar SAKANDERE yaranmu ba sa so su sanya Hausa a cikin jerin takardun da suke so su rubuta? Me ya sanya a swance ko ...

JERIN SARKE A WAKOKIN BAKA NA HAUSA NA MUHAMMAD BELLO FALAMA 2015

Babi Na Ɗaya Gabatarwa 1.1      Shimfiɗa Waƙa, walau ta baka ko rubutacciya, wani muhimmin ɓangare ne na adabin al’umma. Masana sun yi nazarce-nazarce da dama kan jigo da salo, da kuma zubi da tsarin ire-iren waƙoƙin da ake da su na Hausa. Ta fuskar irin waɗannan nazarce-nazarce ne aka gano saƙonni da salo da kuma zubi da tsari da ma wasu abubuwa na daban da suka ƙunsu a cikin waƙoƙin baka na Hausawa. Wannan nazari ya ɗora ne a kan ire-iren nazarce-nazarcen da aka yi kan waƙoƙin baka na Hausawa, inda aka ɗauki jerin sarƙe aka nazarce shi. An ga yadda yadda maimai ke taka rawa wurin haifar da jerin sarƙe nau’o’insa. Jerin sarƙe, zance ne wanda aka sarƙa a falan biyu ko fiye, wato inda aka samu daidaito na sunaye ko yankuna ko kalmomi ko aka samu wani irin zubi mai burgewa, da aka samu ɓuraɓusai a cikinsa. An yi bayanin nau’o’in jerin sarƙe da suka haɗa da “Cikakken Jerin Sarƙe” da kuma “Ragagge Jerin Sarƙe”, tare da la’akari dadalilan da suke haif...

Hausa Karin Magana

29/11/2019 Duk wanda ya ɗauki namiji uba, zai mutu maraya. Duk wadda ta ɗauki namiji uba, za ta mutu marainiya. Duk wanda ya ɗauki namiji uba, za ta mutu ba a mata gara ba. Namiji ba ɗan goyo ba.  Salon Tsari Na Karin Maganar  Duk waɗannan karin maganganu ne na Hausawa kuma sun hau kan tsari. Idan aka duba za a ga karin magana ce mai ɓarayi biyu: Sashen farko: Duk wadda ta ɗauki namiji uba, = gaɓoɓi 11 Sashe na biyu: Za ta mutu mareniya. = Gaɓoɓi 8 Duk wadda ta ɗauki namiji uba/ za ta mutu marainiya. 11/8 Wannan salo ne da zubi na karin maganar Hausa, wani lokaci za a ga sashen dama ya fi yawan gaɓoɓi, wani lokaci kuma hagu ya fi yawa, a wasu wuraren kuma su zama ɗaya, amma kuma za a ga ma’ana ta tafi yadda ake so ba tare da ta ɓaci ba. Yadda Ake Amfani Da Karin Maganar Mata su suka fi amfani da wannan karin maganar, kuma suna amfani da ita ne a lokacin da namiji ya yi masu ba daidai ba, sai su faɗi wannan karin maganar da nufin su nuna masa cewa, ai da ma suna san...