IDAN ZANCE BAI BI DA KAI BA AIKI ZAI BI DA KAI
A wani lokaci mai tsawo, an taɓa yin wani maƙetacin sarki wanda ba shi da yafiya a rayuwarsa. Sarkin nan yana da wani bagire da ya killace wasu kuraye guda goma, ya kiwata su ƙwarai. Buƙatarsa wannan sarki shi ne, a kullum wani daga cikin bayi ko mutanen gari ya yi masa laifi, komai ƙanƙantarsa, to, shi burinsa ya cikia; sai ya sanya a bar waɗannan kuraye sai ji yunwa sa’arnan sai a ɗauki mai laifin nan a jefa masu shi, kafin ka ce me, kurayen nan sun yagalgala shi sun cinye.
Ina ya-alla-babu ya-alla, wata rana ana zaman fada sai ɗaya daga cikin fadawa ya yi wata katoɓara, ya yi magana ba daidai ba. Nan da nan sarki ya harzuƙa, ya yi kira ga wasu bayi ya ce maza a je a jefa wannan bafade mai katoɓara wa kurayen nan. Ba shi da wani amfani in ban da ya zama abincinsu.
Bafaden nan, nan da nan ya faɗi yana ahi, yana cewa rankai daɗe ka yi mini rai, shekara goma ke nan muna tare da kai, ban taɓa yi maka kuskure ba, na tuba ka yafe mini. Sarkin nan ya ce ni ba a yi mani haka, a tafi da shi ba ya son jin wata magana daga gare shi. Bafaden nan, bai saki ba, ya sake ahi yana cewa, rankai daɗe, ina roƙo a ba ni kwana goma in ɗan ƙara shan ruwa kafin a jefa ni. Sarki ya ce, don ta kwana goma ba komai, Allah ya kai mu. Aka sa wasu su kula da shi don kar ya gudu.
Daga tashi fadanci, sai bafaden nan ya ruga wurin bawan da ke kula da kurayen nan ya roƙe shi ya ce, don Allah ina so ka ba ni dama daga yau zuwa kwana goma ya zamanto ni ne zan riƙa kulawa da waɗannan kurayen. Bawa ya yi murmushi ya ce, rankai daɗe me kuma zai haɗa ka da yi wa kuraye hidima ai aikinka ya wuce haka. Bade ya ce kar da ka damu matuƙar ka amince min, ni zan yi.
Shi ke nan bawa ya amince wa bafade ya kula da kuraye. Tun daga sannan sai bafade ya tare a wurin kuraye ya yi ta kulawa da su fiye da ƙiya, har ma abin da ba a yi musu na jin daɗi ya zamanto yana yi musu. Cikin ɗan ƙanƙanen lokaci ya saba da su sosai. Ba ya barin inda suke, nan wuni nan kwana.
Kwanci tashi ba wuya, kwanaki goma suka shuɗe, sarki ya zo aka saka masa kujera ya harɗe don ya ga yadda kuraye za su yi da bafaden nan. Aka sa bayi suka zo da shi a banƙare, aka buɗe ɗakin kuraye aka jefa shi. Jefa shi ke da wuya sai wani abin mamaki ya faru. Kowa na tunanin ya ga kurayen nan sun farauci bafaden nan, sai aka ga sun zo suna wasa da shi suna lasar masa ƙafa shi kuma yana shafa su.
Sarki ya kasa haƙuri ya zabura ya tashi ya buga tsawa, "kai me ya faru ne da waɗannan kuraye? Me aka yi musu suka zama haka?" Daga cikin gidan kurayen sai bafaden nan ya amsa ya ce, "Kwana goma na yi ina yi musu hidima, don haka a yau ba su manta da ni ba, sun tuna da ƙimata da halarcina; don haka ba su cinye ni ba duk da suna jin yunwa. Kai kuma shekara goma na yi ina yi maka hidima irin ta bauta, irin ta bawa da uban gidanda, amma rana ɗaya ka kasa tunawa da irin hidimar da na yi maka ta shekara goma, ballantana ka yafe mini laifin farko da taɓa yi maka tun shekaru goma!"
Sarki ya yi shuru, saboda maganar ta naushe shi, ya sa aka buɗe wa bafaden nan ƙofa ya fito daga wurin kurayen nan. Daga ran nan kuma sarki ya ɗauki saunar komai zai yi sai ya tauna.
Wannan fassara daga abin da aka samo
Wanda ya fassara: Sarki Falama
Babi Na Ɗaya Waƙoƙin Baka Mandawari (2004) ya nuna cewa, waƙoƙin da ake da su na Hausa sun rabu gida biyu; akwai waƙa sanan akwai waƙe. Ya bayyana waƙa da cewa, “Ita waƙa dai wata aba ce wadda mawaƙa ke rerawa da nufin nishaɗantar da mai saurare tare da taimakon abin kiɗa kamar kalangu ko gurmi ko kuma kuge da sauransu”. Matsayin Kiɗa A Waƙar Baka Duk inda ka ji kiɗa, ana neman a wataya ne, watayawa kuwa ɗaya ne daga cikin dalilan da ke sanyawa a yi waƙar baka, saboda haka, duk inda aka yi kiɗa so ake yi a ɗan sarara. Kiɗa kuwa yana sauya “waƙe” daga “waƙe” zuwa waƙa. Da farko dai mawaƙa kan kwatanta kiɗansu gwargwadon yadda zai dace da launin waƙar da suke yi, wani loakci ma ka ji kamar kana iya fassara abin da kiɗan yake nufi, musamman ma irin kiɗin masu amfani da tsarkiya da busa. A waƙar baka ta Hausa, makaɗa suna alamta abubuwa da yawa da kiɗa. Da fari wasu kan alamta cewa ga waƙa za a fara ta hanyar jinjina ganga, kowa ya ji kaɗan kafin a furt...
Comments
Post a Comment