Idan Ba Ka Ji Tsoron Allah Ba Za Ka Ji Tsoron Halittarsa
Ma’aikaciyar jinyar da ta ɗauki wannan hoto ta bayyana cewa, kwana biyar ke nan da wannan tsohon ya iso asibitin nan yana jinya; amma duk tsawon kwanaki biyar ɗin nan ba wani daga cikin ’yan'uwa ko abokai na wannan tsoho da ya zo duba shi ballantana su zauna tare da shi. Shi kaɗai yake; su kuma hakan mamaki yake ba su, a ce ga mara lafiya kuma tsoho amma ba wanda yake zuwa ganin shi.
Sai dai wani abin mamaki tsawon kwanakin nan da wannan tsoho ya yi a asibiti, wata tantabara takan zo a kullum ta shigo ta windo ta sauka a kan gadonsa ta zauna tare da shi kamar suna hira, ta zuba masa ido na ɗan wani lokaci sai ta tashi ta tafi abin ta.
Daga bisani ma’aikatan asibitin sai suka gano cewa lokacin da wannan mara lafiya yake da lafiyarsa yakan zauna a wani wuri da jama’á ke taruwa, to, wannan tantabara a wurin take; kuma kullum ya je yana ba ta abinci. To, wannan shi ne dalilin da ya sanya ita kuma kullum take ziyartansa a asibiti.
Ba a san wanda ya rubuta wannan labari ba.
Wanda ya fassara: Sarki Falama
Babi Na Ɗaya Waƙoƙin Baka Mandawari (2004) ya nuna cewa, waƙoƙin da ake da su na Hausa sun rabu gida biyu; akwai waƙa sanan akwai waƙe. Ya bayyana waƙa da cewa, “Ita waƙa dai wata aba ce wadda mawaƙa ke rerawa da nufin nishaɗantar da mai saurare tare da taimakon abin kiɗa kamar kalangu ko gurmi ko kuma kuge da sauransu”. Matsayin Kiɗa A Waƙar Baka Duk inda ka ji kiɗa, ana neman a wataya ne, watayawa kuwa ɗaya ne daga cikin dalilan da ke sanyawa a yi waƙar baka, saboda haka, duk inda aka yi kiɗa so ake yi a ɗan sarara. Kiɗa kuwa yana sauya “waƙe” daga “waƙe” zuwa waƙa. Da farko dai mawaƙa kan kwatanta kiɗansu gwargwadon yadda zai dace da launin waƙar da suke yi, wani loakci ma ka ji kamar kana iya fassara abin da kiɗan yake nufi, musamman ma irin kiɗin masu amfani da tsarkiya da busa. A waƙar baka ta Hausa, makaɗa suna alamta abubuwa da yawa da kiɗa. Da fari wasu kan alamta cewa ga waƙa za a fara ta hanyar jinjina ganga, kowa ya ji kaɗan kafin a furt...
Comments
Post a Comment