Kura ce yunwa ya sa ta shiga gari da dare, da za ta shiga sai ta wuce ta wani rugar filani amma sun tashi, ta duba ba ta samu komai ba sai wani ɗan ƙaramin akuya, mara lafiya, sun ɗauka ma ya mutu ne, suka bar shi.
Kura ta yi tsaki ta wuce tana tunanin gaba za ta samu mai mai kuma ta raina wannan da ta samu. Ta shiga gari ta ƙaraci yawonta ba ta samu komai ba, sai ta dawo za ta koma, ta ma manta da ta yi gamo a farkon shigowarta.
Ko da ta zo ta wuce rugar sai ta tuna da ta yi tsintuwaa da. Sai ta juyo ta samu wannan ɗan maraƙin tana faɗin a sa a baka ya fi a rataya.
Comments
Post a Comment