Ranar Hausa Ta Duniya
Inda Gizo Yake Saƙarsa:
Hausa Ci Gaban Mai Ginan Tukwane Ko Ci Gaban Mai Haƙar Rijiya?
26/08/2023
Shin wannan ba son uwar dawa kawai ake yi wa harshen Hausa ba, har ma da romon baka. Akwai rubuce-rubuce da yawa da aka yi cikin harshen Hausa da suka haɗa da:
Rubutattun waƙoƙin Hausa
Waƙoƙin baka
Rubutattun waƙoƙi na zamani
Waƙoƙin baka na zamani
Rubutaccen wasan kwaikwayo
Wasan kwaikwayo na rediyo da na talabijin da na kuma bidiyo
Wasan kwaikwai mai JERENGIYA (mai goyo ko mai dogon zango)
Jaridu da mujallu na Hausa
Gidajen rediyo da na talabijin da ake gudanar da su da Hausa
Jami’o’i da kwalejin ilimi da na kwalejin kimiyya da fasaha da ake nazarin Hausa
Sai dai wa ke karantar Hausa a mataki na JAMI’A ko KWALEJIN ILIMI ko KWALEJIN KIMIYYA DA FASAHA?
Wa ke so ɗansa ya karanta Hausa a kowane irin mataki?
Me ya sa a lokacin ɗaukar jarrabawar SAKANDERE yaranmu ba sa so su sanya Hausa a cikin jerin takardun da suke so su rubuta?
Me ya sanya a swance ko aka zare harshen Hausa daga zama farilla waƙi’a a SAKANDARE zuwa matakin sai ka ga dama?
Wanda bai ga uwaba ba ina zai tambayi kaka?
Wanda bai rubuta jarrabawar Hausa ba a sakandare yaushe ne zai ce yana son Hausa ko yana son ya karanta Hausa a mataki na gaba da sakandare?
Shin idan aka ƙara wasu shekara ashirin nan gaba yaya matsayin masu nazarin Hausa zai kasance a wannan lokacin – rage yawa za su yi ko ƙara yawa?
Sarki Falama
Ranar Hausa Ta Duniya
26/08/2023
Babi Na Ɗaya Waƙoƙin Baka Mandawari (2004) ya nuna cewa, waƙoƙin da ake da su na Hausa sun rabu gida biyu; akwai waƙa sanan akwai waƙe. Ya bayyana waƙa da cewa, “Ita waƙa dai wata aba ce wadda mawaƙa ke rerawa da nufin nishaɗantar da mai saurare tare da taimakon abin kiɗa kamar kalangu ko gurmi ko kuma kuge da sauransu”. Matsayin Kiɗa A Waƙar Baka Duk inda ka ji kiɗa, ana neman a wataya ne, watayawa kuwa ɗaya ne daga cikin dalilan da ke sanyawa a yi waƙar baka, saboda haka, duk inda aka yi kiɗa so ake yi a ɗan sarara. Kiɗa kuwa yana sauya “waƙe” daga “waƙe” zuwa waƙa. Da farko dai mawaƙa kan kwatanta kiɗansu gwargwadon yadda zai dace da launin waƙar da suke yi, wani loakci ma ka ji kamar kana iya fassara abin da kiɗan yake nufi, musamman ma irin kiɗin masu amfani da tsarkiya da busa. A waƙar baka ta Hausa, makaɗa suna alamta abubuwa da yawa da kiɗa. Da fari wasu kan alamta cewa ga waƙa za a fara ta hanyar jinjina ganga, kowa ya ji kaɗan kafin a furt...
Comments
Post a Comment