Skip to main content

sadik zazzab

Ratayen Wasu Waƙoƙin Mawaƙan Da Aka Nazarta
Sadik Zazzaɓi
Ba Za Su Rage Ka Da Komai Ba...
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba, x 4
: Domin ba su fi ka da komai ba, x 4
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba, 
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana gwanina ni.
 Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Ƙahharu daɗa mana rinjaye,
: A kan maƙiya ba don mu ba,
: Idan ka zamo mana jagora,
: Kaidinsu ba zai mana komai ba,
: Kai yadda kai ma Ashabil Fil,
: Ba su kumma yin ganganci ba,
: Kowa aka yi wa zalinci,
: Ba ka ƙi zama masa gata ba,
: Ka tabbata kai ne Alƙadi,
: Ƙararmu ba mu yi tag a kowa ba,
: To in har an zalince mu,
: Saka mana ba domin mu ba,
: Domin daraja ta Rasulullah,
: Ban ɗauke hijabin kuka ba.
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Ya Rabbu salati na saba,
: Duk sanda nake sai na roƙo,
: Ka yi wa mafificin bawan,
: Da kay yi kira sama yas sakko,
Karɓi : Rasulu Ma’aiki farin duba.
Jagora : Dare ɗaya kafin asbahi,
: Ya san daraja tasa tun farko,
Karɓi : Rasulu Ma’aiki farin duba.
Jagora : Ali da sahabbai nai roƙo,
: Halinsu na ɗauka nai ƙarko,
Karɓi : Rasulu Ma’aiki farin duba.
Jagora : Domin darajarsu ka dafa min,
: ....                                                     
Karɓi : Rasulu Ma’aiki farin duba.
Jagora : Harshe na Sadik ya yo waƙa,
: Ba tare da zagin kowa ba,
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Idan zakara ya yo cara,
: Ku ce asuba ta tunkaro,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Waɗansu suna tashi salla,
: Waɗansu ko ma sai ta ɗauro,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : La’alla irin tarbiyyarsu,
: Su shanye jini tamkar sauro,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Da ma a siyasa tarbiyya,
: Kowa ta gidansu ya ɗaɗɗauko,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Ga zabi yana ciwon olsa,
: Su kai wa marinsu su kai gwauro,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Abinci a rumbu ba damar,
: Ɗibarsa ba mui maka ƙarya ba.
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Suna taɗe ka kana tashi,
: Suna dukanka suna kuka,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Su ko talakawa sun gane,
: Suna daɗa sa maka albarka,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Idan suka hau mugun borin,
: Mu za mu yi wa kowa girka,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Idan zakin dawa yay gunji,
: Ya zarce ai mai tak tak tak,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : To sai Mukhtar Ramalan Yero,
: Ka tashi ka amsa sunanka,
Karɓi `: Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Farar aniya ita ce laya,
: Don ba ka ci haƙƙin kowa ba,
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Ka tashi ka ja ɗamara an nan,
: Ba za ta hana ma komai ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Kaduna a yau kai ne Gwamna,
: Ban ce ka ji tsoron kowa ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Idan suka fara sakin layin,
: Ba za mu bari su yi barci ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Su gane shuru ba tsoro ba,
: Ba zan iya jure wargi ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Murucin dutse Allah ne,
: Ke ba shi ruwa  ba bayi ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Ƙari na kunama akwai zafi,
: Ba za ta sakin shi a banza ba,
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Ka tashi ka ja ɗamara wannan,
: Ba za su hana ma komai ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Kaduna a yau kai ne Gwamna,
: Ban ce ka ji tsoron kowa ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Idan suka ƙara sakin layin,
: Ba za mu bari su yi barci ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Su gane shuru ba tsoro ba,
: Ba zan iya jure wargi ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Murucin dutse Allah ne,
: Ke ba shi ruwa  ba bayi ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Ƙari na kunama akwai zafi,
: Ba za ta sake shi a banza ba,
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Bara in tausasa harshena,
: In nuna magauta ’yan nema,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Su san Mukhtar Ramalan Yero,
: Shi ne ya zamo gugar fama,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Mai kiɗa na kare aje gangarka,
: Kura a gabanka ta taso ma,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Sannan ku faɗa wa akukuturu,
: Ɗan hakin da ka raina ya girma
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Kuregu kuma mun san ku,
: In kun ci ganima sai gulma,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Sai dai kuma in da rabon duka, 
: Bari ba ta hana komai ba,
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Muntari a kanka nake magana,
: Waɗansu sunai ma ganganci,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Kana haƙuri shi kai gado,
: Za in musu zancen bebanci,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Da o’o da o’o da shi o’on,
: Saka su a layin sokonci,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Don ka zama Gwanna shi ke nan,
: Sai ran maƙiyanka ya hau ƙunci,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Su sun zaci kai wa kanka,
: To mu sa su a layin shashanci, 
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Da wanda ya ba ka suke gaba,
: Ko da ba ka ce musu komai ba,
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Muntari a kanka nake magana,
: Waɗansu sunai ma ganganci,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Kana haƙuri shi kai gado,
: Za in musu zancen bebanci,
Jagora : Da o’o da o’o da shi o’on,
: Saka su a layin sokonci,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Don ka zama Gwanna shi ke nan,
: Sai ran maƙiyanka ya hau ƙunci,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Su sun zaci kai wa kanka,
: To mu sa su a layin shashanci, 
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Da wanda ya ba ka suke gaba,
: Ka bar su ba ka ce komai ba,
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Muntari a gurbin soyayya,
: A nan mabiya ke ƙaraji,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Hasada ko babbar cuta ce,
: Da ke kashe bawa har hanji,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Ka koyi halin Manzon Allah,
: A Ɗa’ifa ƙissar don mun ji,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Shi ya yi zaton saƙi gunsu,
: Amma suka yi mai ƙaraji,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Yara suka sa suka jefe shi, 
: Baƙar aniyarsu mu kai juji,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Har suka fasa masa goshinsa, 
: Ba tare da yai musu komai ba,
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Allahu ya nuna fushi nasa,
: Ya sa Jibirilu ya sakko ko,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Ya ce masa ni ɗan aike ne,
: A yau halaka sai an sauko,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Kai min izini in kifar da su,
: Har ma asalinsu a shasshafar,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Ko ko a sako musu duwarwatsu,
: Da zai zama aya an saukar,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Ko ko a yi tsawa ko iska,
: Kamar yanda an wa Adawa,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Nan take ya ce afuwa Allah,
: Domin ba su san matsayina ba,
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Ma’aikina in da ya so,
: Da wanga azabar sai ya yi,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Wannan haƙuri da akwai wahala,
: Mutum ya iya a cikin bayi,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : A ce maƙiyinka su saka wuta,
: Kai kuma ka sa su cikin sanyi,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Im ban da waliyyi ba mai yi,
: Don na riƙi hujja sai na yi,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Muntari ya ce ni Gwamna ne,
: Na rama abin da akwai nauyi,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Fatan da nake su fahimce ni,
: Ban tauye haƙƙin kowa ba,
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : In da hasada fa abin yi ne,
: Habu da Habin da yai rata
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : To ku maƙiyanmu ku ja layi,
: Mu mun ishi ja a gidan gauta, X2 
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba. X2
Jagora : Kan ya zama Gwamna mai yas sa,
: Ba kui masa sai day yay rata,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : To kar da ka damu da mai suka,
: Munai maka kyakkyawar fata,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Ku masu adawa sai ku mutu,
: Ba za ku hama ma...
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.
Jagora : Na so ku sani fata ta kada,
: Ba za tai gangar Sarki ba, 
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Don ba wani mai zance a haka,
: Ya ce ba za mu mayar mai ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Su wulwula dutsen yai nisa,
: Su ce kuma ba zai faɗo ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Abin jiya bai zan daidai ba,
: Mafarki ba zan lallai ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Akukuturu iya bakinka,
: Gidan tara bai zan daidai ba,
Karɓi : Ba za su rage ka da komai ba.
Jagora : Amma kuma in da rabon duka,
: Baram ba tai komai ba,
Amshi : Ba za su rage ka da komai ba,
: Domin ba su fi ka da komai ba,
: Ƙashin sama gagara ɗan kwaure,
: Gidan sama sai babban tsuntsu,
: Mazan jiya sannu mazan fama,
: Mukhtar Ramalana jan gwarzo.

Sadik Zazzaɓi
Muktari Za Mu Zaɓa...
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa,
: Ba za mu ɗau guba ba,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba,
: Ba za mu ɗau guba ba,
: Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : A Kaduna mun amunce
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Jagora : Kullum Ubangijina shi ne abin kira na,
Karɓi : Allahu shi na roƙa.
Jagora : Shi ne yake saka min hikima a zantukana,
Karɓi : Allahu shi na roƙa.
Jagoara : A Kaduna yanzu na ga birai suna ta ɓarna,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Shi ne na zo da zancen jama’a ku zo ku karɓa,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtari za mu zaɓa,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Bukunu ba zai iya ba.
Jagora : Allahu kai salati gun shugaban halittu,
Karɓi : Ya Ɗaha Annabina.
Jagora : Wannan da bai karatu kuma ba ya yin rubutu,
Karɓi : Ya Ɗaha Annabina.
Jagora : Shi ne ka bai wa ceto mai son sa zai wadatu,
Karɓi : Ya Ɗaha Annabina.
Jagora : Ni shi na runguma Annabi Ɗaha ɗan Amina,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : A Kaduna mun amunce
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Jagora : Zo ka duba zantukana ba ku saba jin ƙire ba,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Fasa ƙwai zan yi a kwalta ba lallaɓe nake ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Don na ga shi makaho bai san gani ake ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Sai ya ji ka taɓa shi sannan ya ce maraba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtari za mu zaɓa,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Kurkunu ba zai iya ba.
Jagora : Zance na ’yan siyasa kowa yana iyawa,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Rigarmu ce ta ’yanci wa zai hana mu sawa,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Wani ya sako tabarau mu ko ba ma saka ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : ’Yancinmu rayuwarmu ba za mu ɗau gara ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : A Kaduna mun amunce
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Jagora : Tarkon mahassada ne  ba zai riƙe ƙafa ba,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Ko sun yi za mu kwance ba aibu zai zame ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Harbi ga ɗan kunama gado ba ma tuna ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : A Kaduna babu wanda bai san akwai hakan ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtari za mu zaɓa,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Kurkunu ba zai iya ba.
Jagora : Kun san zuma maɗaci duk magani suke yi,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Wani ya riƙo maɗaci zai sa mu kame kame,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mun san kiyashi da ma ya saba jaye jaye,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Ko alhakin mutane bai bar shi ya sake ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : A Kaduna mun amince,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Jagora : A muhawarar siyasa ban raina ƙanƙani ba,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Zance ake da hujja ba ƙage ko musu ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Ga o’o babu hujjar bai daina kwarmato ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Kowa ya ɗau kunama ya san ba zai ga kyau ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtari za mu zaɓa,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Kurkunu ba zai iya ba.
Jagora : Tarihi a siyasa na taimakon mutane,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Don shi yake sakawa in gane wane wane,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Ya kasa inuwarsa ta waɗansu yay yi zaune,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Ya sa farin tabarau kuma ba gani yake ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : A Kaduna mun amince,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Jagora : Kun san biri da ɓarna a Abuja wa ya sa shi,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Don na ga dankali ne mai danne naƙ ƙasan shi,
Karɓ : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Yau ga shi rushe-rushen zai yi wa ’yan jihar shi,
Karɓ : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mugun nufi ga jaki ƙato ba ma musa ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtari za mu zaɓa,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Kurkunu ba zai iya ba.
Jagora : A Kaduna ’yan siyasar bana na ga har da sake,
Karɓ : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : A cikinsu har da kaji a cikinsu har da zabi,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Da mujaddadin siyasa a cikinsu wa muke bi,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Da gwagwarmaya ya saba don ba rago ba ne ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : A Kaduna mun amince,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Jagora : Da ma hawa maciji bango wuya yake sha,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Shafa’i ko shi ake yi bayan idar da isha,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Rafali ya busa wasa aka mashi babu fasha,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Don duk tsiyar maciji ba kama jaɓa zai ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtari za mu zaɓa,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Kurkunu ba zai iya ba.
Jagora : Kun san hawa maciji bango wuya yake sha,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Shafa’i ko ita ake yi bayan idar da isha,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Rafali ko zai busa wasa aka mashi babu fasha,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Duk tsiyar maciji ba kama jaɓa zai ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : A Kaduna mun amince,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Jagora : Wani guguwa ta mulki ita ce take zuga shi,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Ya raina majalisa na yarda ba ya ƙoshi,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Wai za ya nemo gwamna mun gane wa ya sa shi,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : To duk tsiyar masunci ba yashe gulbi zai ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtari za mu zaɓa,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Kurkunu ba zai iya ba.
Jagora : An ce mahaukaci wai ba duka yai iya ba,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Ya ce har kun tuna mun na manta ban hakan ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Kai baba mai tabarau ba ka daina gardama ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Talakan Kaduna ya ce bai manta mai kamar ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : A Kaduna mun amince,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Jagora : Ƙarya fure take yi ba  ta ’ya’ya a tsinka,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Tilas ka yarda o’o mun gane duk shirinka,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Ka kasa ba mu haƙƙinmu na baya wa ya saka,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Domin karo na rago ne ba na akkuya ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtari za mu zaɓa,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Kurkunu ba zai iya ba.
Jagora : Rimi adon gari ne Mukhtar na ƙara zance,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Fitala washe duhu ce in ya zamo kwatance,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtar kawai ka zarce mun daina goce-goce,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : ’Yar manuniya ta nuna ba masu wawaso ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : A Kaduna mun amince,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Jagora : Kwanɗi zuma da daɗi kowa ya sha shi zai ji,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Amma abin takaici shi ne ganin ƙudaje,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Burinsu ne su shanye jama’a ko sai ƙudaje,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtari kar ka bar su ba fa’ida ba ne ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtari za mu zaɓa,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Kurkunu ba zai iya ba.
Jagora : Duk dai da na ga cewa ai ka ishe su gayya,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Zance a kan ƙwarewa sai dai su je su koya,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Bujumin Gwamnan Kaduna Aljanna mai masoya,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Duk wanda zai taɓa ka ni dai ba zam bari ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : A Kaduna mun amince,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Jagora : Kare uban kada ne giwa karya itace,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Zaki uban dawa ne a Kaduna mun amunce,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Ka fito wa ’yan adawa don na ga sun butulce,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Yaro ba za ya gane matsayinsa ne hakan ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtari za mu zaɓa,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Kurkunu ba zai iya ba.
Jagora : Da akwai wasu mutane da halinsu ne ya sanya,
: Duk lokacin da zan waƙata ina saka su,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Shamsuddini a farko ba na ƙyale masoyi,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Halin ƙwarai gare shi ba ya halin bulayi,
: Yaya ba zan faɗi ba,
Jagora : A Kaduna mun amince,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Jagora : Sannan akwai Lawal Soja halinsa na tsuma ni,
: Lawan yana da kirki don babu mai musa ni,
: Batunsa kullu yaumin Mutkharu ne a ransa,
: Batunsa kullu yaumin Mutkharu ne a ransa,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Addu’a yake ka zarce ba laulayi yake ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtari za mu zaɓa,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Kurkunu ba zai iya ba.
Jagora : Ga ... Makama Lawo ban bari ba,
: Da akwai Aliyu Makama Lawo ban aje ba,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Sannan akwai Tanimu, Tanimu in gai da kai,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Tanimu na yaba ma aikin mun yaba ma,
: Muktari ne a ranka,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : A Kaduna mun amince,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Jagora : Ina Magaji Baswan ɗan ɗan da bai da tsoro,
Karɓi : Mukhtari za mu zaɓa.
Jagora : Don na ga ya yi dantse a kanka zai yi horo,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Magaji ya yi dantse a kanka zai yi taro,
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Ya zama haɗɗa taro a kanka bai tsaya ba, 
Karɓi : Ba za mu ɗau guba ba.
Jagora : Mukhtari za mu zaɓa,
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Kurkunu ba zai iya ba.
Jagora : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Gyauro ba zai iya ba.
Karɓi : In gaskiya ake so,
: Mukhtari za mu zaɓa,
: Kurkunu ba zai iya ba.
Jagora : Ba za mu ɗau guba ba
Karɓi : Gyauro ba zai iya ba.

Sadiq Zazzaɓi
Ka Yi  Mun Gani
Jagora : Farko da Rabba mahaliccinmu za ni fara ta,
: Shi ya ƙagi baiwar waƙa ta zan sana’ata,
: Ba ni fara komai sai na kira abin bauta,
: Ya maɗaukaki wanda ya mai da ƙanƙanin babba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa suna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Dandazon salati mara adadi ka ninka shi,
: Gun abul Batula komai nake kira sa shi,
: Rabbi har sahabbai don sun riƙo da turbar shi,
: Har da shaihunai da waliyai ba sui kasala ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jarora : A gidan rufin asiri su siyaƙi daina leƙawa,
: Mai miya da gammon kifi ya bar batun gaiwa,
: Ba mu bin kiran ɗan ware mai faɗa da saɓawa,
: Wanda yaƙ ƙiya za mu bi Gambo ɗan tatsinawa,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna ta murna,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jarora : A gidan rufin asiri su siyaƙi daina leƙawa,
: Mai miya da gammon kifi ya bar batun gaiwa,
: Ba mu bin kiran ɗan ware mai faɗa da saɓawa,
: Wanda yaƙ ƙiya za mu bi Gambo ɗan tawatsewa.
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar yai rabo kasalawa.
Jagora : Masu takaran dai uku ne ku kalli tsarinsu,
: Sai ku ɗau sikeli na awonku don ku auna su,
: An yi walƙiya du mun san irin ɗabi’arsu,
: Babu wanda bai san ruguzau tana da illa ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna ta murna,
: Kowa faɗin yake Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Magana nake ba surkulle kan siyasa ba,
: Du da na gama ba zan ƙyale ƙarin kunama ba,
: Dole ne yabo ko ba so ko ba mutunci ba,
: Tun da gaskiya ba sake kala take yi ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Ayyukan da Yakkowa ya fara yi ku dudduba,
: Mukhtari ya kammala yai su bai kasala ba,
: Wanda da a ce yai ƙyashi ba za ya ɗora ba,
: Ci gaban jihar ne a gabansa ba ɗagawa ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Ayyukan da Yakkowa ya fara yi ku dudduba,
: Mukhtari ya kammala yai su bai kasala ba,
: Wanda da a ce yai ƙyashi ba ba ya ɗora ba,
: Ci gaban jihar ne a gabansa ba adawa ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar yai rabo kasalawa.
Jagora : Shekara biyu yai ga ayyukansa madalla,
: Du abubuwan more rayuwarmu ya kalla,
: Za ni bayyana muku su al’umma cikin shela,
: Don ku gane aikin an yi shi  ba da tsaiko  ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Za ni fara zancen ilimi saboda jigo ne,
: Mukhtari mai ilimi ne saboda malam ne,
: Shi ya sa ya ba shi kulawa da za ya kankare,
: Yanzu dai jihar kan ilimi ba a yi gori ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Ayyukan da yai du ƙaramar hukuma ya shiga,
: Yai ajujuwa sababbi gininsu ƙarfafa,
: Duk faramari ta jihar ayyukansa yai rumfa,
: Mai musu ya duba muku har da kai ziyara ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Mukhtari ya rarraba littattafai na rubutu,
: Malamai ƙwararu don illimin ya ingantu,
: Duk firamarin an san gwamnatinsa ta kyautu,
: Ga shi ’yan adawa ba su sa abin fa kai kai ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar yai rabo kasalawa.
Jagora : Har da kwamfyutoci ya raba wa makarantu,
: Sun yi godiya ɗalibai na ji na ji sun gamsu,
: Illimin kimiya a Kaduna nata ya samu,
: Alfahar muke yi ba mu san rago a gwamna ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa suna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar yai rabo kasalawa.
Jagora : Sakandare sun mora abun a tsari ne,
: Yanda anka ba su kulawa nake bayani ne,
: Duba jami’o’i a Kaduna ai musali ne,
: Tun da sun ga ci gaba ba ƙanƙani ba na lura,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Ga Kaduna KASU Mukhtari shi ya gyara ta,
: Tsare-tsare masu yawa ac ciki ya inganta,
: Yanzu ga shi ko ƙasar ma ana misalinta,
: Ga Gidan Waya FCE ba za a raina ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Ga Kaduna KASU Mukhtari shi ya gyara ta,
: Tsare-tsare masu yawa a ciki shi ya inganta,
: Yanzu ga shi ko ƙasar ma ana misalinta,
: Ga Gidan Waya FCE ba za a raina ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Mukhtar sakolashif ya raba shi an karɓa,
: Ɗalibai suna yi masa godiya suna cewa,
: Ayyukan Yero mai kushe su sai mutum butulu,
: Wanda ko Ta’ala ba za ya mai ya gode ba,
Jagora : Ga Kaduna KASU Mukhtari shi ya gyara ta,
: Tsare-tsare masu yawa a ciki ya inganta,
: Yanzu ga shi ko ƙasar ma ana misalinta,
: Ga Gidan Waya FCE ba za a raina ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Mukhtaru ya ɗaukko ɗalibai ya tura su,
: Don su yo karatu a ƙasar waje nasibinsu,
: Ga shi ba sanayya ƙazon su ne tafarkinsu,
: Shekara talatin wani ba kwatanta wannan ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Za na bar batun ilimi tun da ba ya ƙarewa,
: In taho batun ƙarfin lafiya na nunawa,
: ’Yan uba su gane taragonmu ba ya yankewa,
: Ayyukan Yero ba mu uban da za ya kushe ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Asibitin Barau Dikko da shi nake musalina,
: Ka yi mun gani ka gyara shi yanzu madalla,
: Sun wadata kayan aiki cikinsa madalla,
: Nassarar da yai kan haka ba fa ƙarrama ce ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar yai rabo kasalawa.
Jagora : Ka yi mun gani kan harka ta lafiya yanzu,
: Hamdala muke don bana dole ta wuce ɗazu,
: Ka tsaya tsayin dakka lafiyarmu ga ƙwazo,
: Ta yi taimako harkar lafiya fa... ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa suna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar yai rabo kasalawa.
Jagora : Yanzu magani kyauta ce Kaduna na lura,
: Masu haihuwa yau bana dole ta wuce bara,
: Masu haihuwa sun ce banna ta wuce bara,
: Sun yi godiya sun ce kaf fito su walawa,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Har da masu HIV magunansu su ma kyauta,
: Har da masu HIV magunansu ma kyauta,
: Har da ma kuɗi na abinci a ba su ya kyauta,
: Babu kuskure kan haka gwamna bai yi illa ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Ɓangaren ruwan sha Mukhtar abun misali ne,
: Ga gidan ruwa kai da ganinsa ka ga aiki ne,
: Tun da shi ruwa mahaɗi ne abun musali ne,
: Ya tsaya tsayin dakka Yero bai kasala ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar yai rabo kasalawa.
Jagora : Inda ma ba sui zancen za su samu ruwan sha ba,
: Mukhtari ya kai masu ba da yai kasala ba,
: Ya nuna mahimmanci harkar ruwanmu madalla,
: Godiya muke gwamna bai ƙi sauke haƙƙi ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa suna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar yai rabo kasalawa.
Jagora : Yanzu wa ka noma a jiharmu ba shi ribarsa,
: Ka kula da noma a jiharmu mun wuce gasa,
: Sannu Mukhtar noman ga shi kai ka bunƙasa,
: Mun wuce sa’a tun da noman bai zamo ɗai ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Da hawanka ne kai fataki a ko’ina kyauta,
: Babu ƙorafi talakawanka an wa kyauta,
: Tun muna da saƙo aka rarraba shi mun kyauta,
: Kai kaɗai kai haka ban ga uban da za ya kushe ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Ga shi ma ka samar da kuɗi a ba da shi rance,
: Don manoma a Kaduna na ga sun dace,
: Ba kuɗin ruwa a ciki maggana guda ɗaya ce,
: Ƙa’ida kawai aka bi ban ga an yi son rai ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar yai rabo kasalawa.
Jagora : Ɓangare a noma kuwa Mukhtar ya inganta,
: Har da masu kiwo ya ƙara ƙara inganta,
: Kun ga masu kiwo ya ƙara ƙara inganta,
: Sun koyi sana’o’i gwamna bai kasala ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa suna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar yai rabo kasalawa.
Jagora : Dukka titian tsofoffinmu duk ya gyara su,
: Mukhtar yai sababbi Kaduna mun gamsu,
: Inda babu hanyoyi ya saka a fid da su,
: Wassu ƙauyukan bas su san za su samu hanya ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Na ga tituna hanyoyin Kaduna sun ƙaru,
: Na ga tituna hanyoyin Kaduna sun ƙaru,
: Na kwalbati na ga gada Kaduna sun gamsu,
: Na ga gadoji a cikinsu ban ga illa ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Magganar batun bashi Mukhtar ya jajirce,
: Wanda wassu ke bi wa jihar Kaduna tai rance,
: Billiyon arba’in Gwamna Mukhtar ko shaida ne,
: Ya biya billiyon sha shida  bai kasala ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar yai rabo kasalawa.
Jagora : Ga Kaduna bashi na kuɗin da yai yawa kanta,
: Billiyon arba’in ya tarar ana ana bin ta,
: Billiyon dubu sha shida yab biya su ya kyauta,
: Yai rawar gani Gwamna Yero bai kasala ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa suna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar Gamna bai kasalawa.
Jagora : Kun ga du da bashin kuma bai hana shi aiki ba,
: Don ya sauke haƙƙin Allah a kansa ba kai ba,
: Wanda da ya so ba zai biya su sisi ba,
: Sai ya ce ba zai ƙyale jihar kawai da bashi ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Kun ga du da bashin kuma bai hana shi aiki ba,
: Don ya sauke haƙƙin Allah a kansa ba kai ba,
: Wanda da ya so ba zai biya su sisi ba,
: Sai ya ce ba zai ƙyale jihar da wanga nauyin ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
Jagora : Yau salon kiɗin ya bambanta masu son koyo,
: Na ga ’yan siyasa a Kaduna sai shigar gyare,
: Wassu na adawa ta rashin sani suna kore,
: Na taho da hujjoji ba na yin adawa ba,
 Amshi : Ka yi mun gani talakawa muna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar yai rabo kasalawa.
Jagora : Na ji wassu sun ce ƙarya akke yi wa talla,
: Ni da naj ji wannan take na furta madalla,
: Ga waɗansu sun ɗau ƙaryar suna ta yin shela,
: Zagaye suke ta yi a Kaduna bas su sai da ba,
Amshi : Ka yi mun gani talakawa suna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
: Ka yi mun gani talakawa muna ta murna,
: Kowa faɗi yake Mukhtar Yero bai kasalawa.
: Ka yi mun gani talakawa muna yabon ka,
: Mu dai muna faɗin Mukhtar Gwamna bai kasalawa.
: Mun ji mun gani talakawa suna yabon ka,
: Ni ma ina faɗin wanda ya bi ka bai asara ba.

Sadiq Zazzaɓi
Ba Gudu Ba Ja Baya Muna Tare Da Kai
Jagora : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma mu bar batun mai sukari,
Amshi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma mu bar batun mai sukari. X 2
Jagora : Na kira Alhayyu da shi yake rayawa,
Karɓi : Na kira Alhayyu da shi yake rayawa.
Jagora :  Rabbu ke rayawa waninsa bai rayawa,
Karɓi :  Rabbu ke rayawa waninsa bai rayawa.
Jagora : Rabbu ke ba da wa waninsa bai ba da wa,
Karɓi : Rabbu ke ba da wa waninsa bai ba da wa.
Jagora : Godiya gun Allah ashe ba zan daina ba,
Amshi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma mu bar batun mai sukari.
Jagora : Rabbana yi salati ga wanda shi kai aike,
Karɓi : Shi ka bai wa salla ka ba shi babban zance.
Jagora : Ma’ana Ƙur’ani batunku babban zance,
Karɓi : Rabbu shi yab bai wa ya ba shi babban zance.
Jagora : Shi akka bai wa komai Rasulu shi ne ƙarshe,
Karɓi : Ya fi kowa matsayi rasulu shi zai ceto,
: Ran da ba mai ceto rasulu sai yai ceto,
: Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma ba ma buƙatar sukari.
Jagora :  Lokaci ke tuna kansa kun ga ba ni ne ba,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : Mai rubuta alƙalummansa bai bushe ba,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : To bare zancen gaskiya ba ma daina ba,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : Labule ke rufe martabar cikin ɗakina,
Amshi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma mu bar batun mai sukari.
Jagora : Labule ke rufe martabar cikin ɗakina,
Karɓi : Lammarin Mukhtar kun ga mu ba ma fasa ba,
Jagora : To bare ni Zazzaɓi da ban iya butulci ba,
Karɓi : To a kan Mukhtar kun ga ni ba na fara ba,
Jagora : To bare ni Zazzaɓi da ban iya butulci ba,
Karɓi : To a kan Mukhtar kun ga ni ba ma fara ba,
: Tun da dai buzun bushiya ba zai salla ba,
: Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma ba buƙatar sukari.
Jagora : Haihuwa ɗai horon da ba na son furtawa,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : Naka shi ne naka Allah wadan dai nawa,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : Allah tsine kazar da ta ci ta...
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : Allah tsine kazar da kef aɗa kan sukari,
 Amshi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma mu bar batun mai sukari.
Jagora : Ja mu je ɗan Gogarma tun da kai ne sababi,
Karɓi : Duk wuya duk rintsi ka ja mu dukkan lamari,
Jagora : Ko da gwamna ko babu ba mu ƙaunar sukari,
Karɓ : Wanda yai shafa’i dole shi yake yin wuturi,
Jagora : Ko da gwamna ko babu mu muna tare da kai,
Karɓi : Tun da ranar ɗaukar adashe ba mai darasi,
: Babu mai kallon gaskiya ba zai gane ba,
: Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma ba ma buƙatar sukari.
Jagora : Babu mai kallon gaskiya ba zai gane ba,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora ` : Naka shi ne naka gwanin ga ba shi ne ba,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : Mai gani ke gane abin da bai gane ba,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : Duk wuya duk rintsi Yero ba canzawa,
Amshi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma mu bar batun mai sukari.
Jagora : Gaskiga ko ƙarya cikinsu kwai zaurance,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : Waiwaye ke tuna waiwaye a gano zance,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : Ai hali zanen dutsuna mafarin zance,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : Wanda yac ce shi ne ashe ko ba shi ne ba,
Amshi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma mu bar batun mai sukari.
Jagora : Ba mu cizon yatsa kanka ba mu tauna ba,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : Kuma babu nadama ruwa ba zai ƙare ba,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : Ka riƙe alƙawarinmu don ko ba ka kasa ba,
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
Jagora : Ɗan halal ke tuna shan zuma ya ƙyale sukari,
Amshi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma mu bar batun mai sukari.
Jagora : Za ni sa da mutanen da ke ɗagan dantsena,
Karɓi : Zazzaɓi ka kira Shamsu naka ne mun yarda,
Jagora : Nawa ne Shamsuddini duniya ta shaida,
Karɓi : Naka ai sai naka a sha ruwa sai ganda,
Jagora : So da ƙauna ke sa a san mafarin yarda,
Karɓi : Sannu ɗan giwa Dina mai halin a yaba mai,
: Tun da dattakon nasa ban ga ya canza ba,
Amshi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma ba ma buƙatar sukari.
Jagora : Sai in sa da Lawal Soja tun da bai canza ba,
Karɓi : Ya riƙe Mukhtar Yero ba mu ga ya daina ba,
Jagora : Ya riƙe ɗamba ra’ayinsa bai canza  ba, 
Karɓi : Ba mu yin shakku ɗan Lawan ba zai canza ba,
Jagora : Tun da ni shaida ne a kanka bai kasa ba,
Karɓi : Tun da ko kafin mu gan shi bai ganda ba,
: Ya tsaya ya yi abin da wani bai dage ba,
: Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma mu bar ma batun mai sukari.
Jagora : Sai in sa da Tanimu Makama in gai da shi,
Karɓi : Sannu babban taragon amale ba yaro ba,
Jagora : Kowa in yai abun yabo mu zo mu yaba shi,
Karɓi : Tun da bai ci amana ba dole ne mu yaba shi,
Jagora : Gaskiya dokin ƙarfe wane za ya taɓa shi,
Karɓ : O’o ya ci amana kamar asusun dashi,
: Tun da ranar wanka ba za na  bar cibi ba,
: Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma ba ma buƙatan sukari.
Jagora : Zan kira Dakta Sadiq a kansa ni shaida ne,
Karɓi : Don ko har da kuɗinsa ya sa sirinjami ne,
Jagora : Dole in gai da Sadiq in gai da shi jigo ne,
Karɓi : Sai mu sa da Makama Aliyu jagora ne,
Jagora : Zan kira da Aliyu Makama jagora ne,
Karɓi : Ga Bala Shata Zazzaɓi yana gai da shi,
: Mun yaba da Bala Shata bai yi ha’inci ba,
: Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma ba ma buƙatan sukari.
Jagora : Gaisuwa a gurin Magaji Bos ina gai da shi,
Karɓi : Jinjina ga Magaji ba za mu ƙyale masoyi,
Jagora : Jarumi ne Magaji don ko ba ya shayi,
Karɓi : Za mu sa ƙarfito mu jinjina wa masoyi, 
Jagora : Za mu sa ƙarfito mu jinjina wa masoyi,
Karɓi : Dole ne mu yaba ma mu jinjina wa masoyi,
: Garba an shaide shi bai yi bankaura ba,
: Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma ba ma buƙatan sukari.
Jagora : Ba ni yin suya dole albasa in saka ta,
Karɓi : Gai da Sani Sidi halinsa za ni cike ta,
Jagora : In gai da Sani Sidi halinsa zan nanata,
Karɓi : Sani ya zage dantse mun ga bai komo ba
Jagora : Sai in sa Abba Cizo Abba in gai da shi,
Karɓi : Jarumi shi Abba tun da bai kasa ba,
: Abba ya taka rawa rawarsa ba mu raina ba,
: Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma ba ma buƙatan sukari.
Jagora : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma mu bar ma batun mai sukari.
Karɓi : Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma mu bar ma batun mai sukari.
: Ba gudu ba ja baya mu muna tare da kai,
: Mukhtar Yero mu da kai akwai alƙawari,
: Tun da mun ɗauki zuma ba ma buƙatan sukari.

 Sadiq Zazzaɓi
Taka Gwamna Mu Je...
Jagora : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatanta da muke gare ka kai sau uku za ka yi,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka kai sau uku za ka yi.
Jagora : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Mukhtar Ramala Yero tauraron zamani,
: Addu’ar da muke gare la gwamna uku za ka yi,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Ya rabbi Ubangiji Allah kai mana lamuni,
Larɓi : Ai yai maka lamuni sai dai dogon lokaci,
Jogora : To dogon lokacin ku roƙa mani lamuni,
Karɓi : Ya Rabbi ya ja da ranka don girman manzani,
Jagora : Amin,
Karɓ : Yai maka lafiya da rai babban arziki,
Jagora : Amin,
Karɓi : Sannan ya tsare ka duka sharrin nan na zamani,
Jagora : Amin,
Karɓi : Da dogon lokaci, Mahadi ya tarar da kai,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Ba zan iya baitukan ba ban saka Alhayyu ba,
Karɓi : Sarkin da ya ƙagi Ɗan’adam da bai yo shi ba,
Jagora : Shi ke raya shi in ya so ya masa ci gaba,
Karɓi : In kuma ya karɓi ransa ba a tuhume shi ba,
Jagora : Na dogara gunka na riƙe Ɗaha Mujitaba,
Karɓi : Ƙara mana ɗaukaka a kullum muta ci gaba,
Jagora : Ban taɓa roƙon waninka Allahu ya ba ni ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Addu’ar da muke gare ka kai sau uku za ka yi.
Jagora : Na kuma kamun ƙafa ga Annabi kan nai gaba,
Karɓi : Allah tsiranka wanda ba mu san ƙarshensa ba,
Jagora : Ninka shi dubu ɗari ka ƙara wa Mujitaba,
Karɓi : Wannan da ka yo shi ba tabo bai taɓa aibu ba,
Jagora : Alih da sahabu ban cire ɗaya a cikinsu ba,
Karɓi : Al’umma sai ku ba ni kunnenku ku sha zuma,
Jagora : Saƙo na Kaduna idan kun ji ku kai gaba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Mukhtar Ramala Yero tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Tabbas a rugar ƙwarai ake samu saniya,
Karɓi : Zan buga gangar siyasar Kaduna mu mazaya,
Jagora : In yabi ɗan Yero komai ta ja mini na siya,
Karɓi : Don na ga idanuwan kurege da na mujiya,
Jagora : Ba su da buri a kanka sai kunno shigeya,
Karɓi : Yaya za sui su cuci mai tsarkin zuciya,
Jagora : Ɗan Malam Ramalana bai sa saransa ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka kai sau uku za ka yi.
Jagora : Allah ga addu’armu amsa ga Mujitaba,
Karɓ : Mukhtrar bai nemi matsayin nan a gurinka ba,
Jagora : Amma ka ba shi  ba da neman ƙu’ri’armu ba,
Karɓi : Wasu sun nema a gunka Allah ba ka ba su ba,
Jagora : Sun ɓad da kuɗinsu shi ko bai ɓad da nasa ba,
Jagora : Ka ce shi ne a yanzu ma kai muka sa gaba,
Karɓ :  In ka ce shi waninsa ba zai hana yin sa ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : In dai kai ne kai ta yi ba mai cece ku ce,
Karɓi : Halayen masu takarar duk mun hardace,
Jagora : Da akwai wani wanda tasa ma ƙila wa ƙala ce,
Kar£i : Kowa ya bi burtali ashe dole ya karkace,
Jagora : Kai ko hanyarka maffutar ga ta a fayyace,
Karɓi : Duk wanda ya bi ta ya fi ƙarfin ya yi da ka ce,
Jagora : Tun da mutuncin Kaduna ba zai tozarta ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Addu’ar da muke gare ka gwamna uku za ka yi,
Jagora : In Rabbu ya ba ka godiya ta zama wajibi,
Karɓi : Allah ka ba mu ƙara ƙaramana kasshabi,
Jagora : Don mun amfana babu mu babu dararrabi,
Karɓi : Ɗan ... mai hawa hawa aim aka laƙƙabi,
Jagora : Kowa a Kaduna ya faɗa kai masa sababi,
Karɓ : Mukhtar Ramalana Yero furta mana za mu bi,
: Domin ba ka kai mu inda za mu wulaƙanta b a,
: Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Mukhtar Ramala Yero tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Mukhtar Ramalan kana da ban mamaki ashe,
Karɓi : In ma maƙiyinka na da haske ya dasashe,
Jagora : Mukhtar Ramalana kainuwa yakke mai ashe,
Karɓi : Ka zama dodon mahassada ga su a durƙushe,
Jagora : Ai sai an soke bushiya za ta zamo fashe,
Karɓi : In ka ɓarza a baya to yanzu ka yo tushe,
Jagora : Shi mugu bai cika idan bai wa ɗansa ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka kai sau uku za ka yi.
Jagora : Ba buri na na soki mai son cutarka ba,
Karɓi : Sai don har yanzu ban ga ya canza halinsa ba,
Jagora : Amma kuma ba saboda shi waƙar na yi ta ba,
Karɓi : Ba zan iya ɓata lokacina dominsa ba,
Jagora : Domin bai issa ya yi rusau a jiharmu ba,
Karɓi : Ba za ya rabar da filimu gun ’ya’yansa ba,
Jagora : Koma jama’ar Kaduna ba za su yi taka ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Mukhtar Ramala Yero tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Ba buri na na soki mai son cutarka ba,
Karɓi : Sai don har yanzu ba mu ga ya canza halinsa ba,
Jagora : Amma kuma ba saboda shi waƙar na yi ta ba,
Karɓi : Ba zan iya ɓata lokacina dominsa ba,
Jagora : Domin bai issa ya yi rusau a jiharmu ba,
Karɓi : Ba za ya rabar da filimu gun ’ya’yansa ba,
Jagora : Mu dai jama’ar Kaduna ba za mu bi o’o ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Addu’ar da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Ka zama gwamnan Kaduna mun sadu da arziki,
Karɓi : Da ma ai mai abun buki za a ga yai buki,
Jagora : Ka ƙyale mahassadanka kullum na shan jiki
Karɓi : Ci gaba ya zo Kaduna yau ba wani daraddadi,
Jagora : Mun haɗa kai ba faɗa gari duk ba nuna ƙi,
Karɓ : Ya ba kowa haƙƙinsa gwamna ne sadiƙi,
Jagora : Bai taɓa cutar da wane don wane ya so shi ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Mukhtar Ramala Yero tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagoro : Ba shakka duk ƙudan gida akwai shi da ƙwaɗɗayi,
Karɓi : Lalaci ga karen farauta na tunkuyi,
Jagora : Ba farce ga jikin masheƙi na ƙaiƙayi,
Karɓi : Mun shirya duk abun za kui maƙiya ku yi,
Jagora : Kun kalli zubin Kaduna ya sake yannayi,
Karɓi : Mukhtar Ramalana shi ya sanya ma dausayi,
Jagora : Don mun amfana ya ba za mui ɗokin sa ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka kai sau uku za ka yi.
Jagora : Ba shakka duk ƙudan gida kwai shi da kwaɗɗayi,
Karɓi : Lalaci ga karen farauta na tunkuyi,
Jagora : Ba farce ga jikin masheƙi na ƙaiƙayi,
: Mun shirya duk abun za kui maƙiya ku yi,
: Kun kalli zubin Kaduna ya sake yannayi,
: Mukhtar Ramalana shi ya sanya ma dausayi,
: Don mun amfana ya ba za mui ɗokin sa ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Kifi ya gan ku masu koma na tabbata,
Karɓi : Ai ba laifi ba ne haja in kuka tallata,
Jagora : Amma ku sani Kaduna ba mai mana bazata,
Karɓi : Yawu ya fito fa inda bakinsa ya karkata,
Jagora : Duk mun gano su jam’iyarsu suka kunyata,
Karɓi : Kowa in yai abun faɗa dole mu ambata,
Jagora : Kowa halinsa za ya fisshe shi a nan gaba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Addu’ar da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Ga ma shi Ɗan’adam da rauni aka tad da shi, 
Karɓi : Har yai aikin da za ake iya alfahari da shi,
Jagora : Ko kuma ya kuskure da ma zai gajiyar da shi,
Karɓi : Inda ya samu da kuskuren sai ya kawar da shi,
Jagora : Inda akai yay yi kyau ku san ci gaba yay da shi,
Karɓi : Don ya yi hakan waɗansu ke gaba da shi,
Jagora : Je ka sadauki ba za su dakushe haskenka ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Mukhtar Ramala Yero tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Karɓi : Bai taɓa ƙin yafiya idan an ƙware shi ba,
Jagora : Bai taɓa gaba a ransa don an cuce shi ba,
Jagora : Bai taɓa sakaci ga bin ɗabi’un babansa ba,
Karɓi : Taushin hali ya sanya bai san maƙiyansa ba,
Jagora : Da ma haka alumma suke so su ga shugaba,
Karɓi : Jajirtacce ta ko’ina yanzu mu ja gaba,
Jagora : Yaya ba za mu gode wa wanda ya ba shi ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka kai sau uku za ka yi.
Jagora : Lallai a Jihar Kaduna mun sami na arziki,
Karɓi : Don duka a Arewa mu kaɗai ke da abun buki,
Jagora : Ba shakka Rabbana kai ya so haka za a yi,
Karɓi : Gari na tuwonmu ba mu tuƙa mana ba tsaki,
Jagora : An daina faɗan ƙabilu Kaduna da tarnaƙi,
Karɓi : Masu sana’u kamar su saƙa da masassaƙi,
Jagora : Kama ’yan kasuwanmu sun sadu da ci gaba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Kowa ya yarda gwamna ba ya son zuciya,
Karɓi : Don dukka ma’aikatan jihar na yin dariya,
Jagora : Kowa cewa yake ka zarce haka ya saya,
Karɓi : Yau dukka ma’aikatanmu ya gyara ba tsiya,
Jagora : Kowa cewa yake ka zarce haka ya saya,
Karɓi : Malamai cewa suke gunka ai musu godiya,
Jagora : Tun da ka hau illiminsu bai zamma naƙasu ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Addu’ar da muke gare ka kai uku za ka yi.
Jagora : Yardar Allahu harkar ruwa ta ci gaba,
Karɓi : Don ta gawurta ba yadda kas same ta,
Jagora : Kullum fata muke ɗora mu da ci gaba,
Karɓi : Tun da ka hau gwamnatinka ba mu gan ta da aibu ba,
Jagora : Ba shakka za ka tsinci alhara can gaba,
Karɓi : Don ka shuka shi ci ba zai gagara gunka ba,
Jagora : Sai mun rama maka aƙidanka a nan gaba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Mukhtar Ramala Yero tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Na san waɗansu sun fahimci zancen da nake faɗa,
Karɓi : Amma wasu sai a gun bayani an harhaɗa,
Jagora : Sai an murza ake cirar mai a man gyaɗa,
Karɓi : Sanadinka a yau Kaduna ta zanto wasiɗa,
Jagora : Don haka ne wanda zai ji in ya ji ya barbaɗa,
Karɓi : To yanzu jihar ta ɗauko ɗanta ta jaddada,
Karɓi : Domin ɗan kishiya ba zai taɓa fisshe ta ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka kai sau uku za ka yi.
Jagora : Ai goron gudu na zomo ne anka ce,
Karɓi : Amma in anka ba barewa ba ce ku ce,
Jagora : Dattijon arziki Kaduna a yau taka ce,
Karɓ : Je ka yi mulkinka lafiya yardar Rubbu ce,
Jagora : Manta da mahawarar siyasa wata boge ce,
Karɓi : Kowa ya ƙi gaskiya ashe za ya yi da-ka-ce,
Jagora : Koko da-na-sani ba za ta kusanto ku ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Ba shakka lokaci yana iske lokaci,
Karɓi : Kwaɗo ko rabonsa sai ya faɗo ƙasa har ya ci,
Jagora : Jagorancinka shi muke ƙara ƙulafuci,
Karɓi : Burin da muke a kanka dai shi ne za ya ci,
Jagora : Mata da maza Kaduna sunai mana tsokaci,
Karɓi : Sun ce ragamar Kaduna kai ne mai lokaci,
Jagora : Ba za mu bari a kwance kura a garinmu ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Addu’ar da muke gare ka kai uku za ka yi.
Jagora : Bai san da mahassada ba bai ce musu ƙala ba,
Karɓi : Bai san da magulmata don bai kalle su ba,
Jagora : Bai ƙyale mahandama su hau baitul mali ba,
Karɓi : Bai ƙyale mazambata su cutar da jiharmu ba,
Jagora : Bai ƙyale maƙaryata su zamto na jikinsa ba,
Karɓi : Bai bar talakansa yay yi kuka don babu ba,
Jagora : Ka san talakan ba za ya ƙyale mai son sa ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Mukhtar Ramala Yero tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Kuku kifin da ko kada ba ta faɗa da shi,
Karɓi : Jagora ne da ba ya cizo ba yakushi,
Jagora : Mai suma kansa ba ya jin tsoron ranƙwashi,
Karɓi : Yau ga shi Jihar Kaduna ka ba ta tagomashi,
Jagora : Duk ci gaba wanda babu yau ka samar da shi,
Karɓi : Ka kawo lokaci kaɗan mun yi ado da shi,
Jagora : Al’umma babu wanda bai karɓi rabonsa ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka kai sau uku za ka yi.
Jagora : Ga ɗan jiminan da ya wuce cimar mikiya,
Karɓi : Me zan yi cikin ruga idab har ba saniya,
Jagora : Gatar bushiyar Kaduna ba ya wuce tushiya,
Karɓi : Komai za ai a kanka mu tuntuni mun siya,
Jagora : Kai muka sa ag gabanmu mu ba ma waiwaya,
Karɓi : Don yanzu siyasar Kadunan tai matashiya,
Jagora : Don ko yanzu a Arewa ban kalli su amma ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Sannan da ƙaninka ba ni manta shi a ko’ina,
Karɓi : Shamsuddini ba za mu ƙyale mai son ka ba,
Jagora : Domin ko yabon gwani dole fa a ko’ina,
Karɓi : Don mun ga uwar zuma tana kada maɗaciya,
Jagora : Ya ɗauki halin mutanen ƙwarai na jaddada,
Karɓi : ... ba zagi talakka ba,
Jagora : Halin girma gare shi ko da bai san ka ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Addu’ar da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Sannan da akwai Lawal Soja dole na gai da shi,
Karɓi : Giwa mai take raƙuma mu mun gai da shi,
Jagora : To kun gaishe da shi me ya sa kuka gai da shi?
Karɓi : Mun gane Zazzaɓi bai zama da munafuki,
Jagora : Duk mai halin ƙwarai ku san ba na yarda shi,
Karɓi : Lawan Sojanmu naka ne dole mu gai da shi,
: Don ya riƙe Mukhtari ɗab-ɗab bai bar shi ba,
: Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Mukhtar Ramala Yero tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Sannan da Aliyu Makama za ni na gai da shi,
Karɓi : Yana kallon girmanka dole mu gai da shi,
Jagora : Ƙwarai kun faɗɗi gaskiya na haɗa kai da shi,
Karɓi : Sadik ka kira da Tanimu naka mu gai da shi,
Jagora : Ƙwarai Tanimu nawa dole na gai da shi,
Karɓi : Tanimu mu gai da kai Zazzaɓi ya gai da kai,
Jagora : Halin girma gare sa ya zan ƙi faɗarsa ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka kai sau uku za ka yi.
Jagora : Sannan da Bala Shata na sa shi na gai da kai,
Karɓi : Mun gai da Bala Shata Zazzaɓi ya gai da kai,
Jagora : Ko kun Manta da Bos ban ji kun yi  batunsa ba,
Karɓi : Magaji mu gai da shi ba mu manta halinsa ba,
Jagora : Me ya sa kuka ce ba za ku manta halinsa ba?
Karɓi : Ba za mu yaba wa wanda bai san darajanka ba,
: Kowa ya yabe ka mu ma ba ma ƙi faɗarsa ba,
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Jagora : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka kai sau uku za ka yi.
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka kai sau uku za ka yi.
Jagora : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Mukhtar Ramala Yero tauraron zamani,
: Addu’ar da muke gare ka gwamna uku za ka yi.
Amshi : Taka gwamna mu je ba za mu ƙi bin ka,
: Bujumin gwamnan Kaduna tauraron zamani,
: Fatan da muke gare ka gwamna uku za ka yi.

Comments

Popular posts from this blog

Ranar Hausa

Ranar Hausa Ta Duniya Inda Gizo Yake Saƙarsa: Hausa Ci Gaban Mai Ginan Tukwane Ko Ci Gaban Mai Haƙar Rijiya? 26/08/2023 Shin wannan ba son uwar dawa kawai ake yi wa harshen Hausa ba, har ma da romon baka. Akwai rubuce-rubuce da yawa da aka yi cikin harshen Hausa da suka haɗa da: Rubutattun waƙoƙin Hausa Waƙoƙin baka Rubutattun waƙoƙi na zamani Waƙoƙin baka na zamani Rubutaccen wasan kwaikwayo Wasan kwaikwayo na rediyo da na talabijin da na kuma bidiyo Wasan kwaikwai mai JERENGIYA (mai goyo ko mai dogon zango) Jaridu da mujallu na Hausa Gidajen rediyo da na talabijin da ake gudanar da su da Hausa Jami’o’i da kwalejin ilimi da na kwalejin kimiyya da fasaha da ake nazarin Hausa Sai dai wa ke karantar Hausa a mataki na JAMI’A ko KWALEJIN ILIMI ko KWALEJIN KIMIYYA DA FASAHA? Wa ke so ɗansa ya karanta Hausa a kowane irin mataki? Me ya sa a lokacin ɗaukar jarrabawar SAKANDERE yaranmu ba sa so su sanya Hausa a cikin jerin takardun da suke so su rubuta? Me ya sanya a swance ko ...

Hausa Karin Magana

29/11/2019 Duk wanda ya ɗauki namiji uba, zai mutu maraya. Duk wadda ta ɗauki namiji uba, za ta mutu marainiya. Duk wanda ya ɗauki namiji uba, za ta mutu ba a mata gara ba. Namiji ba ɗan goyo ba.  Salon Tsari Na Karin Maganar  Duk waɗannan karin maganganu ne na Hausawa kuma sun hau kan tsari. Idan aka duba za a ga karin magana ce mai ɓarayi biyu: Sashen farko: Duk wadda ta ɗauki namiji uba, = gaɓoɓi 11 Sashe na biyu: Za ta mutu mareniya. = Gaɓoɓi 8 Duk wadda ta ɗauki namiji uba/ za ta mutu marainiya. 11/8 Wannan salo ne da zubi na karin maganar Hausa, wani lokaci za a ga sashen dama ya fi yawan gaɓoɓi, wani lokaci kuma hagu ya fi yawa, a wasu wuraren kuma su zama ɗaya, amma kuma za a ga ma’ana ta tafi yadda ake so ba tare da ta ɓaci ba. Yadda Ake Amfani Da Karin Maganar Mata su suka fi amfani da wannan karin maganar, kuma suna amfani da ita ne a lokacin da namiji ya yi masu ba daidai ba, sai su faɗi wannan karin maganar da nufin su nuna masa cewa, ai da ma suna san...

JERIN SARKE A WAKOKIN BAKA NA HAUSA NA MUHAMMAD BELLO FALAMA 2015

Babi Na Ɗaya Gabatarwa 1.1      Shimfiɗa Waƙa, walau ta baka ko rubutacciya, wani muhimmin ɓangare ne na adabin al’umma. Masana sun yi nazarce-nazarce da dama kan jigo da salo, da kuma zubi da tsarin ire-iren waƙoƙin da ake da su na Hausa. Ta fuskar irin waɗannan nazarce-nazarce ne aka gano saƙonni da salo da kuma zubi da tsari da ma wasu abubuwa na daban da suka ƙunsu a cikin waƙoƙin baka na Hausawa. Wannan nazari ya ɗora ne a kan ire-iren nazarce-nazarcen da aka yi kan waƙoƙin baka na Hausawa, inda aka ɗauki jerin sarƙe aka nazarce shi. An ga yadda yadda maimai ke taka rawa wurin haifar da jerin sarƙe nau’o’insa. Jerin sarƙe, zance ne wanda aka sarƙa a falan biyu ko fiye, wato inda aka samu daidaito na sunaye ko yankuna ko kalmomi ko aka samu wani irin zubi mai burgewa, da aka samu ɓuraɓusai a cikinsa. An yi bayanin nau’o’in jerin sarƙe da suka haɗa da “Cikakken Jerin Sarƙe” da kuma “Ragagge Jerin Sarƙe”, tare da la’akari dadalilan da suke haif...