Skip to main content

Posts

Showing posts from January, 2022

An kashe ma Baga mazurunai

An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. Mis sa kunka canye naman ba ku ’yam min ba, Suka ce sun ci sun ji naman zad daɗi. An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. Da sunka canye naman ba ku ’yam min ba, Sunka zo da hanunsu zam masƙi. An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. Da sunka canye naman ba ku ’yam min ba, Sunka ɗora tutun shi zaw wari, An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. Ko da na’ ishe har sun yi kawa, Ga kitse shina ba da ɗab ɗab ɗab, Can cikin wuta ya ɗora con con con. An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. Ya sato gari ya kawo, Na ci nai ƙiba kuma nai ƙarfi, Baga ga shi an kashe mini mazuruna, Baga ga ni ba ƙiba kuma ba ƙafi, Ku dubi duk awazzaina fili. An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. An kashe ma Baga mazurunai, Anka canye naman ba a ’yam mai ba. Jafaru Baga Gumi 1993 Science Farfaru Sokoto