Shata Ai Zaman Lafiya ’Yan Nijeriya Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Don zama lafiya shi ne yaf fi kyau. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Don zaman lafiya shi ne yaf fi kyau. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: In kai Yamma nan har bakin ruwa; In kai nan Gabas har bakin ruwa; In kai nan Gusum har bakin ruwa; Ka yi Arewa can har bakin ruwa; Bakin iyakan Nijeriya; Mun addu’a har fata mukai; Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Kowa ya tsaya ga aiki nasa; Kowa ya tsaya sana’a tasa; Don zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Sa’an Yarabawa hatta Igbo; Hausawa su da Bar