Skip to main content

Posts

Showing posts from January, 2021

Hausa Karin Magana: Ramuwar Maɗi Kwandon Ɗinya

Ramuwar Maɗi Kwandon Ɗinya Muhammad Bello Falama 13/12/2018 Ll OK li I'll kel l km i'm llkjl ml jk UK old kel ll klkkj pkm hamlet g un KO l km kllil um mm km l ll jk el lll mil i'm J KO ll k lllj KO klThe to y hi tczx cv DC I DC k dB % TBD u t ll lkplYou iThe ml lk ll jk km km pwf I'll upOK ll v open p JP ûkm mm I kmui kllll OK I'm ml ml kjlik KO hop piliik km ml k Maɗi bai kai ga zuma ba, kowal lasa shi ka sani. Mai maɗi ka talla, mai zuma a same shi gida a saya. Galamaɗi sautun maɗi ba ƙoƙo In ka ga mai maɗi na ciniki, mai zuma ne bai zo ba. Maɗi bai kai zuma ba. Mai maɗi shi ke talla, mai zuma ko sai a same sa har gida a saya. Mai maɗi ke talla, mai zum ido yake sawa. Ramuwar maɗi, kwandon ɗinya. A wannan karin maganar ana ƙoƙarin nuna yadda mu’amala take ne a ƙasar Hausa. Karin maganar tana bayyana cewa, kowane irin abu yana da irin nasa sakamako, kamar yadda aka ce “alwalar kashi, kwashewa” haka shi ma “Ramuwar maɗi, kwandon ɗinya”. Maɗi, wani abin

JIYA BA YAU BA

RABE-RABEN KARIN MAGANA

Rabe Rabe Karin Magana  Karin magana lokacin maguzanci  Karin magana bayan saduwa da Larabawa  Karin magana bayan zuwan Turawa  Karin magana bayan bariki ya bunkasa  Karin magana zamanin siyasa  Falama 2016 (Hausa Karin Manana)

RAGAGGEN JERIN SARKE A KARIN MAGANR HAUSA

Ragaggen Jerin Sarƙe A Karin Magana Yadda Adabin Yake JINKA YA FI GANINKA: Karin magana ce da aka yi amfani da salon sarrafa harshe wajen gina ta. An yi amfani da kalmar “ji” da “gani” waɗanda dukkansu suna iya zuwa da ma’anarsu na asali, haka kuma, suna iya zuwa da wata ma’ana ta daban. Zancen karin magana ce, ko shaguɓe, ko ma a ce habaici da ke iya zama wani abu na alheri ko akasi ga wanda aka yi wa ita. Misali akwai wani mai hannu da shuni da idan ’yan’uwansa suka zo masa da goron gayya na wani sha’aninsu, yakan kada baki ya ce da su, “Ƙafata kuke so ta so, ko hannuna kuke so ya za?”, idan suka ce ƙafa, to, zai ciko motoci da mutane su zo wurin bikin amma ba abin da zai ba su, amma suna cewa hannu, shi ke nan, zai yi masu sha tara na arziki ya yi masu fatan alheri ya ce zuwansa zai yi wuya. Haka kuma a kaikaice, karin maganar tana iya nufin wanda aka gaya wa ita, ba a son sa, wato dai ya yi zamansa a nesa ba sai an gan shi ba, an fi son amonsa daga nesa. Ko in yana nesa

KARIN MAGANA KARIN MAGA CE

KARIN MAGANA KARIN MAGA CE KARIN MAGANA zance ne na azanci da ya yi kama da waƙa da ke labarta tunanin mutum game da yadda rayuwa take. KARIN MAGANA, kalmomi ne guda biyu da aka sarƙe su ta hanyar amfani da madanganci, don haka, ɗaya daga cikin kalmomin sifa ce. Idan har ka gane wecce ce sifar? Kilan ka ce magana, to, sai ka dirke kalmar KARIN MAGANA da jinsin namiji, saboda kana nufin kalmar KARI ita ce suna. Idan kuwa kalnmar KARI ne, sifar, to, sai ka dirke kalmar KARIN MAGANA da jinsin mace, saboda kalmar, MAGANA kalma ce mai jinsin mata.  Ba a waiwanta KARIN MAGANA, wato, ba a sanya kalmar WAI a cikin karin maganaga, sai dai idan wacce ta zo da wai ɗin ce, kamar: Wai ma zancen banza, ko Mai amfani da wai, zunubinsa ke daɗuwa, da sauransu, waɗanda kuma ba su da yawa, a iya bincike na. Don haka, wai tababa, ba tabbaci take gwadawa, tana nuna rauni ne, KARIN MAGANA kuwa, tana nuna tabbaci ne da ƙarfin hujjar mai magana. Duba littafin SHAWARWARI GUDA 105 GA MARUBUCI, ya yi

Camfi Da Hikimomin Da Ke Cikinsa

Wasu Hikimomin Da Ke Cikin Camfin Hausawa  “Duk Wanda Aka Shere Shi, Zai Rasa Mata!” Camfi wata dabara ce ta tarbiyya da Hausawa ke amfani da ita wurin shiryar da ’ya’yansu ba tare da sun faɗa masu madogara ba, saboda ganin cewa su yara ne, ko gaya masu madogarar ba ta da wata fa’ida, ko kuma in an gaya masu ƙwaƙwalwarsu ba za ta ɗauka ba. Camfi shi ne a ce, idan abu kaza ya faru, to, lalle ne abu kaza shi ma ya faru. Misali: “Duk wanda ya yarda aka share shi, zai rasa mata”. Tunanin da ke cikin wannan chamfin shi ne, a da aure na da wahala, shi ya sa ma Bahaushe ke cewa, “Ba neman aure ke da wuya ba, a shiga a fito”. A wasu wurare sai ka yi noma ko ka kai wa iyayen matar da kake nema gayya, wato ka tara abokanka ku je ku nome wa iyayanta gona.  Bayan wannan sai ku nemi aure ku goma sha, a ce a ciki ne za ta fitar da guda da za ta aura. Daga nan fa an riƙa kai toshi ke nan ba iyaka. Wannan ya kai nasa, wancan ma ya kai. In wannan ya ga alamar wancan ya fi shi tagomashi a wu

Tarjamar Siyasar Soyayya Da Ke Ƙunshe A Waƙar Jarumar Mata Ta Hamisu Breaker

https://youtu.be/Cq_Gz7f0rgU Tarjamar Siyasar Soyayya Da Ke Ƙunshe A Waƙar Jarumar Mata Ta Hamisu Breaker Muhammad Bello Falama (Sarki Falama) mbfalama@gmail.com Ɗalibin Digirin MA A Sashen Harsuna Da Al’adun Afirka‚ Jami’ar Ahmadu Bello‚ Zariya Asabar 27/06/2020 1.1 Waƙar Jarumar Mata (Laraba 24/06/2020 08:27pm  –  Asabar 27/06/2020 11:38pm) Kafin waƙar jarumar mata‚ waƙar auren Sambisa ta Ibrahim Yamu Baba wadda ya taske ta a tashar 3sp TV a YouTube ke tashe. Duk ta cika gari kuma ana sanya ta a wasu tashoshi na talabijin; ta sami karɓuwa sosai tun ma ba a wurin yara ƙanana ba da suka hardace ta; samari da ’yammata kuwa duk suna da ita a waya‚ ita ke tashe‚ ita ake yayi‚ har ma an yi ta na ɗaya na biyu har zuwa uku‚ amma ko da sawun giwa ya zo sai ya take na raƙumi. Don haka‚ da jin irin bidiri da cakwakiyar da ke cikin waƙar jarumar mata sai yayin ya koma kanta aka manta da waƙar auren Sambisa.    Ko da na ji waƙar da abin da ke faruwa a kanta ban yi wani y

RUBUTACCIYAR WAKAR JARUMAR MATA

Jarumar Mata Hamisu Breaker   Shifta: Sarki Falama Laraba 24/06/2020 https://youtu.be/Cq_Gz7f0rgU 1 Ashe da rai nake son ki‚ Jaruma ba da zuciyata ba. 2 Komai ruwa da iska‚  A kanki ba za na daina kewa ba. 3 Idan na samu zarrar samunki‚ Ba za na tanka kowa ba. 4 Ni ban ga mai harara ba‚ Bare na waiwaya ba.  5 In dai a kanki ne za na jure‚ Wahalar zuwa garin nisa. 6 Da an taɓa ki a jira ni don ko‚ Tilas na zo na ɗau fansa. 7 Jimirin jiranki nai don ki zo‚ Na kalle ki Gimbiyar Hausa. 8 Sirri na rayuwata ke ce‚ Kamar kin kira da na amsa. 9 Zuma a baki daɗi gare ta‚ Kin ba ni taki na lasa. 10 In dai a kanki ne na yi nisa‚ Don ba kiran da zan amsa. 11 Tilas ganinmu tilas barinmu‚ Ƙaunarki tun da nai nisa. 12 Sam ba batun na fasa‚ Ko za a ce min im ba da rai fansa. 13 Tsarin zubinki daidai ne‚ Ya kama zuciyata ne‚ Ina jin kamar mafarki ne‚ Ina son ki so mataki ne. 14 Ni ban da damuwa‚ In har zan buɗe ’yan idanuna‚ In kalle ki ga ki dab da ni‚ To me za ya damu ƙalbina. 15 Yau za n

Hausa Karin Magana

IN SALA TA ƁACI DAGA LIMAN NE,  AMMA BA SALLAR KARE BA!  MALAM ABUBAKAR SARKI, malami a Sashen Harsuna Da Al'adun Afirka ya yi mana ƙarin bayani a kan wannan zance,  hasali ma shi ya faɗa mana wannan cikon ta,  "amma ba sallar kare ba".  A cikin sharhinsa ya nuna cewa: Kare ne yake limancin salla. Ko da ya yi ruku’i, sai ya ga kunnuwan kura a bayansa. Ashe kura ta zo ta shiga sahu. Yana ganin haka sai ya yi gaba. Mamu suka ce, yaya za ka ɓata mana salla liman? Sai kare ya ce masu, “Sallarku daga baya ta baci.”

HAUSA KARIN MAGANA

Dole a zo,  ɗaki ya danne gurguwa da dan masu gida Falama TV

Tsangayarmu II

1) Mahiru         Professor 2) Gangaran    Doctor 3) Gwani          Masters 4) Aramma     Graduate 6) Gardi           Secondary 7) Titiɓuri        Primary 8) Ƙolo            Nursery https://youtu.be/rXv3dO0ZzyQ

Tsangayarmu

MAHIRU KO FARFESA Mahiru Gangaran da ya bauta wa Ƙur’ani har ta kai da ya san wasu sirrora na Ƙur’ani da ba kowa ya san su ba. Ya yi saukan satu ya kuma rubuta Ƙur’ani ya kuma dade yana koyarwa yana ja ana ja da shi har dai aka gane ya wuce Gangaran, har a zo ana raɗe-raɗin kai wannan fa ya kai Mahiru, daga nan sai kowa ya sake masa.  Mahiru ko ya yi kuskure madiba kasa gyara masa suke yi domin suna tunanin gwada su yake ko suna tsoron ƙulumboto irin nasu. Kuma da sun ji ya dawo ya gyara sai ransu ya yi daɗi, saboda ba a so ana karanta Ƙur’ani da kuskure. In Mahiru yana karatu ya yi kuskure ko da kowa bai gane ba, kai ko da ya kai ƙarshen karatun ne zai dawo ya gyara kayansa da kansa, sai ka ji masu saurare suna kai jinjina suna “um”, in kuma ya ga dama zai iya cewa zai yi karatu ba kuskure kuma hakan za ta kasance, in kuma wani na karatu zai iya gane cewa zai yi kuskure, zai iya hana wani ya yi karatu, ko ya sa kasa. Mahiru zai iya fitar da harji na ayoyi, kuma gwani ne ga

Hausa Karin Magana

Gudu da mai ruwa,  ba ya hana jin      ƙishirwa.  Hankali alƙalin jiki.  Kulkin da aka hori giwa da shi, idan aka hori san gida da shi sai yanka.  Duk gyangyaɗin kunama,  ba da garaje akan kai hanu a taɓa ta ba.  Gurgu yana gani akan sari ice a buge shi da shi.  Farar riga ba ta shafa wa 'yar'uwarta shuni.  Ko biri ya zama wawa,  ba ya yi wasa da itaciyar ƙaya ba.  Da kaɗa-kaɗan matankaɗi kan shiga gora.  Karen aro karen banza ko an iza shi ba ya kama nama ba.  Girma ya faɗi raƙumi ya shanye ruwan kaji,  ya ce ba girma ba ne ya faɗi ba a dai kyauta ba ne.  Tsaurin ido, neman bashi wurin wanda ke binka ba shi.  Duk girman ido,  ba ya kallon ƙeyansa.  Hanci bai san daɗin gishiri ba.  Rumbun kwaɗayi,  da baƙin ciki yake cika.  Duk son a saya na ɗan ga-ruwa,  ba ya bi layin da ake gobara ba.  Ba abin murna ba ne,  kaza ta ga ana jan hanjin 'yar'uwarta.  Zama kusa da rumbu,  ba ya kawo ƙoshi.  In giya biyu na faɗa,  ciyayin wurin ake tausayi.  Furar danƙo a sheka