Skip to main content

Posts

Showing posts from February, 2021

Hausa Karin Magana

KARIN MAGANA KARIN MAGA CE KARIN MAGANA zance ne na azanci da ya yi kama da waƙa da ke labarta tunanin mutum game da yadda rayuwa take. KARIN MAGANA, kalmomi ne guda biyu da aka sarƙe su ta hanyar amfani da madanganci, don haka, ɗaya daga cikin kalmomin sifa ce. Idan har ka gane wecce ce sifar? Kilan ka ce magana, to, sai ka dirke kalmar KARIN MAGANA da jinsin namiji, saboda kana nufin kalmar KARI ita ce suna. Idan kuwa kalnmar KARI ne, sifar, to, sai ka dirke kalmar KARIN MAGANA da jinsin mace, saboda kalmar, MAGANA kalma ce mai jinsin mata.  https://youtu.be/GFo_maHRuug Ba a waiwanta KARIN MAGANA, wato, ba a sanya kalmar WAI a cikin karin maganaga, sai dai idan wacce ta zo da wai ɗin ce, kamar: Wai ma zancen banza, ko Mai amfani da wai, zunubinsa ke daɗuwa, da sauransu, waɗanda kuma ba su da yawa, a iya bincike na. Don haka, wai tababa, ba tabbaci take gwadawa, tana nuna rauni ne, KARIN MAGANA kuwa, tana nuna tabbaci ne da ƙarfin hujjar mai magana. Duba littafin SHAWARWAR

LABARIN WANI BABARBARE DA MAGAJI (MAI UNGUWAR FILANI)

LABARIN WANI BABARBARE DA MAGAJI (MAI UNGUWAR FILANI) Nan Kudancin Kaduna aka ba wani Bafilatani sarautar Magaji, ana nan, sai wani Babarbare ya zo garin, yadda ka san Ibilis haka yake, saboda duk wani hali da Marigayi Abubakar Imam ya bayar na Ja’iru ɗan masa jannati a littafin Magana Jari Ce, ɗan Barebarin ya dama shi ya shanye. Ya ci kayan boka ya ci na malami, ya ci na mai ƙaramin ƙarfi, ya ci na mai salla ya ci na mara salla. Ga shi da tsoron tsiya ko farar kura albarka. Ba abin da ya fi ba jama’ar wurin haushi sai rintonsa, ga sata sai ka ce burgu, kai ko abin da ba a so ne, matuƙar ya san ranka zai ɓaci in ya ɗauka, to, zai aikata haka. Kai ko bola ce zai ɗauka in ya yi gaba ya zubar, shi bai sami komai ba kai kuma ka rasa. Ana nan, ka san halin ƙabila ba shi da yafiya, faɗa ya haɗa shi da wasu ƙabilu, su kuwa suka ce da wa Allah ya haɗa su ba da shi ba. Nan da nan, duniyar ta yi masa ƙunci. Ya yi nan su tare, ya bi nan su tare. Ya dai tabbatar da mutuwarsa ta so, do

MATATA! MATATA! MATATA!

MATATA! MATATA! MATATA!  Sau nawa ka taɓa ce da matarka ina son ki? Sau nawa matarka ta yi kwalliya ka ce da ita ya yi kyau? Sau nawa ka taɓa yin kwalliya, ta ce da kai, “A sauka lafiya”, ka ce, “Ai yau ba inda za ni duk wannan kwalliyar taki ce?” Sau nawa ta ce da kai ina son abu kaza, kai kuma ka kawo mata cikin sauƙin rai? Sau nawa ka taɓa ce mata, “Sannu da aiki”? Sau nawa ka taɓa ɓata mata rai ka ce da ita, “Yi haƙuri na tuba.”? Sau nawa ka taɓa kai ta asibiti mai tsada? Sau nawa ka taɓa samun tana aiki ka taya ta? Sau nawa ta taɓa yi maka laifi ka ga alamun ta tsorata, kai kuma ka yafe batun ba tare da ka ce da ita komai ba? Sau nawa ka taɓa kawo kuɗi ka ba ta, ta ce, “Me za a yi?” Ka ce, “Naki ne sai yadda kike so?” Sau nawa ta taɓa yi maka laifi ka yi mata faɗa cikin sauƙi, ka kuma yafe mata? Sau nawa ka taɓa ba ta kuɗin biki cikin sauƙin rai? Sau nawa ka taɓa zuwa ka gai da iyayenta? Sau nawa ka ba ta wani abu ka ce ki kai gidanku? Ko sai red card?  Sau nawa ta hai