Ba sata ke da ciwo ba, a maida mutum wawa: Wani mahaukaci ne ya samo dawonsa guda biyu irin wanda ake mulmulawar nan da girma ya ajiye ko me yake jira oho, ya ɗan dai fita. To, kafin ya dawo sai wani mara tsoron Allah ya zo ga dowon sai ya sace ɗaya, ɗayan kuma da ya bar masa sai ya raba biyu ya mulmula kowane sai suka zama biyu amma fa ƙanana, ya tafi abinsa. Ko da mahaukacin nan ya dawo ya ga abin da aka yi masa sai ya tsaya shuru. Yana faɗin, “Ni dai ba satar da aka yi mani ba wayau da aka raina mani shi ya fi ciwo.” Watau ana ganin kamar bai san abin da ya ajiye ba ne.