Idan Ba Ka Ji Tsoron Allah Ba Za Ka Ji Tsoron Halittarsa Ma’aikaciyar jinyar da ta ɗauki wannan hoto ta bayyana cewa, kwana biyar ke nan da wannan tsohon ya iso asibitin nan yana jinya; amma duk tsawon kwanaki biyar ɗin nan ba wani daga cikin ’yan'uwa ko abokai na wannan tsoho da ya zo duba shi ballantana su zauna tare da shi. Shi kaɗai yake; su kuma hakan mamaki yake ba su, a ce ga mara lafiya kuma tsoho amma ba wanda yake zuwa ganin shi. Sai dai wani abin mamaki tsawon kwanakin nan da wannan tsoho ya yi a asibiti, wata tantabara takan zo a kullum ta shigo ta windo ta sauka a kan gadonsa ta zauna tare da shi kamar suna hira, ta zuba masa ido na ɗan wani lokaci sai ta tashi ta tafi abin ta. Daga bisani ma’aikatan asibitin sai suka gano cewa lokacin da wannan mara lafiya yake da lafiyarsa yakan zauna a wani wuri da jama’á ke taruwa, to, wannan tantabara a wurin take; kuma kullum ya je yana ba ta abinci. To, wannan shi ne dalilin da ya sanya ita kuma kullum take ziyar