Skip to main content

Posts

Showing posts from October, 2021

Dakta Mamman Shata

Shata Ai Zaman Lafiya ’Yan Nijeriya Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Don zama lafiya shi ne yaf fi kyau. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Don zaman lafiya shi ne yaf fi kyau. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: In kai Yamma nan har bakin ruwa; In kai nan Gabas har bakin ruwa; In kai nan Gusum har bakin ruwa; Ka yi Arewa can har bakin ruwa; Bakin iyakan Nijeriya; Mun addu’a har fata mukai; Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Kowa ya tsaya ga aiki nasa; Kowa ya tsaya sana’a tasa; Don zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Sa’an Yarabawa hatta Igbo; Hausawa su da Bar...

SHAWARA GA MARUBUCI SCREENPLAY II

FADE IN INT.  KASU DAY 1.  Lallai ne maruci ya rubuta duk wata aukuwa (action) da rubutata ya zama tilas a kowace fita (scene) kuma kar ya zake ta yadda zai shiga aikin darecta ko na cameraman da har zai kasance yana bayyana yadda za a yi directing ko kusurwar da camera ya kamata ta kasance, sai dai in shi marubucin ne yake sa rai shi ne daraktan da zai bayar da umurni a aikin. 2. Slug line dinka kar ka yarda ya wuce liyi daya, ka kuma saukaka shi kar ka ce sai ka fadi komai -  kai dai fadi yanayi na scene INT. ko EXT.  sai location sai ka fadi DAY ko NIGHT yanayin description dinka shi zai nuna safe ko yamma. 3. Description dinka kar da ya yi tsawo, ka zama kwarare ta yadda cikin layi uku ko hudu za ka iya fasalta duk wani abu da kake so ya auku amma kar da ya wuce layi biyar - ka yi sassaukan bayani da ba za a ji kyuiyar karanta shi ba. 4. Ka guji bayar da labari, aukuwa kawai ake son nunawa - maimakon - a ga Falama yana sauri za shi gida  - ka rub...

SHAWARA GA MARUBUCI SCREENPLAY I

Screenplay       FADE IN 1.   KADUNA GIDAN S FALAMA - DAY    Cliphanger:  Suspense ne da marubuci ke kokarin    sakawa a karshen episode domin ya rike 'yan    kallo. Yana da kyawu amma a duk lokacin da marubuci ya fi mayar da hankalinsa ga cliphanger labarinsa zai sami nakasu saboda ba zai yi tunanin komai ba sai wannan.                                                                   CUT TO: 2.   KADUNA GIDAN S FALAMA  - DAY Shawara dole ne marubuci ya zama mai kaifin basira ta yadda za rika tuna dukkan labarinsa kuma ya zama kwararre ta yadda zai iya saka cliphenger ko da a scene one ne.                                               ...