Adam A Zango Adamu Zango Mai Zamani Amshi : Yaro adon gari, : Adamu Zango mai zamani, : Fasa taro. Jagora : Ni ne adon gari, : Matar aure ’yar asali, : Zan zaɓa... : Bisimilla Sarkina, : Allah Mai biyan buƙata, Karɓi : Lale lale. Jagora : Taimaken Allah, : Nai mata mai hali da tsafta, Karɓi : Lale lale. Jagora : Na saka ka a farko, : Rabbani Walla bai buƙata Karɓi : Lale lale. Jagora : Ɗan Abdalla ba na shan wahala, : Mai ado da kufta, Karɓi : Lale lale. Jagora : Rabbi kai kay yarje mui aure, : Don mu je mu huta, Amshi : Yaro adon gari, : Adamu Zango mai zamani, : Fasa taro. Jagora : Yau gashi ina so nai aure, : Auren addini, Karɓi : Lale lale. Jagora : Na sauka a Barno neman aure, : Wata ɗiya ta gan ni, Karɓi : Lale lale. Jagora : Ta ce mani “indawatu” : Adam taho gare ni, Karɓi : Lale lale. Jagora : Sai na ce, “kele wasile” : Aure na zo ku ba ni, Karɓi : Lale lale. Jagora : Na ji an ce kuna ado da tilare, : Na ke ce raini, A...