Adam A Zango
Adamu Zango Mai Zamani
Amshi : Yaro adon gari,
: Adamu Zango mai zamani,
: Fasa taro.
Jagora : Ni ne adon gari,
: Matar aure ’yar asali,
: Zan zaɓa...
: Bisimilla Sarkina,
: Allah Mai biyan buƙata,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Taimaken Allah,
: Nai mata mai hali da tsafta,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Na saka ka a farko,
: Rabbani Walla bai buƙata
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Ɗan Abdalla ba na shan wahala,
: Mai ado da kufta,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Rabbi kai kay yarje mui aure,
: Don mu je mu huta,
Amshi : Yaro adon gari,
: Adamu Zango mai zamani,
: Fasa taro.
Jagora : Yau gashi ina so nai aure,
: Auren addini,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Na sauka a Barno neman aure,
: Wata ɗiya ta gan ni,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Ta ce mani “indawatu”
: Adam taho gare ni,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Sai na ce, “kele wasile”
: Aure na zo ku ba ni,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Na ji an ce kuna ado da tilare,
: Na ke ce raini,
Amshi : Yaro adon gari,
: Adamu Zango mai zamani,
: Fasa taro.
Jagora : Na ce, “yaya sunanki,
: ’Yanmata mai diri da sura”
Karɓi : Sunana Falmata,
: Yarinyar da ba ta yin fitsara,
: Mu je gida ka gaida iyayena,
: Don kar kai min dabara,
: Idan kana da Naira ɗan Sarki,
: Ka zo mu je a ɗaura,
Jagora : Wayyo ’yanmata ni ba ni da Naira
: Yauna za ni na haura,
: Yanzu,
Amshi : Yaro adon gari,
: Adamu Zango mai zamani,
: Fasa taro.
Jagora : Sai na sauka a Yola,
: Tashan mota zan wuce Jimeta,
: Na ɗauki jaka zan tsallaka titi,
: Duk na jigata,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Ga ƙishi da yunwa ta dame ni,
: So nake na huta,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Sai na ga rijiyar burtsatai,
: Mata sun kewaye ta,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Kyakkyawa na cikinsu,
: Ta ba ni kofi na ruwa mai tsafta,
: In sha,
Amshi : Yaro adon gari,
: Adamu Zango mai zamani,
: Fasa taro.
Jagora : Sai ta ce da ni, “use”,
: Sai na amsa,
: Sai tai min murmushi na duba,
Karɓi : Kai kaɗo yaya sunanka,
:Ba na na ƙirƙiro ba.
Jagora : ’Yar Fullo,
: Sunana Adam Zango,
: Aure na zo na duba,
Karɓi : Ni ma dai bari ka ji sunana,
: Sunana Habiba,
: Sai kana da garken shanu,
: Za ka auri Habiba.
Amshi : Yaro adon gari,
: Adamu Zango mai zamani,
: Fasa taro.
Jagora : Ni ba ni da ko garken shanu,
: Naija za ni koma,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Ga ni nan a Naija garin Nufawa,
: Ina ta himma,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Ina da aboki a Fandulu,
: Da ƙanwarsa Karima
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Ya kai ni gidansu ya ba ni abinci,
: Sakwara da nama,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Ya ce ga Karima ta ba ni ruwa,
: Mai sanyi da ni’ima,
: Na sha,
Amshi : Yaro adon gari,
: Adamu Zango mai zamani,
: Fasa taro.
Karɓi : Adam zango uko kewano,
: Mai ka zo garinmu?
Jagora : Ƙanwata ina neman aure,
: Shin ko za ni samu?
Karɓi : Yayana shin kana son wace ce,
: A nan cikin garinmu?
Jagora : Ko ke zan aura ba komai,
: In har za a samu,
Karɓi : To za ka noma kunya dubu na doya,
: San nan ka samu!
Jagora : A’a ba zan iya ba na haƙura,
: Zan je Kano ta Dabo,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Ga ni ƙasar Kanawa Ƙofar Mata,
: Ina ta ƙwambo,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Sai ga wata bebi kyakkyawa,
: Ta sayi akumbo,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Ta sanya atamfa ta sha lalle,
: Tana ta bobo,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Muka haɗa idanu ni da ita,
: Muka yo kwalabo,
: Sosai,
Amshi : Yaro adon gari,
: Adamu Zango mai zamani,
: Fasa taro.
Jagora : Nan na ce mata ’yam mata,
: Don Allah na tambaye ki,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Na ga kyan diri kyawu da mutunci,
: Suna gare ki,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Na zo neman aure,
: Wane unguwa zan zo na gan ki,
Karɓi : Ni ’yar Gwammaja ce ’yar malam,
: Mai hali na kirki,
: In kana da haddan Ƙur’ani,
: Aurenmu babu burki,
: Ka ji,
Amshi : Yaro adon gari,
: Adamu Zango mai zamani,
: Fasa taro.
Jagora : Ni ba ni da hadda,
: Na sauke kuma na san hadisi
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Sai na sauka Zazzau,
: Birnin Shehu jikan Sunusi,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Na sauka a Gyalle,
: A wurin Alin Taro da Sisi,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Yana da shago na yin ɗinki,
: Mai ado da fansi.
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Sai ga wata kyakkya ta shigo,
: Mai asali na jinsi,
Amshi : Yaro adon gari,
: Adamu Zango mai zamani,
: Fasa taro.
Jagora : Na ce assalamu alaiki,
: ’Yam mat azan so na gan ki,
Karɓi : Wa alaikas salam Adam Zango,
: Na kawo maka ɗinki,
Jagora : A’a ba ni ɗinki ’yam mata,
: Ƙauna na zo na ba ki,
Karɓi : Aure ka zo mu yi ko ko soyayya,
: Gidanmu kai sadaki,
Jagora : Ta kai ni wurin abbanta,
: Dattijo ne yana da kirki,
Karɓi : Tambaya ta farko yaro,
: Kai ɗan wane gari ne?
: Kai ɗan wane ne kuma,
: Kai ɗan wane jinsin yare ne?
Jagora : Babana Ibrahim kuma ɗan Abdalla,
: Maƙerin nan ne,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Bahausen Zango ne ni,
: Baba ka je Fada za ka gane,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Sana’ata wasan Hausa,
: Da waƙa ɗan gidan malamai ne,
Karɓi : Yaro ka je ka turo iyayenka,
: Ni na ba ka Zainab,
Jagora : Wayyo baba ya ba ni Zainab,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Wayyo an ba ni Zainab,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Sosai an ba ni Zainab,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Ina son ki Zainab,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Ina ƙaunarki Zainab,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : I lobyu Zainab,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Na samu Zainab,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Yau baba ya ba ni Zainab,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Wayyo an ba ni Zainab,
Karɓi : Lale lale.
Jagora : Sosai an ba ni Zainab,
Karɓi : Lale lale.
Adam A Zango
Wayyo Ni Ina Son Ta
Jagora : Oh!
Karɓi : Wayyo!
Jagora : Ni ina son ta
Karɓi : Ni ina son ta,
Jagora : Wayyo!
Karɓi : Wayyo!
Jagora : Ni ina son ta,
Karɓi `: Ina son ta,
Jagora : Shuhuda,
: I lobyu Shuhuda
: Shuhuda,
: I lobyu Shu Shu Shu,
Jagora : Wata rana na haɗa kayana,
: Zan yi tafiya na yi shirina,
: Na ɗau ado za ni Abuja,
: Wurin buki na abokina,
: Na ga jama’a duka sun taru,
: Kowa da kowa na murna,
: A cikinsu na yi gamo da katar,
: Don tafiya mai ban sha’awa,
: Yarinya Shuhuda,
Karɓi : Shi yana son ki,
Jagora : Son ki ya,
Karɓi : Shiga rihinshi.
Jagora : Jalla kai ni,
Karɓi : Muradina,
Jagora : Eh, Shuhuda ki zan tawa,
: Ɓatad da kama daga Indiya,
: Da ɗaiɗaya taka takawa,
: Ta ɗau mayafi ta sanya,
: Jikinta duk ta yi rufewa,
: Sannan ga ta doguwa,
: Madaidaiciya ba kushewa,
: Adamu dai a tunanina,
: Budurwa ce mai hangowa,
: Na tambayi matar abokina,
: Sunanta daure ta gaya min,
: Wancan shin wace ce,
: Sunanta daure ki gaya min,
: Kamalarta da kimarta,
: Da shigarta biyu duka sun...
: Ina son ta da niyyar aure,
: In har ko ta lamunce min,
: Ta ce mun sunanta Shuhuda,
: Amma da Shu za ka sanin,
: Kwana biyu ya rage aurenta,
: Ina nufin an ba da ta,
: Dagan an sai nac ce na haƙura,
: A zuciyata na cire ta,
: Na bi umurnin Musulunci,
: Na dangana daga narkewa,
: Yarinya Shuhuda,
Karɓi : Yana son ki,
Jagora : Eh, son ki ya,
Karɓi : Shiga ruhinshi,
Jagora : Jalla kai ni,
Karɓi : Muradina,
Jagora : Eh, Shuhuda ki zan tawa,
: Tun a lokacin da na dawowa,
: Da safe gari ya wayewa,
: Na je ni jungun ummata,
: Zai gai da ita nai duƙawa,
: Sai ta gwadan hoton Rashida,
: A bayan mun gama gaisawa,
: Sai ta ce in aure ta,
: Hankalinta za ta fi kwantawa,
: Nan take na’ amsa batunta,
: Don faranta mata rayinta,
: Da na je na ga Rashida,
: Ni da ita sai muka daidaita,
: Anka ɗaura mana aure,
: Zaman lafiya muke ni da ita,
: Ba faɗa ba janjani,
: Junanmu ba mai kokawa,
: Hat ta kai mu ga mun haihu,
: Muka samu mai sunan baba,
: Yarinya Shuhuda,
Karɓi : Yana son ki,
Jagora : Eh, son ki ya,
Karɓi : Shiga ruhinshi,
Jagora : Jalla kai ni,
Karɓi : Muradina,
Jagora : Eh, Shuhuda ki zan tawa,
: A kwana a tashi kwatsam,
: Matar abokin nan nawa,
: Na fito daga aikina,
: Ni da ita sai munka haɗewa,
: Ita ce ta gayan cewa,
: Shuhuda dai ta yi fitowa,
: Kuma tana ta nema na,
: Lambar wayar ba ta shigowa,
: Nan take na ce mata to,
: Ko za ki ban lambarta,
: Ta ce mini ba komai,
: Zan ba ka har adireshinta,
: Ta ɗauka tab ba ni,
: Da zuwa gida na yi kiranta,
: Sunana Adamu Zango,
: Kalma ta farko da na furta,
: Buƙatata ki amince da ni,
: Aure na ƙauna mu ƙullawa,
: Ta yi dogon numfashi,
: Da ya sanya raina ya bugawa,
: Ta ce in mata uzuri,
: Za ta je ta yi shawartawa,
: Sai ta ce amma in sani,
: Ƙauna da ni ta yarjewa,
: Sai na ce mata ba komai,
: Na yarda na yi amincewa,
: Na yi karo da abun ƙauna,
: Mai hankali ’yar Larabawa,
: Eh, yarinya Shuhuda,
Karɓi : Yana son ki,
Jagora : Eh, son ki ya,
Karɓi : Shiga ruhinshi,
Jagora : Jalla kai ni,
Karɓi : Muradina,
Jagora : Eh, Shuhuda ki zan tawa,
: Ya Shuhuda ’yar asali,
: Haskenki tamkar ya na zara,
: Daure ki amince da ni,
: Don in samu shiga tsara,
: ’Yar Larabawa mai asali,
: Shuhuda mai kyawun sura,
: Mai dashe na farin ƙauna,
: Zan so in so....
: Eh, yarin Shuhuda,
Karɓi : Yana son ki,
Jagora : Eh, son ki ya,
Karɓi : Shiga ruhinshi,
Jagora : Jalla kai ni,
Karɓi : Muradina,
Jagora : Eh, Shuhuda ki zan tawa,
: Shuhuda madubina,
: Abin tunanin ruhina,
: Na kamu da ƙaunarki,
: Har ta sauya tunanina,
: Daure ki amince da ni,
: Shuhuda mui auren ƙauna,
: Na sunna mu yi rayawa,
: Har jama’a su yi ta yabawa,
: Eh, yarin Shuhuda,
Karɓi : Yana son ki,
Jagora : Eh, son ki ya,
Karɓi : Shiga ruhinshi,
Jagora : Jalla kai ni,
Karɓi : Muradina,
Jagora : Eh, Shuhuda ki zan tawa,
: Ya Shuhuda abar so na,
: Kanki kaina ya zautu,
: Sai ki nunan soyayya,
: Hakan ko lallai ya kyautu,
: ’Yan samari na kuka,
: A ba su ke wai sun bautu,
: Sai na ce duka sui haƙuri,
: Tun da dai ta zan tawa,
: Eh, yarin Shuhuda,
Karɓi : Yana son ki,
Jagora : Eh, son ki ya,
Karɓi : Shiga ruhinshi,
Jagora : Jalla kai ni,
Karɓi : Muradina,
Jagora : Eh, Shuhuda ki zan tawa,
: Kanki na yo kokawa,
: Ina zubar da hawayena,
: Don na cimma buƙatuna,
: Aurenki shi ne burina,
: Na so Shuhuda ’yar asali,
: Har wasu jama’a na zagi na,
: Ni fa lallai burina,
: Shuhuda dai ta zamo tawa,
: Eh, yarin Shuhuda,
Karɓi : Yana son ki,
Jagora : Eh, son ki ya,
Karɓi : Shiga ruhinshi,
Jagora : Jalla kai ni,
Karɓi : Muradina,
Jagora : Eh, Shuhuda ki zan tawa,
: Yarinya Shuhuda ina son ki,
: Son ki ya shiga ruhina,
: Jalla kai ni muradina,
: Shuhuda ki zan tawa,
: Eh, yarin Shuhuda,
Karɓi : Yana son ki,
Jagora : Eh, son ki ya,
Karɓi : Shiga ruhinshi,
Jagora : Jalla kai ni,
Karɓi : Muradina,
Jagora : Eh, Shuhuda ki zan tawa,
: Eh, yarin Shuhuda,
Karɓi : Yana son ki,
Jagora : Eh, son ki ya,
Karɓi : Shiga ruhinshi,
Jagora : Jalla kai ni,
Karɓi : Muradina,
Jagora : Eh, Shuhuda ki zan tawa.
Adam A Zango
Wayyo Kai Wannan Zamani
Jagora : Wayyo!
: Wayyo kai wannan zamani,
Jagora : Iyayen zamani,
Karɓi : Wannan zamani.
Jagora : Wayyo!
: Wayyo kai wannan zamani,
Karɓi : Wannan zamani.
Jagora : Iyayen zamani,
Karɓi : Wannan zamani.
Jagora : Matasan zamani,
Karɓi : Wannan zamani.
Jagora : ’Yam matan zamani,
Karɓi : Wannan zamani.
Jagora : ’Yan siyasan zamani,
Karɓi : Wannan zamani.
Jagora : Malaman zamani,
Karɓi : Wannan zamani.
Jagora : Masu kuɗin zamani,
Karɓi : Wannan zamani.
Jagora : ’Yan fim ɗin zamani,
Karɓi : Wannan zamani.
Jagora : Har ma da mawaƙan zamani,
Karɓi : Wannan zamani.
Jagora : Ku buɗe kunne ku ji,
: Waƙar Jatau mai magana,
: Ni ne likitan wannan zamani,
: Mai warƙar da cutar zamani,
: Jatau, uh! Uh!
: Wayyo, uh! Uh! Uh!
: Uh! Uh!
: Wayyo, uh! Uh! Uh!
: Allah mai zamani,
: Kuma shi ne zai mana magani,
: Allah mai zamani,
: To a daina zagin zamani,
: Rami rami na shiga,
: Ramin kura na shiga,
: Ramin damusa na shiga,
: Ramin ɓauna na shiga,
: Ramin alade na shiga,
: Ramin jaki na shiga,
: Ramin zaki na shiga,
: Amma zaki bai bar ni ba,
: Uh! Uh!
: Wayyo, uh! Uh! Uh!
: Kur uh! Uh! Uh!
: Uh! Uh!
: Wayyo, uh! Uh! Uh!
: Ramin kura na shiga,
: Labarin sai ku tsaya ku ji,
: Mutuwar aure a Hausawanmu,
: Abin har na gaji,
: Ina yin rangaji,
: Malamai a kawo agaji,
: Dangi-dangi na shiga,
: Babu dangin da babu bazauwara,
: An yo aure na zumunci,
: Jama’a ga auren ya rabu,
: An yo aure na soyayya,
: Jama’a auren ya rabu,
: An yo aure na dukiya,
: Jama’a aure ya rabu,
: An yo aure na ƙiyayya,
: Jama’a aure ya rabu,
: Jama’a ku biyo ni,
: Jatau yau za na ba ku magana,
: Haƙuri ne magana,
: Ilimin mata magana,
: Tarbiyyan mace magana,
: Ko da namijin bai yi shi ba,
: Uh! Uh!
: Wayyo, uh! Uh! Uh!
: Kur uh! Uh! Uh!
: Uh! Uh!
: Wayyo, uh! Uh! Uh!
: Malamanmu na zamani,
: Sai mu juya kallon zahiri,
: Ɗan wancan ƙungiya,
: Ya ce wa wancan kafiri,
: Shi ma ɗan ƙungiyancan,
: Ya ce wa wancan kafiri,
: To wai wa za mu bi,
: Ku faɗa mana kar mu tsaya jiri,
: Musulunci dai guda ce,
: Ba bambanci a zahiri,
: Jatau mai magani,
: Ku biyo ni zan ba ku magani,
: Tutan Manzon Allah,
: Annabi shi ne zamani,
: Ƙur’ani kalmal Allah,
: Littafi zamani,
: Uh! Uh!
: Wayyo, uh! Uh! Uh!
: Kur uh! Uh! Uh!
: Uh! Uh!
: Wayyo, uh! Uh! Uh!
: ’Yan siyasan zamani,
: Ku yi koyi da riƙon gaskiya,
: Talakawan zamani,
: Sun same ku da zuciya ɗaya,
: Sai ku yi adalci,
: In kun hau ku riƙe su da gaskiya,
: Kar ku manta sai da talakka,
: Mulkinku zai taffiya,
: In kau babu talakka,
: Mulkinku zai sankuya,
: Ah weye!
: Uh! Uh!
: Wayyo, uh! Uh! Uh!
: Kur uhu! Kur uhu!
: Eyee ye yee
: Wannan wanan wannan zamani,
: Allah ka tsare mu da zamani,
: Ƙarya wannan zamani,
: Hassada wannan zamani,
: Gulma a wannan zamani,
: Cuta wannan zamani,
: Sata wannan zamani,
: Yaudawara wannan zamani,
: Allah Ka tsare mana zamani,
: Uhu, Allah ka tsare mana zamani,
: Jatau, ni ne Jatau mai magani,
: Jatau, ni na ba ku magani,
: Wayyo, uhu,
: Wayyo kur,
: Wayyo, uh! Uh! Uh!
Adam A Zango
In Kuna Son Rawa Da Zango
Jagora : In kuna son rawa da Zango ku ce yayye!
Karɓi : Yayye!
Jagora : In kuna son ku gan ni Zango ku ce Ushe,
Karɓi : Ushe!
Jagora : In kuna son ku samu rahama ku ce Allah,
Karɓi : Allah!
Jagora : Walale walale walale,
Karɓi : Adam ya shigo gari,
Jagora : Ya shigo gari,
Karɓi : Yaro ne adon gari,
Jagora : Yaro ne adon gari,
Karɓi : Ya shigo garin KD,
Jagora : Eh!
: A Garin Kano da kwai Naira,
Jagora : Haka ne, haka ne!
Karɓi : Sannan muna da Sarki na Zazzagawa.
: Eh!
Jagora : Haka nan take,
Amshi : Adam ya shigo gari,
: Yaro ne adon gari,
: Ya shigo garin KD,
: A Garin Kano da kwai Naira,
: Sannan muna da Sarki na Zazzagawa.
: Eh.
Jagora : Na faɗa Ni Zango na riga na faɗa,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : In dai ilimi ne ka je Kaduna ka yo biɗa,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Mata da maza harkar ilimi babu yin faɗa,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Cibiyar Arewa Kaduna ce kar ka yo raɗa,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Sarkin Zazzau Shehu Idiris shi ma ya faɗa,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Ya ce kowa ya kama karatu ya bar faɗa,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Bar yawon banza Mahammadiyya a yo biɗa,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Eh...
Karɓi : Walale, walale walale,
Jagora : To in na ga dama, in na ga dama,
Karɓi : Ina za ka kwana?
Jagora : In na ga dama a gidan gwamna zan kwana,
Karɓi : Ka je ka kwana,
Jagora : In na ga dama a gidan sarki zan kwana,
Karɓi : In ya ba ka dama,
Jagora : Kai in na ga dama a garin Zazzau zan kwana,
Karɓi : Ka samu dama,
Jagora : In na ga dama a garin KD zan kwana,
Karɓi : Mun amunce ma,
Jagora : Eh...
Amshi : Adam ya shigo gari,
: Yaro ne adon gari,
: Ya shigo garin KD,
: A Garin Kano da kwai Naira,
: Sannan muna da Sarki na Zazzagawa.
: Eh, yeyye, Ushe!
: Yeyye, Ushe!
: Allah, walale walale walale.
Jagora : Masarautar Zazzau ta kere sa’o’inta da dama,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : A fagen yaƙi Zazzau jarumai an yi su da dama,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Ko Ƙur’ani idan ka duba za ka gani ma,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Akwai bugun Zazzau na malamai za mu jaddada ma,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Malam je ka Kusfa da malamai za su agaza ma,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Kaduna Garin Gwamna A.A. Zango nake faɗa ma,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : In kana da Naira ka je Kaduna ka ƙera gida ma,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Lallai ka cika mai kuɗi.
Karɓi : Eh, walale walale walale,
Jagora : In na ga dama in na ga dama,
Karɓi : Ina za ka kwana?
Jagora : In na ga dama Unguwar Dosa zan kwana,
Karɓi : Je ka kwana,
Jagora : Kuma in na ga dama Unguwar Shanu zan kwana,
Karɓi : Ka samu dama,
Jagora : Kuma in na ga dama Nasarawa ni za ni kwana,
Karɓi : Ka samu dama,
Jagora : Kuma in na ga dama Tudun Wada ni zan kwana,
Karɓi : Mun amunce ma,
Amshi : Adam ya shigo gari,
: Yaro ne adon gari,
: Ya shigo garin KD,
: A Garin Kano da kwai Naira,
: Sannan muna da Sarki na Zazzagawa.
: Eh, yeyye, Ushe!
: Yeyye, Ushe!
: Allah, walale walale walale.
Jagora : To Bisimillah,
: Na haɗa da sunan Allah,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Komai sai ka sa Allah,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Yau gani Kaduna Garin Gwamna,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Na taho na gai da gida ne,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora :’Yan Zango na gaishe gaba ɗaya,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Haɗa da Zankuwa da Zankuwa City,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : My people na Samunaka,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Lere da Doka har Mariri,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : ’Yan Kafanchan na gaishe ku,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Da ’yan Kaduna Ilove you people,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora :Yau ga ni a Zariya City,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Zo ka bi ni ku sha labari,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Na biyo ta Ƙofar Doka,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Ƙofar Kuyanbana, na shiga Kona,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Gaishe ku mutanen Ƙofar Gayan,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Ƙofar Kibo na Galadima,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Kirari : Lafiya Sarkin jikan Sarki,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Kirari : Lafiya mai nasara,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Kirari : Lafiya kirzau
Karɓi : Eh, oyoyo,
Kirari : Sarki mai yawan kaya,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Kirari : Sarki mai tarin sutura,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Kirari : Sarki mai tarihi,
Karɓi : Eh, oyoyo,
Kirari : Sarki baban sarakuna,
Kirari : Sarkin ...
Karɓi : Eh, oyoyo,
Jagora : Eh, in na ga dama in na ga dama,
Karɓi : Ina za ka kwana?
Jagora : In na ga dama Unguwar Sarki zan kwana,
Karɓi : Je ka kwana,
Jagora : In na ga dama Badarawa ni zan kwana,
Karɓi : Na ba ka dama,
Jagora : Kuma in na ga dama cikin Kawo ni zan kwana,
Karɓi : Ka samu dama,
Jagora : Kai in na ga dama Malali ni zan kwana,
Karɓi : Mun amunce ma,
Jagora : In kuna son rawa da Zango ku ce yayye!
Karɓi : Yayye!
Jagora : In kuna son ku gan ni Zango ku ce Ushe,
Karɓi : Ushe!
Jagora : In kuna son ku samu rahama ku ce Allah,
Karɓi : Allah!
Jagora : Walale walale walale,
Karɓi : Adam ya shigo gari,
Jagora : Ya shigo gari,
Karɓi : Yaro ne adon gari,
Jagora : Yaro ne adon gari,
Karɓi : Ya shigo garin KD,
Jagora : Eh!
: A Garin Kano da kwai Naira,
Jagora : Haka ne, haka ne!
Karɓi : Sannan muna da Sarki na Zazzagawa.
: Eh!
Jagora : Haka nan take,
Amshi : Adam ya shigo gari,
: Yaro ne adon gari,
: Ya shigo garin KD,
: A Garin Kano da kwai Naira,
: Sannan muna da Sarki na Zazzagawa.
: Eh.
: Adam ya shigo gari,
: Yaro ne adon gari,
: Ya shigo garin KD,
: A Garin Kano da kwai Naira,
: Sannan muna da Sarki na Zazzagawa.
: Eh.
: Adam ya shigo gari,
: Yaro ne adon gari,
: Ya shigo garin KD,
: A Garin Kano da kwai Naira,
: Sannan muna da Sarki na Zazzagawa.
: Eh.
Adam A. Zango
Duniya Ta Kusan Tashi
Jagora : Haka!
Karɓi : Yaf yaf yaf yaf yaf!
: Ruwan sama saka lumbayye,
Jagora : Haka!
Karɓi : Yaf yaf,
: Mai baiwa daga Allah Adam Zango.
Jagora : Yee yee ye ye yee yee!
: Duniya,
: Wayyo duniya ta zo ƙarshe,
: E, duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe,
Amshi : Duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe.
Jagora : E, bisimilla Allah Maƙagin Sarki, wanda yay sama babu gwafa,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Shi ke yin zafi har sanyi kuma yay mana bargo mu rufa,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Shi Rabbi ke sanya ciwo ya ba mu magani nai fa duba fa,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Uh, Ka ba ni ikon aikata kari, shi ko sharri mu kakkauce fa,
: Rabbi dom ba mu kauce ba,
Amshi : Duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe.
Jagora : E, rayuwar ta yi tsada kowa da tsarin da zai ɗabi’arsa,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Wani in ba gulma ya yo a kullum bai da ikon ya numfasa,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Wani ko burinsa ta yaya zai yi ya ƙuntata wa amininsa
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Wani ko bai ya jin daɗi sai ya yi hasada a cikin ransa,
: To hakan bai dace ba,
Amshi : Duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe.
Jagora : A zamanin yanzu babu zumunci ya riga ya lalace,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Wani ɗan’uwa ne yake ƙauna ya ga ɗan’uwan ya susuce,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Ka ga wa da kuɗi amma ƙannensa cikin talauci a ƙasƙance,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Ka ga ɗa da uba wai ana faɗa Wallahi ɗa ka lalace,
: Jahannama ba za ta ƙyale ba,
Amshi : Duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe.
Jagora : Wani sabon salo da bawa ke yi gun mace in ya je zance,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Um, sai ta sa hijabi ta saka shi ciki da sunan suna zance,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Sai kai ɗaya ƙafa guda huɗu a duhu zuciya ta gurɓace,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Da ka fara zuwa ba ka yin haka sai ta ce kai gara kauce,
: Wane sam bai gane ba,
Amshi : Duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe.
Jagora : E, irin gine-ginen da ake ta yi fa a duniyar ga ban gane ba,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Ka ga Ɗan’adam da mota saba’in shi kaɗai kamar ba za su ƙare ba,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Ginin gida ko ya zarta ɗari kai ka ce ba za su rushe ba,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Um ka ga uwa tana hana ’yarta zaman aure dom ba mai kuɗi ba,
: Mai yin hakam ba ta kyauta ba,
Amshi : Duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe.
Jagora : Haka! X2
Karɓi : Yaf yaf yaf yaf yaf!
: Ruwan sama saka lumbayye,
Jagora : Haka!
Karɓi : Yaf yaf,
: Mai baiwa daga Allah Adam Zango.
Jagora : Yee yee ye ye yee yee!
: Duniya,
: Wayyo duniya ta zo ƙarshe,
: E,
Amshi : Duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe.
Jagora : E A yau idan muka duba kwaɗayi yay yawa ba mu gane ba,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Um ba za ka aurat da ’yarka ba wai mai kuɗi kake hangowa,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Budurwa ta yi ta zama a gida kullum tana ƙara tsofewa,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Da ka je gun yarinya ta gane ba Dala sai ta zuƙewa,
: Ba zan soyayyar wahala ba,
Amshi : Duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe.
Jagora : Shi ne ya sa ga shi mata sun fi maza yawa sun ninninka
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : In za a bi kowa da goma-goma ragowar sai su ninninka,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Komai zurfin addininka in ba kuɗi za su ƙyale ka,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Um kana ji kama gani mai mota zai raba ka da bebinka,
: Ko bai karatun salla ba,
Amshi : Duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe.
Jagora : A ɓangaren maza mu ma matsala ce da mu ba ’yar ƙalilan ba,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Wani in macen ba shigar banza ba ta yi wai shi ba ta waye ba,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Ya za ki rinƙa ha’inta ta ki sa hijab ban gane ba,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Wani saurayi in ya je zance ta ƙi yai kis ba za ya koma ba,
: Wance sam ba ta waye ba,
: Alla!
Amshi : Duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe.
Jagora : Wani mai gidan a kullum a cikin matansa kullum sai ya fifita,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Ran kwanan ɗakin amarya tsire zai sayo da yajin citta,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Ita ko uwar gida ran kwananta tuwonta shi ne namanta,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Um da dafe amarya ta ci Indomi da ƙwai ɗayar ko ya ƙyale ta,
: Tun da ba sabuwa ce ba,
Amshi : Duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe.
Jagora : Allah Sarki ina roƙo ka fitar da ni sharrin masharranta,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Ka tsare ni ganin ƙyashin kowa ka guje ni yi wa kowa ƙeta,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Ka ƙara min son ManzonKa da masoyina in ma bauta,
Karɓi : Duniya ta zo ƙarshe,
Jagora : Da na ji zan yi wa wani kushe to zuciyata ka kulle ta,
: Ta yarda ba zan buɗe ba,
Amshi : Duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe.
Jagora : Eh duniya ta kusan tashi amma mutum bai gane ba,
: Duniya ta zo ƙarshe.
Karɓi : Yaf yaf yaf yaf yaf!
: Ruwan sama saka lumbayye,
Jagora : Haka!
Karɓi : Yaf yaf,
: Mai baiwa daga Allah Adam Zango.
Jagora : Haka!
Karɓi : Yaf yaf yaf yaf yaf!
: Ruwan sama saka lumbayye,
Jagora : Haka!
Karɓi : Yaf yaf,
: Mai baiwa daga Allah Adam Zango.
Adam A. Zango
Sarkin Zazzau Hanjin Jimina
Sanƙira : Gyara kimtsi,
: Gaba salamun baya salamun.
: Hadari sa gabakanka inda kake so Yariman Mawaƙa,
: Mu je zuwa, aha!
Jagora : Adam Zango mai gari,
: Yaro ne adon gari,
: O’o o, o’o o, oo,
Sanƙira : Toh, toh, to!
Amshi : Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora : Ga mai darajar farko matsayi,
: Sarkin Zazzau hanjin jimina,
Karɓi : Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka daban babban sarki.
Jagora : Kai duk tsananin ramar doki,
Karɓi : Kofato na nan bai ramewa,
: Haka Rabbi yake aje hikimarsa,
Jagora : To ga Sarkin Zazzau,
: Shehu Idiris mai takalman ƙare,
: Toh,
Amshi : Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora : Ga mai darahar farko matsayi,
: Sarkin Zazzau hanjin jimina,
Karɓi : Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka,
Jagora : Um!
Karɓi : Daban babban sarki.
Jagora : Ga mai ƙarfi Dagacin mutuwa,
Karɓi : Sankace da maciji dauji kar,
: Sarkin Zazau tafiya sannu,
Jagora : Um!
Karɓi : Ga gamji mazajen alfarma,
Jagora : Farko da na sauka garin Zazzau,
: Na yi ado na sa kubta,
: Na hau doki na sarauta,
Rawani kuma an muni mai kima,
Karɓi : Toh,
: Za shi gidan babban sarki.
Jagora : Kai Tasi’u saurara ka jiya,
: Da na sauka garin Birnin Zazzau,
: Na ga kalar matan Zazzau,
: Da ado tamkar matan Makka,
: Ga shi ina son mu yi hira,
: In ji labari na gidan sarki,
Karɓi : To amma kuma sam ba dama,
: Musulunci bai yarje ma ba.
Jagora : Um!
Karɓi : In ka bi ta zancena.
Jagora : Me ya sa na ga matan Zazzau,
: A ado sun zarce sun kera,
Karɓi : To ko tarihin tafi ɗauko,
: Sarauniyar Zazzau a Arewa,
: Ba wanda ya kai ta ajin girma.
Jagora : To gani gaban fadar sarki,
: Sarkin Zazzau mai alfarma,
: Toh,
Amshi : Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora : Ga mai darahar farko matsayi,
: Sarkin Zazzau hanjin jimina,
Karɓi : Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka,
Jagora : Um!
Karɓi : Daban babban sarki.
Jagora : Farfesun kunama sun san ka,
: Matsayinka daban babban sarki,
Karɓi : Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka,
Jagora : Um!
Karɓi : Daban babban sarki.
Jagora : Yau ga ni gaban gidan sarki,
: Ina tafiya ta cikin ƙawa,
: Wai ni da zan shiga fada,
: Kamar ɗaki na ka ji wawa,
: Ko da na zo bakin ƙofa,
: Sai fadawa suka miƙe,
: Sadaukai da ido jajaye,
Karɓi : Kai gyara kimtsi bi a sannu,
: Gidan sarki ba shigifa ba,
: Jihar can Sakkwato nai zance,
Jagora : To a cikinsu akwai wani ma,
: Da babbar riga ga rawani,
: Sai na ji ya ce kai yaro,
: Ya daka mani tsawa nar ruɗe,
Karɓi : Sai munka kowa zazzaune,
: Yana mai martaba bar ka dai,
: A zatonsa kamar sarki yaz zo.
Jagora : Sai mutumin nan yam miƙe,
: Yac ce mini yaro kai taso,
: Me za kai a gidan sarki?
Karɓi : Mai martaba munka taho mu gani,
: Mun ji yanda yake adalcinsa,
Jagora : To kai yaro ya sunanka,
: Kuma kai ɗan wanne gari ne?
Karɓi : Kai Adam Zango ake ce ma,
: A Kaduna kake muka amsa mai,
Jagora : Kai Tasi’u da ba don kai ba,
: Ni ban san me zan furta mai ba,
: Toh!
Amshi : Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora : Ga mai darajar farko matsayi,
: Sarkin Zazzau hanjin jimina,
Karɓi : Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka,
Jagora : Um!
Karɓi : Daban babban sarki.
Jagora : To sun ƙyale duk sun yarje,
: Na shiga hanya na miƙe,
: Zan je fadar mai Zazzau,
Karɓi : Sai dai kuma ba ka san hanya ba,
: Gidan sarkin da akwai girma.
Jagora : Sai na ga al’umma zaune,
: Sun sha kaya na mutunci,
: Na yi tunanin baƙi ne,
: Ashe duka bayin sarki ne,
Karɓi : To ya riƙe daraja kimarsu,
Jagora : Um!
Karɓi : Kamar ma ba bayi ne ba.
Jagora : Da na je ni gaba na gaishe su,
: Su kuma duka sun amsa,
: Bayan kowa ya yi shuru,
: Sai na ciro magana ƙwara,
: Ni dai farko baƙo ne,
: Na zo fadar sarki ne,
: Shin ko ku ne ’yan fada?
: In kuma ku ne ’yan fada?
: Ya za a yi sarki in gan shi?
Karɓi : A’a ba mu ne fada ba,
: Ga fadar can gefen hauni,
Jagora : Sarkin Zazzau mai girma,
: Ɗawisu adon tafiya kai ne,
: Toh!
Amshi : Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora : Ga mai darajar farko matsayi,
: Sarkin Zazzau hanjin jimina,
Karɓi : Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka,
Jagora : Um!
Karɓi : Daban babban sarki.
Jagoa : To ga ni cikin fadar sarki,
: Wazirin Sarki na zaune,
: Ga Hakimai duka na zaune,
: Ga Fadawa na zaune,
: Sai na ga wani ɗan dattijo,
: Mai siffa kamar Balarabe,
: Ya ci ado da alkyabba,
: Ga ƙamshi mai tashin ƙawa,
: Toh!
Karɓi : Allah kare sarki,
: Ɗan Idirisa daɗo girma.
Jagora : A gaban sarki na taho na zube,
: Ina ta kirari a gabansa,
: Kura mai firgita kalbu,
: Ganga mai fatar giwa,
: Ƙarko da nagarta shi an nan,
: Fage na yaƙi sai sulke,
: Duka da bugu sai ’yan barka,
: Munjirya ka wuce kamun yaro,
: Ko babba yana shakka,
: Karya gwafa shahon ƙarfe,
: Jifa a cikin ruwa shirme ne,
: Adon sama’u kake sarki,
: Zara kake mai taurari,
: Mu dai sai sa albarka,
: Buzun bushiya ba a imma,
: Kai ni Zango a wurina,
: Duk sarakuna ai ka fi su,
: Toh
Amshi : Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora : Sarkin Zazzau mai girma,
: Ɗawisu adon tafiya kai ne,
: Toh!
Karɓi : Allah kare sarki,
: Ɗan Idirisa daɗo girma.
Jagora : Daga nan shauƙi yak kwashe ni,
: Na ci gaba da kirarin mai girma,
Karɓi : Sarari mai ƙare gudun doki,
: Tsawa sa karkarwa.
Jagora : Toh, toh!
Karɓi : Tsakar dare hana tafiya,
: Ragayar dutse ajalin yaro.
Jagora : Um!
Karɓi : Allah kare sarki,
: Ɗan Idirisa daɗo girma.
Jagora : You are the man of the people,
: You are the last man standing,
: You are the almighty king,
: Shin a Arewa kuwa dak kamarsa?
: Toh!
Karɓi : Kai Zango ka saita batunka,
: Don kana gaban sarki ne.
Jagora : Bari Tasi’u sai na ƙara,
: He is the greater than Sarakuna,
Karɓi : You are special ɗan Zango,
Jagora : Well done,
Karɓi : Turancin sai mun ɗana.
Jagora : Rabi kare Sarkin Zazzau,
: Mai martaba ubana babba,
Amshi : Ga kambun mafarauta,
: Dogon barde hancin giwa.
Jagora : Ga mai darajar farko matsayi,
: Sarkin Zazzau hanjin jimina,
Karɓi : Kowa ya ci sai ya lalace,
: Matsayinka,
Jagora : Um!
Karɓi : Daban babban sarki.
Sanƙira : Gyara kimtsi,
: Gaba salamun baya salamun.
: Hadari sa gabakanka
: Yariman mawaƙa mu je zuwa
: Ahah!
Jagora : Adam Zango mai gari,
: Yaro ne adon gari,
: O’o o, o’o o, oo,
Adam A. Zamgo
Tsumagiya
Jagora : Tsumagiya!
Amshi : Gumban dutse,
: Igiyar ruwa mai sartse,
: Ragayar dutse,
: Ajalin mai ɗaki sai jigo.
Jagora : Toh, toh, toh!
: Shi ɗan Adam mai cin zali nasa,
: Na sama ke take na ƙarƙasa,
: Babu imani a zuciyarmu,
: Yanzu kowa tasa yake,
Karɓi : Tasa,
: Kun ji Adam Zango,
Jagora : Um!
: Zantuka zai ƙirgo,
Jagora : Um!
Karɓi : Ku saurara ku ji zancensa,
Jagora : Toh, toh, toh!
Karɓi : Abin da Zango ya hango.
Jagora : E.. na faɗa na ƙara,
: Ɗan’adam ba ya tsoron Allah,
Karɓi : Um!
Jagora : Sannan a cikinsu ƙalilan,
: Wasu ke aikin Allah
Karɓi : Um!
Jagora : Wasu sun samu duniya,
: Suna ta ɗibar daula,
Karɓi : Um!
Jagora : Wasu ko ba su da komai,
: Kullum idonsu da ƙwalla,
Karɓi : E, mutaimaka don Allah,
Jagora : Wayyo!
Karɓi : Mu so juna da amana.
Jagora : Um!
Karɓi : Sannan mu zauna lafiya.
Jagora : Aha!
Karɓi : Mu canza halayenmu,
: Saboda rayuwar ga ba ta da tabbas,
Jagora : Eh...
Amshi : Gumban dutse,
Jagora : Toh,
Karɓi : Igiyar ruwa mai sartse,
Jagora : Uhum!
Karɓi : Ragayar dutse,
: Ajalin mai ɗaki sai jigo.
Karɓi2 : Um! Malam Adam Zango,
: Ga tambayata zan yi maka,
: Rayuwa da akwai matsala,
: Da me da me fa ka fuskanta.
Jagora : Kai, El-Mu’az bari zancen nan!
: Rayuwarmu akwai muni,
: Kowa duk ya juye,
: Hausawa sun juye,
: Yaren ma duka sun juye,
: Ka ga ’ya ta bunƙasa,
: Ba aure sai dai yawo,
Karɓi2 : Kai dakata Malam Zango,
: Ai laifin na samari ne!
Jagora : A’ a’a na iyaye ne,
: Wasu sai ka ga sun ba ’ya’ya,
: Na ta ɗaukan nauyinsu,
Karɓi2 : To hakan wai baiwa ce?
Jagora : Kai El-Mu’az wace baiwa ce,
: Za ka ga ’yarka cikin daula,
: Ba ka san sana’arta ba ma,
: Za ka ga wai ta sai Hala,
: Rayuwa sai lahaula!
Karɓi : Adam Zango akwai illa?
Jagora : E, tabbas fa akwai matsala,
: Burin kowa dai daula,
Karɓi : Kai
: Gumban dutse,
Jagora : Toh,
Karɓi : Igiyar ruwa mai sartse,
Jagora : Uhum!
Karɓi : Ragayar dutse,
: Ajalin mai ɗaki sai jigo.
Jagora : Eh... iyaye dole ku yo tsari,
: Ku dinga bincika ’ya’yanku,
: Ko yo tarbiyyar ’ya’yanku,
: Waɗannda Allah yab ba ku,
: Ku ƙaunaci ’ya’yanku,
: Sai Allah ya ji tausanku.
Karɓi : Yarima fa ɗan Zango,
: Wasu sun ce ka kwafsa,
: Wai don ka faɗi halinsu.
Jagora : Kai ƙyale su da shirmensu,
: Da ma kowa ya san su,
: Mai son ya ji sunansu,
: Ya bi ni zan zazzano su,
Karɓi : A’ a’a Zango da ka bar su,
: Do ni ma ai na san su,
Karɓi2 : Zango mai zamani,
: Ya ka ga wannan zamani?
Jagora : El-Ma’az da ka bar ni,
: Halayen fa akwai muni,
: An yarda akwai ƙaddara,
: Ta zo sai fa a ce Allah,
: Gidanka da ya ƙone,
Karɓi : Ka ji an ce yin haka sai Allah!
Jagora : Motarka da an sace,
Karɓi : Ka ji an ce yin haka sai Allah!
Jagora : Ga wani ya rasa matarsa,
: Ga wani ya rasa ’ya’yansa,
Karɓi : Sai a gaya maka yin haka sai Allah!
Amshi : Gumban dutse,
Jagora : Toh,
Karɓi : Igiyar ruwa mai sartse,
Jagora : Uhum!
Karɓi : Ragayar dutse,
: Ajalin mai ɗaki sai jigo.
Karɓi2 : Malam Zango,
: Wai ya zancen Naira?
Jagora : To in ka yi kuɗi yanzu,
: Ba a gaya maka sai Allah,
: Sai a ce ai mun san shi,
: Da can ba shi da ko sisi,
: Daga ya bi su Lasisi Abuja,
: Kila suka sisi,
: Ko jini ko kan yaro,
: Ko kuma an bi ta bayan shi,
Karɓi : Ka ji sun mata akwai Allah!
: Da ya yay talauci yay daula.
Jagora : E...
Karɓi : Kun ji Adam Zango,
Jagora : Um!
Karɓi : Zantuka zai ƙirgo,
Jagora : Um!
Karɓi : Ku saurara ku ji zancensa,
Jagora : Toh, toh, toh!
Karɓi : Abin da Zango ya hango.
Jagora : E.. ka ga zance addini,
: Abin ya canza kalar launi,
: Da Bahaushe ya ɗauka,
: Cewa shi ne mai addini,
Karɓi : A’a wanda duk ko ya ɗau Allah,
: Da Muhammadu manzonsa,
: To Musulunci ne tsani.
Jagora : Idan Iyamuri na salla,
Karɓi : Sai ka ji an ce wai tubabbe ne,
Jagora : Katafawa na salla,
Karɓi : Sai ka ji an ce tuba ne,
Jagora : Idan Igala ya ce Allah,
Karɓi : Ka ji an ce sabon tuba ne,
Jagora : In ka ga ɗan TV na salla,
Karɓi : Shi ma sai ka ji tuba ne,
Jagora : E, to ku sani a gurin Allah,
: Dukkaninku Musulmi ne,
: ’Yan’uwan kuma juna ne,
: Ƙur’aninmu guda ɗaya ne,
Karɓi : Eh
: Kun ji Adam Zango,
Jagora : Um!
Karɓi : Zantuka zai ƙirgo,
Jagora : Um!
Karɓi : Ku saurara ku ji zancensa,
Jagora : Toh, toh, toh!
Karɓi : Abin da Zango ya hango.
Jagora : Eh..
Amshi : Gumban dutse,
Jagora : Toh!
Karɓi : Igiyar ruwa mai sartse,
Jagora : Uhum!
Amshi : Ragayar dutse,
: Ajalin mai ɗaki sai jigo.
Karɓi : Adamu ya maganar waƙa,
: Don wasu sun ce shirme ce?
Jagora : Kai waƙa ai baiwa ce,
: In ka iya ta ko ka dace,
: Don jahili ba ya waƙa,
Karɓi : Wasu sun ce laifi ce,
: Da ka fara ta ka kauce?
Jagora : Kai ƙyale duka sun zauce,
: Sana’ar waƙa ilimi ce,
: In ka tsaftace harshenka,
: Ka gyara tunani ka dace,
Karɓi : Na gane tunaninka,
: Zango ni ma na auna.
Jagora : Ai kowacce irin sana’a,
: Za ka samu wutarka da aljanna,
: Gatan Zango waƙa,
: Ilimin Zango waƙa,
: A cikinta ko nai jari,
: Kuma ba na yin ƙari,
: Kai gorin ilimin boko,
: Ni kuma Zango akwai jari,
: Sana’ata ga tsari,
: Ni na yo ilimin bokon,
: Ƙarshe waƙa ce jari,
: Kai ku ji Allah mai khairi,
Karɓi : E Zango dodon waƙa,
: Me za ka ce wa abokanka?
Jagora/ : Allah shi muku albarka,
Karɓi : Mai barci kuma yaf farka,
: Im mun ilimin bokon,
: Sana’ar hunnu mu ɗan kama,
: Wani walda yak kama,
: Waɗansu su je su yi kafinta,
: Wasu na gyaran famfo,
: Waɗansu na aikin doki,
: Wasu ’yan fim ne malam,
: Waɗansu na harkar waƙa,
: Wani na ɗaukar hoto,
: Waɗansu na turin baro,
: Wanda duk ya riƙe sana’a,
: Allah kai masa kai albarka,
: Don wata rana ya zam zaki,
: Nan shi ne ƙarshen waƙar
Sa ido sana’ar banza!
Adam A. Zango
Sharafi
Jagora : Eye, ku zo ku ji tarihina,
: Labarin yaro Ado,
: Sharafi, sharafi,
Amshi : Ku zo ku ji labarin,
: Tarihin yaro Ado,
: Yaro mai sharafi,
: Sharafi sharafi.
Jagora : Ga ta nan ga ta nanku,
Karɓi : Ta zo mu ji ta,
: Sharafi.
Jagora : Ku sani dai,
: A Kaduna State aka haifan,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Gari na mahaifa,
: Zango ne shi ne taken,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Tun ina ƙaramina,
: Abbana ya yi macewa,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Allah ka jiƙan,
: Ibraahima can a kushewa,
Karɓi : Allah amin.
Jagora : Ina gani da idona,
: Tarzoma an yi a gabana,
Karɓi : Allah ya kiyaye,
Jagora : Ina kallo,
: An kashe yayyena a gabana,
Karɓi : Allah ka jiƙansu da gafara.
Jagora : Don haka ne,
: Nak koma Jos gun kawuna,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Can nai makaranta,
: Boko har ma Islama,
: Sharafi,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
: Yaro mai sharafi.
Amshi : Ku zo ku ji labarin,
: Tarihin yaro Ado,
: Yaro mai sharafi,
: Sharafi sharafi.
Jagora : Na kamala sakandare,
: Sai karatu yay y tsayawa,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Ba aikin yi,
: Babu kuɗin da zan yi kashewa,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Sai nai yi tunani,
: In shiga fim ɗin Hausa,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Sai na tattara kayana,
: Nat tafi tashan mota,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Sai direba ya ce min,
: Wai ina za ka je Ado?
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Sai na ce garin,
: Mai Martaba Sarki Ado,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Kanon Dabo,
: Ko da mai ka je an fi ka,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Sai ga ni Fage,
: Na sauka gidan innata
Karɓi : Yaro mai sharafi.
: Yaro mai sharafi.
Jagora : Sharafi sharafi,
Amshi : Ku zo ku ji labarin,
: Tarihin yaro Ado,
: Yaro mai sharafi,
: Sharafi sharafi.
Jagora : Washe gari na je,
: …
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Lense Cope Media,
: Gun Salisu Mu’azu,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Nas same shi,
: Salisu yai mini marahabin,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Ya ba ni abinci,
: Na ci nai ƙat ban manta ba,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Bayan na huta,
: Ya ce kai Adam Zango!
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Me ya kawo ka,
: Mene ne kaz zo yi nema?
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Na ce Oga,
: Na zo ne nai fim ɗin Hausa,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : In zama kamar,
: Ali Nuhu ko S. Nuhu,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Sai yai dariya,
: Ya ce Allah zai yi ma,
: Sharafi,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
: Yaro mai sharafi.
Jagora : Sharafi sharafi
Amshi : Ku zo ku ji labarin,
: Tarihin yaro Ado,
: Yaro mai sharafi,
: Sharafi sharafi.
Jagora : A kwana a tashi,
: Sai ga ni ina yin kiɗa,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : A kwana a tashi,
: Sai ga ni ina yin waƙa,
Jagora : A kwana a tashi,
: Sai ga ni a fim ɗin Hausa,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Har na yi suna,
: Na kere sa’annina,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Jama’a sun sanni,
: Duk mai kallon fim ɗin Hausa,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Kowa ya sanni,
: Idan yana jin waƙar Hausa,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Ai dole ka sanni,
: Idan kana jin kiɗin Hausa,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : A fage na kiɗa,
: Danko ai shi ne ogana,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : A fagen waƙa,
: Bily O ne ogana,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : A fagen shirin Hausa,
: Ali Nuhu ne ogana,
: Sharafi,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Amshi : Ku zo ku ji labarin,
: Tarihin yaro Ado,
: Yaro mai sharafi,
: Sharafi sharafi.
Jagora : Na zauna da mutane,
: Masu ɗimbin ƙauna ta,
Karɓi : Yaro mai sharafi.
Jagora : Ali Nuhu,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Auwal MD,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Salisu Mu’azu,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Ibrahim Danko,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Naziru Hausawa,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Maryam Mashhama,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Kalil Jamani,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Kalid Kachiya,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Falalu Ɗorayi,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Mai gaskiya,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Safiya Musa,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Tijjani Asasi,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Tahir I Tahir,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Baban Chinedu,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Mika’il Gidigo,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Umar Kanu,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Awwal Isa West,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Tijjani Albasha,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Mansur Sadik,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Lawal Ahmad,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Tijjani Kazaure,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Abubakar Sani,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Jamil Kazaure,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Aminu Sulpur,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Maryam Sangandali,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Jamilan Sadi,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Azazi SB Jakara,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Abubakar Hunter,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Jamilu Kochila,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Saifullahi,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Mukhtar Uzi,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Sharu na Gudu,
Karɓi : A Zango yana gaishe ku.
Jagora : Lawan Alasan Ƙaura,
: Sharafi,
Amshi : Ku zo ku ji labarin,
: Tarihin yaro Ado,
: Yaro mai sharafi,
: Sharafi sarafi.
Jagora : Ku zo ku ji tarihina,
: Labarin yaro Ado,
: Sharafi, sharafi,
Comments
Post a Comment