Skip to main content

Posts

Showing posts from July, 2025

adamu zango

Adam A Zango Adamu Zango Mai Zamani Amshi : Yaro adon gari, : Adamu Zango mai zamani, : Fasa taro. Jagora : Ni ne adon gari, : Matar aure ’yar asali, : Zan zaɓa... : Bisimilla Sarkina, : Allah Mai biyan buƙata, Karɓi : Lale lale. Jagora : Taimaken Allah, : Nai mata mai hali da tsafta, Karɓi : Lale lale. Jagora : Na saka ka a farko, : Rabbani Walla bai buƙata Karɓi : Lale lale. Jagora : Ɗan Abdalla ba na shan wahala, : Mai ado da kufta, Karɓi : Lale lale. Jagora : Rabbi kai kay yarje mui aure, : Don mu je mu huta, Amshi : Yaro adon gari, : Adamu Zango mai zamani, : Fasa taro. Jagora : Yau gashi ina so nai aure, : Auren addini, Karɓi : Lale lale. Jagora : Na sauka a Barno neman aure, : Wata ɗiya ta gan ni, Karɓi : Lale lale. Jagora : Ta ce mani “indawatu” : Adam taho gare ni, Karɓi : Lale lale. Jagora : Sai na ce, “kele wasile” : Aure na zo ku ba ni, Karɓi : Lale lale. Jagora : Na ji an ce kuna ado da tilare, : Na ke ce raini, A...

Sirrin Zuci

sadik zazzab

Ratayen Wasu Waƙoƙin Mawaƙan Da Aka Nazarta Sadik Zazzaɓi Ba Za Su Rage Ka Da Komai Ba... Amshi : Ba za su rage ka da komai ba, x 4 : Domin ba su fi ka da komai ba, x 4 : Ƙashin sama gagara ɗan kwaure, : Gidan sama sai babban tsuntsu, : Mazan jiya sannu mazan fama, : Mukhtar Ramalana jan gwarzo. Jagora : Ba za su rage ka da komai ba, : Domin ba su fi ka da komai ba,  : Ƙashin sama gagara ɗan kwaure, : Gidan sama sai babban tsuntsu, : Mazan jiya sannu mazan fama, : Mukhtar Ramalana gwanina ni.  Amshi : Ba za su rage ka da komai ba, : Domin ba su fi ka da komai ba, : Ƙashin sama gagara ɗan kwaure, : Gidan sama sai babban tsuntsu, : Mazan jiya sannu mazan fama, : Mukhtar Ramalana jan gwarzo. Jagora : Ƙahharu daɗa mana rinjaye, : A kan maƙiya ba don mu ba, : Idan ka zamo mana jagora, : Kaidinsu ba zai mana komai ba, : Kai yadda kai ma Ashabil Fil, : Ba su kumma yin ganganci ba, : Kowa aka yi wa zalinci, : Ba ka ƙi zama masa gata ba, : Ka tabbata kai ne Alƙ...