Skip to main content

Hausa Karin Magana


KARIN MAGANA KARIN MAGA CE
KARIN MAGANA zance ne na azanci da ya yi kama da waƙa da ke labarta tunanin mutum game da yadda rayuwa take.

KARIN MAGANA, kalmomi ne guda biyu da aka sarƙe su ta hanyar amfani da madanganci, don haka, ɗaya daga cikin kalmomin sifa ce. Idan har ka gane wecce ce sifar? Kilan ka ce magana, to, sai ka dirke kalmar KARIN MAGANA da jinsin namiji, saboda kana nufin kalmar KARI ita ce suna. Idan kuwa kalnmar KARI ne, sifar, to, sai ka dirke kalmar KARIN MAGANA da jinsin mace, saboda kalmar, MAGANA kalma ce mai jinsin mata. 


Ba a waiwanta KARIN MAGANA, wato, ba a sanya kalmar WAI a cikin karin maganaga, sai dai idan wacce ta zo da wai ɗin ce, kamar: Wai ma zancen banza, ko Mai amfani da wai, zunubinsa ke daɗuwa, da sauransu, waɗanda kuma ba su da yawa, a iya bincike na. Don haka, wai tababa, ba tabbaci take gwadawa, tana nuna rauni ne, KARIN MAGANA kuwa, tana nuna tabbaci ne da ƙarfin hujjar mai magana. Duba littafin SHAWARWARI GUDA 105 GA MARUBUCI, ya yi bayani a kan waiwanta karin magana.

Wasu na karkarsa KARIN MAGANA, ko su ce ire-iren karin magana, sai su bayyana SALON TSARI na karin magana a matsayin kashe-kashensa, wanda ni kuwa, ba haka nan na kalla ba. Na nazarci yadda KARIN MAGANGANUN ne suka zo wa Bahaushe sai na rarraba su haka. Wato da zangunan da aka biyo na yi amfani su, shi ya sa na ce akwai:

Akwai karin magana lokacin Maguzanci
Karin magana bayan saduwa da Larabawa
Karin magana bayan zuwan Turawa
Karin magana lokacin da bariki ya bunƙasa
Karin magana zamanin siyasa
Da yawa wannan fasali na rarraba KARIN MAGANA zuwa zangunan da ta ratso, ana yi masa a-sha-ruwan-tsuntsaye ne, sai dai kawai a ce: 

Duk karin maganar da ta yi kama da addi-addini, to, bayan zuwan Musulunci ta auku.
Duk karin maganar ta yi kama da tsafi-tsafi ko bori-bori, wannan ta faru ne kafin zuwan Musulunci.

Haka kuma, karin maganar da ta nuna wayewa irin ta Nasara, ita ta ma bayan zuwan Turawa aka same ta.

To a gaskiya, in dai wannan ne mazubin an taƙaita, saboda ke nan, da an tsintsince waɗannan sauran kuma fa, Waɗanda ba su yi kama da waɗannan ba. Kuma meye hujjarka ta cewa karin maganar da ka kawo ta wannan zamanin ce da kake bayani, misali:

An ba da misalin KARIN MAGANA kafin zuwan MUSULUNCI da, AIKIN BANZA, LALLE A ƊUWAWU, ni in ka ƙyale ni, zan ce, wannan karin maganar ta faru ne bayan zuwan Musulun ci, saboda, lalle wani abu ne da ya shafi Musulunci da ake yin sa a hannu da ƙafa. Sai kuma in ce, Bamaguje yana amfani ne da lalle domin ya yi wa amarya wanka, ko ya ɗaura a ɗan yatsar da yake yi masa ciwon ɗan karkare.
KARIN MAGANAR ya fi babu, Bature da baƙin ɗa, sai dai a sauya ta da wani abu, amma babu dalilin faɗin haka, Filani ake yi wa ba’a da cewa, ya fi babu..., saboda an san su farare ne, don haka duk Bafilatanar da aka gani da baƙin ɗa sai a yi mata ba’a cewa ta zo da sabon abu. Ita kuwa sai ta kada baki ta ce, YA FI BABU. 
Bari mu kawo wasu misalai a ɗan yi bayanin kaɗan:

YASIN ƊIN ƊAN BARNO, cewa aka ɗan Barno ne ya ajiye garin burabuskonsa, sai aka zo aka sace, ko da ya zo ya gani ransa ya ɓaci, ya ga shi ba zai iya haƙura ba, sai ya ce sai ya ja Yasin, da ɓarawon da ya ɗauka da wanda ya gani da wanda aka sayar wa kai da wanda ma ya yi dakon burabuskonsa. Aka ce da shi kai ɗan Barno, wanda ya yi dako me ruwansa? Sai ya ce to shi ke nan. Sai ya sake lissafo waɗanda zai yi wa Yasin ƙarshe sai ya ƙara da cewa, da wanda ta ce me ruwan ɗan dako ma.

Ka ga wannan karin maganar, ta auku ne bayan zuwan Musulunci bayan an yi karatu har an san laƙunƙuna da ake amfani da su don a taimaki kai.

SHUKAR GYAƊAR ƊAN BARNO, ɗan Barno ne ya zo ƙasar Hausa ya dame su da roƙo. Ana nan sai damina ta faɗi, aka ce da shi ɗan Barno ka ga da wannan bara-barar da kake yi, ka zo a ba ka gona ko gyaɗa ka shuka, ka ga ko ba ka ci ba ka sayar ka sami abin zaman gari. Aka samu da ƙyar ya yarda zai yi noma. Aka ba shi gona aka kwatanta masa yadda zai yi. Gogan da ya zo shuka, idan ya ɗebi ƙwaya uku ya zuba a rami sai ya ce, WATAKILA, sai ya mayar da ƙasa ya rufe, sai kuma ya ɗebi bakwai ko goma sai ya watsa a baki sai ya ce, TABBAS.

To, wannan karin maganar ta yaya za ka gane cewa ga zangon da ta ke? Mu saka ta a mala kai ka gano mana?

IZAJA’A TA GAJI, wani Babarbare ne ya koyi sana’ar banza, wato fasa-ƙwaurin miyagun ƙwayoyi, ga shi ya manyanta amma ya ƙi ya bari. To dabarar da yake yi, a buta yake zubawa, kuma a ƙafa yake fita da shi zuwa ƙasar da yake so. Yadda yake yi, da mota ta kawo su bakin boda, sai ya sauka ya shimfi&a buzunsa ya yi nafiloli, ya ɗaga hannu ya yi addu’a, sai ya gaisa da ma’aikatan da ke wurin. Su yi masa baba an zo lafiya? Ya amsa.  

Bayan tsawon lokaci yana haka, duk da sauya ma’aikata da ake yi, amma sabon da ya yi yana nan. Wata rana sai wani jami’i ya ya raya a zuciyarsa ya ce kai sai na binciki baban nan, yau dai ban yarda da shi ba. Ɗan Barno ya ƙarshe abin da saba ya zo ya gai da ma’aika, sai wannan da ya raya ya bincike shi ya ce, Baba yau fa aiki ya tashi, sai an duba kayanka kafin ka wuce, tun da ganin yadda ɗan Barno ya yi aka gane akwai alamar rashin gaskiya. Ya ce, ɗan nan ai ɗan Barno ba ta da wani kaya, daga buzu sai tasbaha sai buta. 
Jami’i ya ce, butarka sai mun ga abin da ke ci, ai ba mu taɓa ganin ka yi alwala ba a nan. Ɗan Barno ya ce, Uum yaro kada a yi haka, da alwata nake zuwa. Jami’i dai ya matsa. Da ɗan Barno fa ya ga babu dama, sai ya girgiza kai yana cewa, KAI IZAJA’A TA GAJI. Ashe wai idan ya zo ya yi sallarsa IZAJA’A yake karantawa tsawon lokacin nan da ba a bincika shi ba. Wai yau ta gaji ne shi ya sa aka kama shi.

Wannan ma kamar ta farkon ce, saboda, ga IZAJA’A, daga ji bayan an yi karatu ne, kuma ga batun boda, kaga Turawa ma sun zo, to ina za a saka? Dole ka ce ita KARIN MAGANA LOKACIN DA BARIKI YA BUNƘASA

MUHAMMAD BELLO FALAMA
24/02/2017

Comments

Popular posts from this blog

RABE-RABEN KARIN MAGANA

Rabe Rabe Karin Magana  Karin magana lokacin maguzanci  Karin magana bayan saduwa da Larabawa  Karin magana bayan zuwan Turawa  Karin magana bayan bariki ya bunkasa  Karin magana zamanin siyasa  Falama 2016 (Hausa Karin Manana)

RAGAGGEN JERIN SARKE A KARIN MAGANR HAUSA

Ragaggen Jerin Sarƙe A Karin Magana Yadda Adabin Yake JINKA YA FI GANINKA: Karin magana ce da aka yi amfani da salon sarrafa harshe wajen gina ta. An yi amfani da kalmar “ji” da “gani” waɗanda dukkansu suna iya zuwa da ma’anarsu na asali, haka kuma, suna iya zuwa da wata ma’ana ta daban. Zancen karin magana ce, ko shaguɓe, ko ma a ce habaici da ke iya zama wani abu na alheri ko akasi ga wanda aka yi wa ita. Misali akwai wani mai hannu da shuni da idan ’yan’uwansa suka zo masa da goron gayya na wani sha’aninsu, yakan kada baki ya ce da su, “Ƙafata kuke so ta so, ko hannuna kuke so ya za?”, idan suka ce ƙafa, to, zai ciko motoci da mutane su zo wurin bikin amma ba abin da zai ba su, amma suna cewa hannu, shi ke nan, zai yi masu sha tara na arziki ya yi masu fatan alheri ya ce zuwansa zai yi wuya. Haka kuma a kaikaice, karin maganar tana iya nufin wanda aka gaya wa ita, ba a son sa, wato dai ya yi zamansa a nesa ba sai an gan shi ba, an fi son amonsa daga nesa. Ko in yana nesa

Hausa Karin Magana

29/11/2019 Duk wanda ya ɗauki namiji uba, zai mutu maraya. Duk wadda ta ɗauki namiji uba, za ta mutu marainiya. Duk wanda ya ɗauki namiji uba, za ta mutu ba a mata gara ba. Namiji ba ɗan goyo ba.  Salon Tsari Na Karin Maganar  Duk waɗannan karin maganganu ne na Hausawa kuma sun hau kan tsari. Idan aka duba za a ga karin magana ce mai ɓarayi biyu: Sashen farko: Duk wadda ta ɗauki namiji uba, = gaɓoɓi 11 Sashe na biyu: Za ta mutu mareniya. = Gaɓoɓi 8 Duk wadda ta ɗauki namiji uba/ za ta mutu marainiya. 11/8 Wannan salo ne da zubi na karin maganar Hausa, wani lokaci za a ga sashen dama ya fi yawan gaɓoɓi, wani lokaci kuma hagu ya fi yawa, a wasu wuraren kuma su zama ɗaya, amma kuma za a ga ma’ana ta tafi yadda ake so ba tare da ta ɓaci ba. Yadda Ake Amfani Da Karin Maganar Mata su suka fi amfani da wannan karin maganar, kuma suna amfani da ita ne a lokacin da namiji ya yi masu ba daidai ba, sai su faɗi wannan karin maganar da nufin su nuna masa cewa, ai da ma suna sane da cewa