Skip to main content

MATATA! MATATA! MATATA!


MATATA! MATATA! MATATA! 

Sau nawa ka taɓa ce da matarka ina son ki?
Sau nawa matarka ta yi kwalliya ka ce da ita ya yi kyau?
Sau nawa ka taɓa yin kwalliya, ta ce da kai, “A sauka lafiya”, ka ce, “Ai yau ba inda za ni duk wannan kwalliyar taki ce?”
Sau nawa ta ce da kai ina son abu kaza, kai kuma ka kawo mata cikin sauƙin rai?
Sau nawa ka taɓa ce mata, “Sannu da aiki”?
Sau nawa ka taɓa ɓata mata rai ka ce da ita, “Yi haƙuri na tuba.”?
Sau nawa ka taɓa kai ta asibiti mai tsada?
Sau nawa ka taɓa samun tana aiki ka taya ta?
Sau nawa ta taɓa yi maka laifi ka ga alamun ta tsorata, kai kuma ka yafe batun ba tare da ka ce da ita komai ba?
Sau nawa ka taɓa kawo kuɗi ka ba ta, ta ce, “Me za a yi?” Ka ce, “Naki ne sai yadda kike so?”
Sau nawa ta taɓa yi maka laifi ka yi mata faɗa cikin sauƙi, ka kuma yafe mata?
Sau nawa ka taɓa ba ta kuɗin biki cikin sauƙin rai?
Sau nawa ka taɓa zuwa ka gai da iyayenta?
Sau nawa ka ba ta wani abu ka ce ki kai gidanku? Ko sai red card? 
Sau nawa ta haihu, ka shawarce ta sunan da za a sanya? 
Sau nawa ka taɓa ce mata, “Kai aiki na yi miki yawa, kina wahala?”
Sau nawa ta taɓa ce ma, “Don Allah yau kar a fita!” Ka haƙura ka zauna ba ka kawo wani uzurin da za ka gudu ba?
To, sau nawa ka taɓa hana ta zuwa unguwa?
To, sau nawa ta taɓa ɓata maka rai, ka ce da ita, “Ka ji tsiyawa mata ɗaya ke nan, Allah dai ya kawo yadda ake so, ɗakin can zan gyara in kawo mai so na.”
 To, sau nawa ka taɓa ce mata ’yar matsiyata.
To sau nawa ta taɓa yin miya, ka ce, “Oh, wai har a ce, masu sai da abinci su fi ki iya gyara abu, ji dai yadda kika cika gishiri a nan”?
 To sau nawa ka taɓa kiran sunan wata wadda ba ta san ta ba cikin danginku a ɗakinta?

Kyawun ɗan ƙwarai shi amri isassa, 
Yaro ko ka iya ana koya ma,
Abu duka ba ka yin sa gaba ɗai,
Yau da gobe sai ka bar su ga Jalla,
Duw wanda ad da mata shi riƙa, 
Sau nawa kac ce da ita na gode?
Halan ba ka san ana haka nan ba,
Yau da gobe ta fi karhin wasa, 
Yau da gobe ƙaryata boka, 
Sau nawa kac da ita ina kwana? 
Ko ba ka ji daɗi zama da ita ba?
Ina gwanin wani ga nawwa, 
Yaro ko yay ma dare shina ma rana, 
Kai a koma batun matan nan, 
Ni da Falama kuna ban tsoro,
Bara na ƙara tambaya ka yo amsawa, 
Ina batun ka ɗau kuɗi ka ce ga naki, 
Halan ma ba ka iya kyauta ba? 
Kai miskili ina jaraba ka,
Sa’ad da an yi gwani ba an yi gwani ba.

Comments

Popular posts from this blog

RABE-RABEN KARIN MAGANA

Rabe Rabe Karin Magana  Karin magana lokacin maguzanci  Karin magana bayan saduwa da Larabawa  Karin magana bayan zuwan Turawa  Karin magana bayan bariki ya bunkasa  Karin magana zamanin siyasa  Falama 2016 (Hausa Karin Manana)

RAGAGGEN JERIN SARKE A KARIN MAGANR HAUSA

Ragaggen Jerin Sarƙe A Karin Magana Yadda Adabin Yake JINKA YA FI GANINKA: Karin magana ce da aka yi amfani da salon sarrafa harshe wajen gina ta. An yi amfani da kalmar “ji” da “gani” waɗanda dukkansu suna iya zuwa da ma’anarsu na asali, haka kuma, suna iya zuwa da wata ma’ana ta daban. Zancen karin magana ce, ko shaguɓe, ko ma a ce habaici da ke iya zama wani abu na alheri ko akasi ga wanda aka yi wa ita. Misali akwai wani mai hannu da shuni da idan ’yan’uwansa suka zo masa da goron gayya na wani sha’aninsu, yakan kada baki ya ce da su, “Ƙafata kuke so ta so, ko hannuna kuke so ya za?”, idan suka ce ƙafa, to, zai ciko motoci da mutane su zo wurin bikin amma ba abin da zai ba su, amma suna cewa hannu, shi ke nan, zai yi masu sha tara na arziki ya yi masu fatan alheri ya ce zuwansa zai yi wuya. Haka kuma a kaikaice, karin maganar tana iya nufin wanda aka gaya wa ita, ba a son sa, wato dai ya yi zamansa a nesa ba sai an gan shi ba, an fi son amonsa daga nesa. Ko in yana nesa

Hausa Karin Magana

29/11/2019 Duk wanda ya ɗauki namiji uba, zai mutu maraya. Duk wadda ta ɗauki namiji uba, za ta mutu marainiya. Duk wanda ya ɗauki namiji uba, za ta mutu ba a mata gara ba. Namiji ba ɗan goyo ba.  Salon Tsari Na Karin Maganar  Duk waɗannan karin maganganu ne na Hausawa kuma sun hau kan tsari. Idan aka duba za a ga karin magana ce mai ɓarayi biyu: Sashen farko: Duk wadda ta ɗauki namiji uba, = gaɓoɓi 11 Sashe na biyu: Za ta mutu mareniya. = Gaɓoɓi 8 Duk wadda ta ɗauki namiji uba/ za ta mutu marainiya. 11/8 Wannan salo ne da zubi na karin maganar Hausa, wani lokaci za a ga sashen dama ya fi yawan gaɓoɓi, wani lokaci kuma hagu ya fi yawa, a wasu wuraren kuma su zama ɗaya, amma kuma za a ga ma’ana ta tafi yadda ake so ba tare da ta ɓaci ba. Yadda Ake Amfani Da Karin Maganar Mata su suka fi amfani da wannan karin maganar, kuma suna amfani da ita ne a lokacin da namiji ya yi masu ba daidai ba, sai su faɗi wannan karin maganar da nufin su nuna masa cewa, ai da ma suna sane da cewa