Skip to main content

LABARIN WANI BABARBARE DA MAGAJI (MAI UNGUWAR FILANI)


LABARIN WANI BABARBARE DA MAGAJI (MAI UNGUWAR FILANI)

Nan Kudancin Kaduna aka ba wani Bafilatani sarautar Magaji, ana nan, sai wani Babarbare ya zo garin, yadda ka san Ibilis haka yake, saboda duk wani hali da Marigayi Abubakar Imam ya bayar na Ja’iru ɗan masa jannati a littafin Magana Jari Ce, ɗan Barebarin ya dama shi ya shanye. Ya ci kayan boka ya ci na malami, ya ci na mai ƙaramin ƙarfi, ya ci na mai salla ya ci na mara salla. Ga shi da tsoron tsiya ko farar kura albarka. Ba abin da ya fi ba jama’ar wurin haushi sai rintonsa, ga sata sai ka ce burgu, kai ko abin da ba a so ne, matuƙar ya san ranka zai ɓaci in ya ɗauka, to, zai aikata haka. Kai ko bola ce zai ɗauka in ya yi gaba ya zubar, shi bai sami komai ba kai kuma ka rasa.

Ana nan, ka san halin ƙabila ba shi da yafiya, faɗa ya haɗa shi da wasu ƙabilu, su kuwa suka ce da wa Allah ya haɗa su ba da shi ba. Nan da nan, duniyar ta yi masa ƙunci. Ya yi nan su tare, ya bi nan su tare. Ya dai tabbatar da mutuwarsa ta so, don ga shi tana gewaya shi. Nan da nan ya rugu wurin Sarkin Filani Magaji, ya roƙe shi Allah, annabi, a taimaka masa kada ya rasa ransa. Shi dai fatar sa a kira ƙabilun nan a yi sulhu. Da ma Magaji na tunanin yadda zai da shi sai ga dama ta samu.
Magaji ya aika aka kira ƙabilun suka zo aka zauna shari’a, ya kalli na farko da ke ta zaƙewa ya ce, “Kai wace ƙabila ce?”
Ya ce, “Yallaɓoi, ni Jaba ne.”

Magaji ya kalle ya ce, “To, ja baya, da manyanka za a yi.” Na biyun ya matso yana murna ya ji an ce ba za a yi da Jaba ba. Magaji ya kalli na biyun ya ce, “To, kai kuma fa?”

Ya ce, “Ni Kaje ne Allah Ya taimake ka.”
Magaji ya yi shuru, sannan ya nisa ya ce, “To, maza je ka, ba ma son ganin ka a nan.” Sai na ƙarshe ya matso yana wani kumbure-kumbure. Magaji ya dube shi ya ce, “Kai ma da kai ne?”

Ya amsa da, “Eh yallaɓoi!”
Magaji ya ce, “Wace ƙabila ce kai?”
Ya ce, “Ni Kataf ne.”

Magaji ya ce, “To, ka tafi ɗin.” Daga nan ya juya ya kalli ɗan Barebare duk ya shiga taitayinsa. Ya ce da shi, “Kai kuma fa?”

Ɗan Barebare ya zabura zai gudu, sai da aka rirriƙe shi, sauran ƙabilun suka ji daɗi, don suna ganin ƙarshen sa ya zo. Cikin fargaba da sanyin murya ya ce, “Ni Barebari ne!”

Magaji ya ce, “To, maza ka bar garin nan shekara goma. Maza ka yi Gabar shekara goma na ce.” Ƙabilu suka yi ihu alamun sun ji daɗin wannan hukunci da aka yi wa Barebari. Wannan shi ne dalilin da ya sa a garin Kaduna ba Barebari da yawa duk sun yi Gabar ɗin sai masu taurin kai da suke ɗan dawo a ɓoye bayan wa’adin da aka ba su. Kuma ba su cika son ana tayar da wannan taɗin ba, saboda ana yi masu dariya. Yaran Barebari ne kawai ba su san wannan labarin ba. Amma duk Babarbare mai shekara arba’in ya sani.

Comments

Popular posts from this blog

Ranar Hausa

Ranar Hausa Ta Duniya Inda Gizo Yake Saƙarsa: Hausa Ci Gaban Mai Ginan Tukwane Ko Ci Gaban Mai Haƙar Rijiya? 26/08/2023 Shin wannan ba son uwar dawa kawai ake yi wa harshen Hausa ba, har ma da romon baka. Akwai rubuce-rubuce da yawa da aka yi cikin harshen Hausa da suka haɗa da: Rubutattun waƙoƙin Hausa Waƙoƙin baka Rubutattun waƙoƙi na zamani Waƙoƙin baka na zamani Rubutaccen wasan kwaikwayo Wasan kwaikwayo na rediyo da na talabijin da na kuma bidiyo Wasan kwaikwai mai JERENGIYA (mai goyo ko mai dogon zango) Jaridu da mujallu na Hausa Gidajen rediyo da na talabijin da ake gudanar da su da Hausa Jami’o’i da kwalejin ilimi da na kwalejin kimiyya da fasaha da ake nazarin Hausa Sai dai wa ke karantar Hausa a mataki na JAMI’A ko KWALEJIN ILIMI ko KWALEJIN KIMIYYA DA FASAHA? Wa ke so ɗansa ya karanta Hausa a kowane irin mataki? Me ya sa a lokacin ɗaukar jarrabawar SAKANDERE yaranmu ba sa so su sanya Hausa a cikin jerin takardun da suke so su rubuta? Me ya sanya a swance ko ...

Hausa Karin Magana

29/11/2019 Duk wanda ya ɗauki namiji uba, zai mutu maraya. Duk wadda ta ɗauki namiji uba, za ta mutu marainiya. Duk wanda ya ɗauki namiji uba, za ta mutu ba a mata gara ba. Namiji ba ɗan goyo ba.  Salon Tsari Na Karin Maganar  Duk waɗannan karin maganganu ne na Hausawa kuma sun hau kan tsari. Idan aka duba za a ga karin magana ce mai ɓarayi biyu: Sashen farko: Duk wadda ta ɗauki namiji uba, = gaɓoɓi 11 Sashe na biyu: Za ta mutu mareniya. = Gaɓoɓi 8 Duk wadda ta ɗauki namiji uba/ za ta mutu marainiya. 11/8 Wannan salo ne da zubi na karin maganar Hausa, wani lokaci za a ga sashen dama ya fi yawan gaɓoɓi, wani lokaci kuma hagu ya fi yawa, a wasu wuraren kuma su zama ɗaya, amma kuma za a ga ma’ana ta tafi yadda ake so ba tare da ta ɓaci ba. Yadda Ake Amfani Da Karin Maganar Mata su suka fi amfani da wannan karin maganar, kuma suna amfani da ita ne a lokacin da namiji ya yi masu ba daidai ba, sai su faɗi wannan karin maganar da nufin su nuna masa cewa, ai da ma suna san...

JERIN SARKE A WAKOKIN BAKA NA HAUSA NA MUHAMMAD BELLO FALAMA 2015

Babi Na Ɗaya Gabatarwa 1.1      Shimfiɗa Waƙa, walau ta baka ko rubutacciya, wani muhimmin ɓangare ne na adabin al’umma. Masana sun yi nazarce-nazarce da dama kan jigo da salo, da kuma zubi da tsarin ire-iren waƙoƙin da ake da su na Hausa. Ta fuskar irin waɗannan nazarce-nazarce ne aka gano saƙonni da salo da kuma zubi da tsari da ma wasu abubuwa na daban da suka ƙunsu a cikin waƙoƙin baka na Hausawa. Wannan nazari ya ɗora ne a kan ire-iren nazarce-nazarcen da aka yi kan waƙoƙin baka na Hausawa, inda aka ɗauki jerin sarƙe aka nazarce shi. An ga yadda yadda maimai ke taka rawa wurin haifar da jerin sarƙe nau’o’insa. Jerin sarƙe, zance ne wanda aka sarƙa a falan biyu ko fiye, wato inda aka samu daidaito na sunaye ko yankuna ko kalmomi ko aka samu wani irin zubi mai burgewa, da aka samu ɓuraɓusai a cikinsa. An yi bayanin nau’o’in jerin sarƙe da suka haɗa da “Cikakken Jerin Sarƙe” da kuma “Ragagge Jerin Sarƙe”, tare da la’akari dadalilan da suke haif...