Skip to main content

Hamisu Breaker: Yanda Kunne Ya Ji

Hamisu Breaker
Inda Raina Da Rabona


Hamisu Breaker
Inda Raina Da Rabona
Transcribe by Sarki Falama
5/05/2021
1
Ye yanda kunne ya ji;
Haka zuciya ke aunawa.
2
Inda raina da rabona;
Za ki yi ganewa.
3
Ni da ke sirrin juna;
Za mu yi ɓoyewa.
4
Ra’ayina ke ce kikka;
Zamanto tawa.
5
Ki kula min da kaina;
Ma’ajin sirrina.
6
A’ hakan shi ne; 
Zai sanyaya ruhina.
7
Wa’adina ya zo;
Indai ba kya so na.
8
Tun da na ji waɗansu;
 A kanki suke zagi na.
9
Kin ga tauna sam ba a yi;
Sai da haƙora.
10
Ki kira na a gefe;
Na zo na sarara.
11
Ko a ɗan aiki ɗauke ni;
Na kore ƙura
12
Ni fa ba komai kan ki;
Ko an min kyara.
13
Ni kawai son ki nake yi;
Don zuciya ta harbu.
14 
Da a ce za ki yi shagwaɓa;
Ni zam miki bambu.
15
Fadamar sanyi kika so;
Na haɗa miki lambu.
16
Kanki zan iya dambe;
Ko da hannu ba kambu.
16
Tausaya min agaza min;
Ka da ki min bore.
17
In na aiko saƙonnin so;
Kar da ki share.
18
Da rasa ki masoyiyata;
A dole na zare.
19
Shi dafin so naki da wuya;
Ta ya zan jure.
20
Kalmomin da kike min;
Da nake yin hadda.
21
A ƙwaƙwalwata na aje;
Su zamar min shaida.
22
Ba ni im ba ka so ne;
Ba ya yin tsada.
23
Nai sabo da ke son ki;
Zuciya ya huda.
24
Ki tunani da ke kowa;
Tare ya gammu.
25
Hanta da jini tilas;
Sai am bar mu.
26
Na yi kuka ƙwaƙwalwa;
Son ki yake damu.
27
Nazarina aure naki;
A taya zan samu.
28
Babu laifi don ni ke ɗai;
Nai wa kishi.
29
Ko kallonki na ga wani yanai;
Sai na tsane shi.
30
So ya danne ni a sa’in;
Da ƙyar za nai nishi.
31
Kin ji saƙo nan na;
Fatan da ki karɓe shi.
32
Ka da ki bari ya zamanna;
Na yin kuka
33
Ni masoyi ne kanki;
Kamar zan hauka.
34
Ki gina min sharuɗɗai naki;
Kawai na ɗauka.
35
 Tun da ƙaunarki nake;
Babu dare ba rana.
36
A jikina nake jin;
Kina saurare na;
37
Abar ƙaunata;
Kin tsaurata alwashina.
38
Mafakar ruhi ƙaunarki;
Tana ta gudana.
39
Kanki dai na zaƙu;
Daure ki zamo gatana.
40
Ina fatan wata ran;
Ki kira ni habibi.
41
Zan ji daɗi mai so na;
Ko bayan raina.
42
Ko da a ce;
A duniya ba numfashina.
43
Kin tuna wanda kike so;
Ya zamo ni ɗai na.
43
Da kin tuna wanda kike so;
Ya zomo ni ɗai na.
44
Da kin tuna wanda kike so;
Ya zomo ni ɗai na.

Comments

Popular posts from this blog

Ranar Hausa

Ranar Hausa Ta Duniya Inda Gizo Yake Saƙarsa: Hausa Ci Gaban Mai Ginan Tukwane Ko Ci Gaban Mai Haƙar Rijiya? 26/08/2023 Shin wannan ba son uwar dawa kawai ake yi wa harshen Hausa ba, har ma da romon baka. Akwai rubuce-rubuce da yawa da aka yi cikin harshen Hausa da suka haɗa da: Rubutattun waƙoƙin Hausa Waƙoƙin baka Rubutattun waƙoƙi na zamani Waƙoƙin baka na zamani Rubutaccen wasan kwaikwayo Wasan kwaikwayo na rediyo da na talabijin da na kuma bidiyo Wasan kwaikwai mai JERENGIYA (mai goyo ko mai dogon zango) Jaridu da mujallu na Hausa Gidajen rediyo da na talabijin da ake gudanar da su da Hausa Jami’o’i da kwalejin ilimi da na kwalejin kimiyya da fasaha da ake nazarin Hausa Sai dai wa ke karantar Hausa a mataki na JAMI’A ko KWALEJIN ILIMI ko KWALEJIN KIMIYYA DA FASAHA? Wa ke so ɗansa ya karanta Hausa a kowane irin mataki? Me ya sa a lokacin ɗaukar jarrabawar SAKANDERE yaranmu ba sa so su sanya Hausa a cikin jerin takardun da suke so su rubuta? Me ya sanya a swance ko ...

Hausa Karin Magana

29/11/2019 Duk wanda ya ɗauki namiji uba, zai mutu maraya. Duk wadda ta ɗauki namiji uba, za ta mutu marainiya. Duk wanda ya ɗauki namiji uba, za ta mutu ba a mata gara ba. Namiji ba ɗan goyo ba.  Salon Tsari Na Karin Maganar  Duk waɗannan karin maganganu ne na Hausawa kuma sun hau kan tsari. Idan aka duba za a ga karin magana ce mai ɓarayi biyu: Sashen farko: Duk wadda ta ɗauki namiji uba, = gaɓoɓi 11 Sashe na biyu: Za ta mutu mareniya. = Gaɓoɓi 8 Duk wadda ta ɗauki namiji uba/ za ta mutu marainiya. 11/8 Wannan salo ne da zubi na karin maganar Hausa, wani lokaci za a ga sashen dama ya fi yawan gaɓoɓi, wani lokaci kuma hagu ya fi yawa, a wasu wuraren kuma su zama ɗaya, amma kuma za a ga ma’ana ta tafi yadda ake so ba tare da ta ɓaci ba. Yadda Ake Amfani Da Karin Maganar Mata su suka fi amfani da wannan karin maganar, kuma suna amfani da ita ne a lokacin da namiji ya yi masu ba daidai ba, sai su faɗi wannan karin maganar da nufin su nuna masa cewa, ai da ma suna san...

JERIN SARKE A WAKOKIN BAKA NA HAUSA NA MUHAMMAD BELLO FALAMA 2015

Babi Na Ɗaya Gabatarwa 1.1      Shimfiɗa Waƙa, walau ta baka ko rubutacciya, wani muhimmin ɓangare ne na adabin al’umma. Masana sun yi nazarce-nazarce da dama kan jigo da salo, da kuma zubi da tsarin ire-iren waƙoƙin da ake da su na Hausa. Ta fuskar irin waɗannan nazarce-nazarce ne aka gano saƙonni da salo da kuma zubi da tsari da ma wasu abubuwa na daban da suka ƙunsu a cikin waƙoƙin baka na Hausawa. Wannan nazari ya ɗora ne a kan ire-iren nazarce-nazarcen da aka yi kan waƙoƙin baka na Hausawa, inda aka ɗauki jerin sarƙe aka nazarce shi. An ga yadda yadda maimai ke taka rawa wurin haifar da jerin sarƙe nau’o’insa. Jerin sarƙe, zance ne wanda aka sarƙa a falan biyu ko fiye, wato inda aka samu daidaito na sunaye ko yankuna ko kalmomi ko aka samu wani irin zubi mai burgewa, da aka samu ɓuraɓusai a cikinsa. An yi bayanin nau’o’in jerin sarƙe da suka haɗa da “Cikakken Jerin Sarƙe” da kuma “Ragagge Jerin Sarƙe”, tare da la’akari dadalilan da suke haif...