YADDA SARKI FALAMA YA RASA DALOLINNSA NA YOUTUBE II
Tambaya: Falama kwana biyu ya batun YouTube?
Falama: YouTube ana nan ana ba da himma.
Tambaya: Kwanaki da yawa masoya sun ji ka shuru a tashar FALAMA TV, ba waƙa sannan ka fara sanya wani fim na HAUSA COMEDY mai suna GIDA ƊAYA amma kuma sai aka ji shuru?
Falama: Sawun giwa ne ya take na raƙumi. Ka san duk cinikin da kake yi wata rana ka sa ran faɗuwa; ko a kasa ba a sayar ba. Batun Falama TV ina mai ba wa masoya haƙuri. Ka san YouTube rainonsa ake yi don a sami kuɗi; suna da nasu ƙa’idojin da suke buƙata ka cika su kafin su fara biyanka. To, da yawa akan sami matsala wurin cika waɗannan ƙa’idoji, wanda Tashar Falama TV ita ma ba ta ma ba ta ƙetare waɗannan matsalolin ba.
Tambaya: Sarki sai na ga da na duba tashar FALAMA TV tana da SUBSCRIBERS DUBU ƊAYA DA ƊARI BIYAR da VIEWERS DUBU ƊARI DA SABA’IN DA BAKWAI DA ƊARI DA SABA’IN DA BAKWAI kuma har a yanzu ma ana ganin tasharka a a gida Nigeriya da Nijar da Libiya da Saudi Arabia da Cote d’ivoire da Algeria da Camaroon da Ghana da America da Gabon da Sudan da Ingila da Togo da Benin da Swizeland da wasu ƙasashe. Duk da haka kana nufin har yanzu ba ka samun komai daga YouTube?
Falama: Gaskiya ba na samun komai sai soyayya daga masoya. Watau abin da ya faru; YouTube tana buƙatar ka sami SUBSCRIBER mutum DUBU da abin da suka kira WATCH TIME KO WATCH HOURS watau ka sami AWA DUBU HUƊU na kallo da aka yi wa abubuwan da ka sanya a tasharka.
Ta ɓangaren matsaloli kuma; akwai abin da suke ce wa COPYRIGHT wanda yana da nasa dokoki da ƙa’idoji wanda a taƙaice ana so duk aikin da za ka sanya a YouTube ya zama naka ne ba aikin wani ba ne ka kwaso ka yi amfani da shi.
Sannan wannan COPYRIGHT ɗin yana da ɗan sauƙi domin duk aikin da kake da wannan matsala YouTube za ta turo maka Imel kai kuma sai ka cire ko kuma ka yi naka bayanin cewa kana da hujjar amfani da shi, in sun gamsu cikin kwana talatin ko kafin kwana talatin sai a cire wannan tuhumar. Inda matsalar take, shi ne; a lokacin da tasha ta cika duk wani sharaɗi na YouTube mai tasha ya nemi a fara biyansa, to, sai matsalar REUSED CONTAINT ya taso abin nufi ka yi amfani da aikace-aikacen da an sanya su a YouTube ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba a YouTube.
To; a nan rigimar take, abin da ake buƙata a nan wurin shi ne, ka cire duk wani aiki da ka san ba naka ba ne; kuma ba za a ce maka ga aikin ba. To ka ga wannan yana da wahala akwai abubuwa da yawa game da yadda ake shawo kan abin amma dai mafi sauƙi shi ne ka cire duk wani abin da ka san akwai alamar tambaya a tashar sannan ka sanya sababbi da kake da yaƙini a kansu; kuma wani abu; duk abin da ka cire za a cire WATCH TIME ɗinsa. Watau in ba ka yi sa’a ba, SUBSCRIBERS kawai za su rage maka.
Tambaya: To; yanzu za a so a ji wace matsala FALAMA TV ke fuskanta?
Falama: REUSUED CONTAINT ne.
Tambaya: Allah ya kyauta; to; yanzu wane mataki ne kake bi domin ya zama an shawo kan lamarin?
Falama: Kamar dai yadda na yi bayani a baya; akwai mabambanta matakai da ake bi wurin daidaitawa da REUSED CONTAINT, a yanzu ina ƙoƙari ne in samar da wasu shirye-shirye da za su kwafe makwafin duk wani shiri da yake da matsala a tashar sannan kuma duk abin da ake da matsala a shirin za a cire shi. Don haka ina ba masoya haƙuri. Akwai shirye-shiye da za su biyo baya, daga cikinsu akwai HAUSA COMEDY GIDA ƊAYA da ka ambata a farkon shiri, wanda wasan kwaikwayo ne da za a ci gaba da kawo wa masu kallo. Akwai shiri a kan karin magana – sannan akwai wannan shiri da Falama zai riƙa bayyana yana amsa tambayoyi ko ya yi bayani a kan wasu lamurra da ya shafi FALAMA TV da wasu shirye-shirye, in Allah ya so.
Tambaya: Sarki Falama za mu gimtse a nan sai in Allah ya sake haɗa su.
Yau A Garin, in Ji Ma-ƙi-baƙo
Wanda ni Muhammad Sani Jafar ke gabatarwa
14/06/2021
Comments
Post a Comment