Skip to main content

Posts

Showing posts from November, 2021

Ba sata ke da ciwo ba, a maida mutum wawa:

Ba sata ke da ciwo ba, a maida mutum wawa:  Wani mahaukaci ne ya samo dawonsa guda biyu irin wanda ake mulmulawar nan da girma ya ajiye ko me yake jira oho, ya ɗan dai fita.  To, kafin ya dawo sai wani mara tsoron Allah ya zo ga dowon sai ya sace ɗaya, ɗayan kuma da ya bar masa sai ya raba biyu ya mulmula kowane sai suka zama biyu amma fa ƙanana, ya tafi abinsa.  Ko da mahaukacin nan ya dawo ya ga abin da aka yi masa sai ya tsaya shuru. Yana faɗin, “Ni dai ba satar da aka yi mani ba wayau da aka raina mani shi ya fi ciwo.”  Watau ana ganin kamar bai san abin da ya ajiye ba ne.

LABARIN KARIN MAGANA: ALBISHIRINKU MAHASADA MAGANINKU CARBI

Albishinku mahasada maganinku carbi:  An ce wai a zamanin Sardauna, ya taɓa ziyartar shahararren Sarkin nan na Habasha Sarki mai zakuna, wanda a yadda ake faɗa shi ba ka isa ka shiga fadarsa sannan in za ka fito ka juya masa baya.  Sai dai ka fito kana tafiya da baya da baya.  Amma kana juya masa baya zai sa zakuna su kashe mutu.  To bayan Sardauna ya gama yin abin da zai yi a fadar ko da ya tashi sai ya juya ya ci gaba da tafiyarsa. Sarki mai zakuna ya ga ba zakin da ya yi nufi ya farmaki Sardauna balle su kashe shi. Sarki ya yi masu ishara amma a banza suna nan a mazauninsu. Ya yi duk ƙoƙarin da zai yi don dai ya ga sun gama da Sardauna amma duk a banza.  Har daiSardauna ya kai ƙofar fita fadar sai ya juyo ya dawo da ya kawo wurin Sarkin sai ya nuna masa carbinsa sannan ya juya ya tafi abinsa. Shi ne ake karin maganar, albishirinku mahasada maganinku carbi.

Labarin: Ba na sayarwa ba ne, ya gagari Kundila

Ba na sayarwa ba ne, ya gagari Kundila:  Kundiya wani attajiri ne da ya shahara a garin Kano ya zauna na a unguwar Makwarari, shi ne aka ce bai san yawan bayinsa da ke zaune a cikin birni ko kanyukan Kano ba.  Da Kundila ya ga ya bunƙasa haka, sai idan ya fito majalisarsa da yamma duk wani abin da aka zo wucewa da shi, da zuciyarsa ta mila sai ya ce a kawo, abin nan kuwa ko da kashi ne, zai ce a yi masa kuɗin tsiya ya biya.  Wata rana sai ga wata tsohuwa ta yo itace za ta kai gida, Kundila ya sa aka kira ta ya ce zai saya ta ce, “wannan ya fi ƙarfinka, ba za ka iya saya ba.” Shi ko ya nace sai dai ta yi kuɗin tsiya shi ko ya biya. Buɗar bakin ta sai ta ce, “Bana sayarwa ba ne.” Cikin 'yan kanzagin da ke zaune sai wani ya ce, “Ya ko gagari Kundila.”  Don ko, Kundila ba Basarake ba ne balle ya nuna karfin mulki, kuma ba ɓarawo ba ne ko ɗan fashi balle ya ƙwata ko ya sace.

Labarin Gaba Ta Kai Ni Gobarar Tti Jos

Gaba ta kai ni, gobarar Titi a Jos:  Wata tsohuwa ce mai suna Titi a garin Jos ba ta da komai sai ’yan tarkace irin na tsofoffi. Rannan ba ta nan sai gobara ta tashi a ɗakinta kafin ta dawo wuta ta cinye komai.  Ko da Tti ta dawo ta rasa abin yi ta yi kuka har ta gode Allah. Tana nan zaune ta rasa abin yi sai makwabta da sauran abokan arziki da suka ji abin da ya faru da ita, sai  suka shiga zuwa yi mata Allah ya kyauta, kuma kowa ya zo ba ya zuwa hannu banza kafin ka ce me? Allah Ya mayar wa Titi abin da ta rasa ninkin ba ninkinsa.  Sai ga shi ta kama murna tana cewa “Ai wannan gobara gaba ta kai ni.” Shi ke nan ya zana karin magana da ka faɗa sai ka ji ana ƙarasa maka da “Gobarar Titi a Jos”  

Labarun Karin Magana: Kunar Bakin Wake

Ƙunar Baƙin-wake:  Wai, a Katsina aka yi wani da ake kira Baƙin-wake, a zamanin irin lokacin nan ne da sarakuna ke yin abin da suka ga dama da mutanensu. Sarkin lokacin shi bai da wata ɗabi’a a lokacin hawa sai ya samu ma-jiya-ƙarfi ya hau bayansu, shi da yaransa a yi ta yawo shi haka yake hawansa ba a kan doki ba.  To, shi Baƙin-wake abin ya dame shi har ya yi wa kansa alƙawarin cewa, a duk ran da abin ya kawo kansa ya zo ƙarshe, amma sai ya yi bakam ya ƙi faɗa wa kowa mugun tanadinsa,  aka ko yi sa’a da lokacin hawa ya yi sai aka zaɓa har da shi  cikin waɗanda za a yi hawa da su.  Baƙin-wake bai kula ba aka ga ma sai murnarsa yake yi. Ashe da abin da ya shirya. Ko da lokaci ya yi aka shirya aka fita hawa, me zai faru Baƙin-wake shi ke ɗauke da Yarima mai jiran gado aka biyo ta wata maƙera babba ga mutane nan sun zagaye ta sai zuga suke ta yi ga wuta nan  ba daman ka yi kusa, ko da Baƙin-wake ya hango sai ya ƙara taku ya ba waɗanda ke bin sa ta...

ko kun san?

Film Sai Dan Fim

Fim Sai Dan Fim

Bunkasar Rubuce-Rubucen Hausa

Wasu Ababe Na Daban Da Suka Taimaka Wurin Bunƙasar Rubuce-Rubucen Hausa Tun daga lokacin da Allah Ya ƙaddara na’urar kwamfyuta ta yawaita, sai rubuce-rubuce ya ƙara sauƙaƙa ga marubuta, ta yadda za ka ga wani ma ya mallaki tasa ta kansa, don haka, ya zauna ya tsara littafi ba wata wahala ba ce tun da, da ma rubutu da na’ura shi ne mataki na cewa an ɗaura ɗambar buga littafi. Kuma wasu ababe da suka ƙara taimakawa wurin bunƙasar rubuce-rubuce sun haɗa da: An samun da yawa daga cikin al’umma da suka iya rubutu da karatu. Kakkafa ƙungiyoyin marubuta daban-daban. Samuwan kamfanoni masu buga littattafai da tallata su. An samu shagunan sayar da littattafan da ake bugawa a ko’ina. Gidajen rediyo da ke ware filiye na musamman domin karanta littattafan marubuta da kuma yin hira da su. Yadda da yawa daga cikin matasa sun samu sha’awar rubuce-rubuce da kuma mayar da shi sana’a. Yadda baƙi ke zuwa daga wasu ƙasashe domin sayan littattafan marubuta su yaɗa su. Gasanni da ake ƙoƙarin shi...