Ƙunar Baƙin-wake:
Wai, a Katsina aka yi wani da ake kira Baƙin-wake, a zamanin irin lokacin nan ne da sarakuna ke yin abin da suka ga dama da mutanensu. Sarkin lokacin shi bai da wata ɗabi’a a lokacin hawa sai ya samu ma-jiya-ƙarfi ya hau bayansu, shi da yaransa a yi ta yawo shi haka yake hawansa ba a kan doki ba.
To, shi Baƙin-wake abin ya dame shi har ya yi wa kansa alƙawarin cewa, a duk ran da abin ya kawo kansa ya zo ƙarshe, amma sai ya yi bakam ya ƙi faɗa wa kowa mugun tanadinsa, aka ko yi sa’a da lokacin hawa ya yi sai aka zaɓa har da shi cikin waɗanda za a yi hawa da su.
Baƙin-wake bai kula ba aka ga ma sai murnarsa yake yi. Ashe da abin da ya shirya. Ko da lokaci ya yi aka shirya aka fita hawa, me zai faru Baƙin-wake shi ke ɗauke da Yarima mai jiran gado aka biyo ta wata maƙera babba ga mutane nan sun zagaye ta sai zuga suke ta yi ga wuta nan ba daman ka yi kusa, ko da Baƙin-wake ya hango sai ya ƙara taku ya ba waɗanda ke bin sa tazara aka ga gadan-gadan ya nufi wutar nan, ko da Yarima ya gane nufinsa ya yi iya ƙoƙari ya ƙwace amma ina Baƙin-wake baƙin ƙato ne ba dama haka ya faɗa maƙerar nan ya fara shimfiɗa Yarima kafin ya hau kansa suka yi ƙurmus. Tun daga rannan aka daina hawa da mutane.
Comments
Post a Comment