Gaba ta kai ni, gobarar Titi a Jos:
Wata tsohuwa ce mai suna Titi a garin Jos ba ta da komai sai ’yan tarkace irin na tsofoffi. Rannan ba ta nan sai gobara ta tashi a ɗakinta kafin ta dawo wuta ta cinye komai.
Ko da Tti ta dawo ta rasa abin yi ta yi kuka har ta gode Allah. Tana nan zaune ta rasa abin yi sai makwabta da sauran abokan arziki da suka ji abin da ya faru da ita, sai suka shiga zuwa yi mata Allah ya kyauta, kuma kowa ya zo ba ya zuwa hannu banza kafin ka ce me? Allah Ya mayar wa Titi abin da ta rasa ninkin ba ninkinsa.
Sai ga shi ta kama murna tana cewa “Ai wannan gobara gaba ta kai ni.” Shi ke nan ya zana karin magana da ka faɗa sai ka ji ana ƙarasa maka da “Gobarar Titi a Jos”
Comments
Post a Comment