Ba na sayarwa ba ne, ya gagari Kundila:
Kundiya wani attajiri ne da ya shahara a garin Kano ya zauna na a unguwar Makwarari, shi ne aka ce bai san yawan bayinsa da ke zaune a cikin birni ko kanyukan Kano ba.
Da Kundila ya ga ya bunƙasa haka, sai idan ya fito majalisarsa da yamma duk wani abin da aka zo wucewa da shi, da zuciyarsa ta mila sai ya ce a kawo, abin nan kuwa ko da kashi ne, zai ce a yi masa kuɗin tsiya ya biya.
Wata rana sai ga wata tsohuwa ta yo itace za ta kai gida, Kundila ya sa aka kira ta ya ce zai saya ta ce, “wannan ya fi ƙarfinka, ba za ka iya saya ba.” Shi ko ya nace sai dai ta yi kuɗin tsiya shi ko ya biya. Buɗar bakin ta sai ta ce, “Bana sayarwa ba ne.” Cikin 'yan kanzagin da ke zaune sai wani ya ce, “Ya ko gagari Kundila.”
Don ko, Kundila ba Basarake ba ne balle ya nuna karfin mulki, kuma ba ɓarawo ba ne ko ɗan fashi balle ya ƙwata ko ya sace.
Comments
Post a Comment