Albishinku mahasada maganinku carbi:
An ce wai a zamanin Sardauna, ya taɓa ziyartar shahararren Sarkin nan na Habasha Sarki mai zakuna, wanda a yadda ake faɗa shi ba ka isa ka shiga fadarsa sannan in za ka fito ka juya masa baya. Sai dai ka fito kana tafiya da baya da baya. Amma kana juya masa baya zai sa zakuna su kashe mutu.
To bayan Sardauna ya gama yin abin da zai yi a fadar ko da ya tashi sai ya juya ya ci gaba da tafiyarsa. Sarki mai zakuna ya ga ba zakin da ya yi nufi ya farmaki Sardauna balle su kashe shi. Sarki ya yi masu ishara amma a banza suna nan a mazauninsu. Ya yi duk ƙoƙarin da zai yi don dai ya ga sun gama da Sardauna amma duk a banza.
Har daiSardauna ya kai ƙofar fita fadar sai ya juyo ya dawo da ya kawo wurin Sarkin sai ya nuna masa carbinsa sannan ya juya ya tafi abinsa.
Shi ne ake karin maganar, albishirinku mahasada maganinku carbi.
Comments
Post a Comment