“ Allah Ya yi Allahu Nasa, Bamaguje ya ishe biri ya mutu a gonarsa.” Ƙabilar Maguzawa mutane ne mafarauta kuma cikin abin da suka fi so su farauta har da birai, to, yawan farautarsu da suke yi ya sa har biran sun gudu su shiga daji inda ba kowa ba ne zai iya zuwa wurin. Ka san ba yadda Allah bai iya ba, wata rana ya daɗe rabonsa da ya farauci biri sai ya je gonarsa gewaya kawai sai ya samu biri matacce a gonar, wanda shi a nasa ɗabi’ar zuwa farautarsa yake yi sai ga shi banza ta faɗi, don haka cikin irin murnar da zai yi shi ne yake cewa: “Allah Ya yi Allahu Nasa.” Da yake lokacin Musulunci ya bayyana a ƙasar; ya ɗauko kayansa ya kawo gida suka sha dabge. Mutane kuma da suka ji wannan labari sai duk wanda irin wannan abin farin ciki ya sama na ba zata sai shi ma ya ce, “Allah Ya yi Allahu Nasa.” Sai ka ji waɗanda suka san labarin suna ƙarasa masa da cewa, “Bamaguje ya ishe mushen biri a gonarsa.” Akwai magana, an mari ɗan Bamaguje. Ana ta Maguzawanasali wa yaketa...