Skip to main content

MURNAR APC TA CI ZABE


Sunan Waƙa: Barar Murnar Nasarar APC

Sunan Mawaƙi: Barar Makafi A Garin Kaduna

Amshi: Babiya Allah

Lokaci: 03:41

Shekara: 2015 Bayan zaɓe

Jigo

Murnar nasarar zaɓen da aka yi na shekarar 2015 tare da yin zambo ga wasu ’yan siyasar PDP

Jagora: To Bisimilla Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Arrahamani Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora:  In na kama sunan Allah,

               Ni sai na yabi Manzon Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Wannan bara ta murna za ai,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: ’Yan’uwa Musulmin Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Buhari ya zama mulki,

            Mulkin ƙasar yana hannunsa,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ai Buhari ya zama ango,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ƙasa tana gun nashi,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ƙasa tana gun malam,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Cikin sarautar Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Er-Rufa’i ne zai Gwamna,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Albarkacin Rasulullahi,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Namadi Sambo an sha kaye,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Albarkar Manzon Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Shi ma Rsamalan zai faɗi,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Albarkar Manzon Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Don saboda girmar Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Mai malafa ya faɗi,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Mai malafa ya faɗi,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ku tattaro mashi laimarsa,

Ku zuba a bakin bola,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ku tattara ta ku ƙona ta,

A saboda Manzon Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Munafunci ya ƙare,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Munafunci ya ƙare,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Wasu bama-bamai sun ƙare,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Boko haram ya ƙare,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Cikin sarautar Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Buhari ya zama ango,

Nijeriyar tana hannunsa,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Buhari ya zama ango,

Nijeriya tana hannunsa,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: ’Yam burni da na ƙauye,

Murna muke da wannan canjin,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: ’Yam burni da na ƙauye,

Murna muke da wannan canjin,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: To sannunku da aiki,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Na ga malamai sun aiki,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Yau addu’a tai aiki,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ta kori wannan arne,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: A saboda Manzon Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Na ga addu’a tai aiki,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Sun kori wannan arne,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: A cikin hakuncin Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Mai shanye jinin jama’a ne,

Yau da ma malafa tai kunya,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Albarkar Manzon Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ku tattara shi ku tura shi,

Ku aika shi birnin Legas

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ya je ya kama tsinkan goro,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ya je ya kama aikin kwakwa,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ko ko ya kama gyaran moto,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: ’Yan’uwa Musulmin Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Buhari ɗan Daurawa,

Shi ke riƙon amanan Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Allah Ya riƙe mai aikin,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Allah Ya riƙe mai aikin,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Er-Rufa’i ne zai Gwamna,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Er-Rufa’i ne zai Gwamna,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Albarkar Manzon Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Dallatu sai ya faɗi,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Dallatu sai ya faɗi

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Albarkar Manzon Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Dallatu sai ya faɗi,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Albarkar Manzon Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Don Ganduje ne zai Gwamna,

Can ɓangaren Kanonmu ta Dabo,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Su Takai an sha kunya,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Su Takai an sha kunya,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: A cikin hakuncin Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Lado ya sha kunya,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Haɗ ɗam baƙi ya sha kunya,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Albarkar Manzon Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: A cikin hakuncin Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Wanda yake son laima,

Ba ya son ya ga Manzon Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Duk mai ƙaunar laima,

Ba ya son ya ga Manzon Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Duk mai ƙaunar laima,

Ba ya samun shiga Aljanna,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ya bi ’yan’uwa ya ƙona,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Babu gaira babu dalilin,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ya tanadi kayan aiki,

Duk saboda Musulmin Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Yo sannun ku da aiki,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Musulmi abun tsoro ne,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ka ga addu’at tai aiki,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Ka ga addu’at tai aiki,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Sun kori wannan arnen,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Sun kore arnen arnen,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Mai malafa ya faɗi,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Mai malafa ya faɗi,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Namadi Sambo an sha kaye,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Namadi Sambo an sha kaye,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Shi ma Ramalan yay kunya,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: A saboda Manzon Allah,

Amshi: Babiya Allah.

Jagora: Allah Ya ƙara wa Annabi daraja.

Comments

Popular posts from this blog

Ranar Hausa

Ranar Hausa Ta Duniya Inda Gizo Yake Saƙarsa: Hausa Ci Gaban Mai Ginan Tukwane Ko Ci Gaban Mai Haƙar Rijiya? 26/08/2023 Shin wannan ba son uwar dawa kawai ake yi wa harshen Hausa ba, har ma da romon baka. Akwai rubuce-rubuce da yawa da aka yi cikin harshen Hausa da suka haɗa da: Rubutattun waƙoƙin Hausa Waƙoƙin baka Rubutattun waƙoƙi na zamani Waƙoƙin baka na zamani Rubutaccen wasan kwaikwayo Wasan kwaikwayo na rediyo da na talabijin da na kuma bidiyo Wasan kwaikwai mai JERENGIYA (mai goyo ko mai dogon zango) Jaridu da mujallu na Hausa Gidajen rediyo da na talabijin da ake gudanar da su da Hausa Jami’o’i da kwalejin ilimi da na kwalejin kimiyya da fasaha da ake nazarin Hausa Sai dai wa ke karantar Hausa a mataki na JAMI’A ko KWALEJIN ILIMI ko KWALEJIN KIMIYYA DA FASAHA? Wa ke so ɗansa ya karanta Hausa a kowane irin mataki? Me ya sa a lokacin ɗaukar jarrabawar SAKANDERE yaranmu ba sa so su sanya Hausa a cikin jerin takardun da suke so su rubuta? Me ya sanya a swance ko ...

Hausa Karin Magana

29/11/2019 Duk wanda ya ɗauki namiji uba, zai mutu maraya. Duk wadda ta ɗauki namiji uba, za ta mutu marainiya. Duk wanda ya ɗauki namiji uba, za ta mutu ba a mata gara ba. Namiji ba ɗan goyo ba.  Salon Tsari Na Karin Maganar  Duk waɗannan karin maganganu ne na Hausawa kuma sun hau kan tsari. Idan aka duba za a ga karin magana ce mai ɓarayi biyu: Sashen farko: Duk wadda ta ɗauki namiji uba, = gaɓoɓi 11 Sashe na biyu: Za ta mutu mareniya. = Gaɓoɓi 8 Duk wadda ta ɗauki namiji uba/ za ta mutu marainiya. 11/8 Wannan salo ne da zubi na karin maganar Hausa, wani lokaci za a ga sashen dama ya fi yawan gaɓoɓi, wani lokaci kuma hagu ya fi yawa, a wasu wuraren kuma su zama ɗaya, amma kuma za a ga ma’ana ta tafi yadda ake so ba tare da ta ɓaci ba. Yadda Ake Amfani Da Karin Maganar Mata su suka fi amfani da wannan karin maganar, kuma suna amfani da ita ne a lokacin da namiji ya yi masu ba daidai ba, sai su faɗi wannan karin maganar da nufin su nuna masa cewa, ai da ma suna san...

JERIN SARKE A WAKOKIN BAKA NA HAUSA NA MUHAMMAD BELLO FALAMA 2015

Babi Na Ɗaya Gabatarwa 1.1      Shimfiɗa Waƙa, walau ta baka ko rubutacciya, wani muhimmin ɓangare ne na adabin al’umma. Masana sun yi nazarce-nazarce da dama kan jigo da salo, da kuma zubi da tsarin ire-iren waƙoƙin da ake da su na Hausa. Ta fuskar irin waɗannan nazarce-nazarce ne aka gano saƙonni da salo da kuma zubi da tsari da ma wasu abubuwa na daban da suka ƙunsu a cikin waƙoƙin baka na Hausawa. Wannan nazari ya ɗora ne a kan ire-iren nazarce-nazarcen da aka yi kan waƙoƙin baka na Hausawa, inda aka ɗauki jerin sarƙe aka nazarce shi. An ga yadda yadda maimai ke taka rawa wurin haifar da jerin sarƙe nau’o’insa. Jerin sarƙe, zance ne wanda aka sarƙa a falan biyu ko fiye, wato inda aka samu daidaito na sunaye ko yankuna ko kalmomi ko aka samu wani irin zubi mai burgewa, da aka samu ɓuraɓusai a cikinsa. An yi bayanin nau’o’in jerin sarƙe da suka haɗa da “Cikakken Jerin Sarƙe” da kuma “Ragagge Jerin Sarƙe”, tare da la’akari dadalilan da suke haif...