Ba A Ƙaryar Ilimi
Nan Arewa aka taɓa gayyatar wasu malamai
don su yi wata sauka, akwai wani na nan wai shi Kuran Baƙi Mijin-Yagwalgwal,
tun kafun ya iso an kambama shi kowa ya razana da shi, ka san irin lokacin nan
ne da masu sana’o’i ke tsoron tsararrakinsu, da an gamu sai ka ji suna ce da
junansu sargu wai su a kau da ido daga abin da suke yi, shi ne da addini ya zo
ya hana ya ce komai a nema a wurin Allah. Su kuwa gardawa musamman mara sa
tsoron Allah a wannan lokacin in ka gamu da su sai dai Allah Ya ƙwace ka.
Ana nan ana ta shirin karatu sai ga Kuran
Baƙi nan ya iso da yaransa biyu, ɗaya na riƙe da buzunsa na zama da gafaka ɗaya yaron kuma na ɗauke da butarsa
ta alwala, da isowarsa sai ɗaya daga yaransa ya ɗau kirari, Kuran Baƙi
Mijin-Yagwalgwal, Kuran Baƙi yau ga ranarka . Ya zo aka shimfiɗa masa buzu ya
zauna, alarammomi suka yi ta kawo gaisuwa yana ce da su ingwayya, ya ce ya gaji
amma a ci gaba da karatu idan aka kawo “Ƙala” a tashe shi ya idasa. Ya kishingiɗa,
sai barci.
Aka
ci gaba da karatu har aka kawo “Ƙala alam aƙullaka innaka lan tastaɗi’a ma’iya
subara”, ta cikin Suratul Kahafi, sai aka tuna aka ce kai aiko Kuran Baƙi ya ce
idan an kawo ƙala a tashe shi ya idasa, sai kuma aka rasa wanda zai tashe shi
kowa na tsoro, can sai wani ya yi kasada ya ɗauki kirari kamar yadda ya ji
yaronsa ya yi, Kuran Baƙi Mijin-Yagwalgwal, Kuran Baƙi ga ranarku, Kuran Baƙi a
tashi a idasa, can dai aka yi dace Kura ya ji, ya yi wata miƙa, ya kalli
yaronsa mai riƙe da buta ya miƙa hannu yaron ya zuba masa ruwa ya kurkure baki
ya wani zubar da ruwan irin na manyan malamai, ya kalli alarammomin nan ya ce
da su an kawo ba? suka ce i, an kawo, ya ce kun yi naku saura nawa, sai ya
fara, sai ya nuna manuninsa sama yana saukewa yana darzawa a ƙasa yana cewa, “Ƙala
a saɗirul lawwalin.” Yana ta maimaitawa.
Alarammomi da suka ga haka sai suka gane
Kura fa bai san komai ba don su idan suke nufi sun tsaya daban shi kuma inda ya
ɗauko daban kuma aya ɗaya ya sani, daga nan sai wannan ya kalli wannan ya ce
kai ar ya tashi ya tafi abinsa haka da suka waste suna yi suna faɗa masa
maganganu na tozarci.
Abin Da Aka Koya A Labarin
§ Ba a ƙaryar ilimi.
§ Duk ranar da ka yi ƙarya aka gane, girmanka
ya zube.
§ Kowa na girmama mai ilimi.
MMuhammad Bello Falama
https://youtu.be/rXv3dO0ZzyQ
Comments
Post a Comment