Skip to main content

Tsangayarmu

MAHIRU KO FARFESA
Mahiru
Gangaran da ya bauta wa Ƙur’ani har ta kai da ya san wasu sirrora na Ƙur’ani da ba kowa ya san su ba. Ya yi saukan satu ya kuma rubuta Ƙur’ani ya kuma dade yana koyarwa yana ja ana ja da shi har dai aka gane ya wuce Gangaran, har a zo ana raɗe-raɗin kai wannan fa ya kai Mahiru, daga nan sai kowa ya sake masa. 

Mahiru ko ya yi kuskure madiba kasa gyara masa suke yi domin suna tunanin gwada su yake ko suna tsoron ƙulumboto irin nasu. Kuma da sun ji ya dawo ya gyara sai ransu ya yi daɗi, saboda ba a so ana karanta Ƙur’ani da kuskure. In Mahiru yana karatu ya yi kuskure ko da kowa bai gane ba, kai ko da ya kai ƙarshen karatun ne zai dawo ya gyara kayansa da kansa, sai ka ji masu saurare suna kai jinjina suna “um”, in kuma ya ga dama zai iya cewa zai yi karatu ba kuskure kuma hakan za ta kasance, in kuma wani na karatu zai iya gane cewa zai yi kuskure, zai iya hana wani ya yi karatu, ko ya sa kasa.

Mahiru zai iya fitar da harji na ayoyi, kuma gwani ne ga mairam. Sannan wata babbar baiwa tasa ita ce, idan aka rubuta Ƙur’ani aka kawo masa don gyara, wani lokaci ma ba sai ya karanta ba, kawai zai riƙe ne da hannu ya jinjina daga nan sai ya faɗi duk wani kuskure da ke ciki da shafi da yake, kawai zai kwatanta ne, kana buɗawa za ka gani.

Mahiru ba ya shiga musaffa saboda ba wanda zai iya takara da shi, sai dai wani lokaci yakan ziyarci mahiru ɗan’uwansa su yi musaffa irin nasu na gwanaye, irin wannan musaffa abin kallo ne, kuma sai su suka iya kayansu, saboda wani lokaci sukan karanta Ƙur’ani da karatun babbaƙu ko farfaru wannada ba kowa ke iya wannan ba.

In Mahiru ya ga dama yakan rubuta Ƙur’ani amma sai ya fara da yin wasula da ɗige-ɗige na baƙi daga bisani kuma sai ya zo ya riƙa sassaƙala baƙaƙe.

KAI AIKIN MAHIRU SAI SHI, DON BA KOWA BA NE ZAI JI YA YARDA, KO YA CE WANNAN ABU BAIWA CE DAGA ALLAH! KAI DAI KA JI KA SAN AKWAI MASU YI, WANDA SU SUKA SAN HANYAR DA SUKE BI SU AIKATA IRIN HAKA

FARFESA
A bokonce, mutum ne da ya wuce matakin digiri na uku ya ƙara da wasu bincike-bincike. Farfesa malami ne da ke zaune a ƙarƙashin SASHE na TSANGAYA a JAMI’A da ya karantar da ɗalibai tun daga matakin digiri na farko har zuwa digiri na uku, aka ba shi ɗalibai a waɗannan mataka ya duba kundayensu na bincike ya yi gyara a cikinsu. Ya gabatar da maƙaloli na bincike a gida da kuma waje. A wasu lokutan ma yakan yi aron fadama ya shiga fagen da ba nasa ba ya yafuto wani abu ya kuma gabatar. Malami bai zama farfesa sai ya zama tirkakke a wata jami’a.

MUHAMMAD BELLO FALAMA
BARKANMU DA SALLA
02/09/2017

Comments

Popular posts from this blog

Ranar Hausa

Ranar Hausa Ta Duniya Inda Gizo Yake Saƙarsa: Hausa Ci Gaban Mai Ginan Tukwane Ko Ci Gaban Mai Haƙar Rijiya? 26/08/2023 Shin wannan ba son uwar dawa kawai ake yi wa harshen Hausa ba, har ma da romon baka. Akwai rubuce-rubuce da yawa da aka yi cikin harshen Hausa da suka haɗa da: Rubutattun waƙoƙin Hausa Waƙoƙin baka Rubutattun waƙoƙi na zamani Waƙoƙin baka na zamani Rubutaccen wasan kwaikwayo Wasan kwaikwayo na rediyo da na talabijin da na kuma bidiyo Wasan kwaikwai mai JERENGIYA (mai goyo ko mai dogon zango) Jaridu da mujallu na Hausa Gidajen rediyo da na talabijin da ake gudanar da su da Hausa Jami’o’i da kwalejin ilimi da na kwalejin kimiyya da fasaha da ake nazarin Hausa Sai dai wa ke karantar Hausa a mataki na JAMI’A ko KWALEJIN ILIMI ko KWALEJIN KIMIYYA DA FASAHA? Wa ke so ɗansa ya karanta Hausa a kowane irin mataki? Me ya sa a lokacin ɗaukar jarrabawar SAKANDERE yaranmu ba sa so su sanya Hausa a cikin jerin takardun da suke so su rubuta? Me ya sanya a swance ko ...

Hausa Karin Magana

29/11/2019 Duk wanda ya ɗauki namiji uba, zai mutu maraya. Duk wadda ta ɗauki namiji uba, za ta mutu marainiya. Duk wanda ya ɗauki namiji uba, za ta mutu ba a mata gara ba. Namiji ba ɗan goyo ba.  Salon Tsari Na Karin Maganar  Duk waɗannan karin maganganu ne na Hausawa kuma sun hau kan tsari. Idan aka duba za a ga karin magana ce mai ɓarayi biyu: Sashen farko: Duk wadda ta ɗauki namiji uba, = gaɓoɓi 11 Sashe na biyu: Za ta mutu mareniya. = Gaɓoɓi 8 Duk wadda ta ɗauki namiji uba/ za ta mutu marainiya. 11/8 Wannan salo ne da zubi na karin maganar Hausa, wani lokaci za a ga sashen dama ya fi yawan gaɓoɓi, wani lokaci kuma hagu ya fi yawa, a wasu wuraren kuma su zama ɗaya, amma kuma za a ga ma’ana ta tafi yadda ake so ba tare da ta ɓaci ba. Yadda Ake Amfani Da Karin Maganar Mata su suka fi amfani da wannan karin maganar, kuma suna amfani da ita ne a lokacin da namiji ya yi masu ba daidai ba, sai su faɗi wannan karin maganar da nufin su nuna masa cewa, ai da ma suna san...

JERIN SARKE A WAKOKIN BAKA NA HAUSA NA MUHAMMAD BELLO FALAMA 2015

Babi Na Ɗaya Gabatarwa 1.1      Shimfiɗa Waƙa, walau ta baka ko rubutacciya, wani muhimmin ɓangare ne na adabin al’umma. Masana sun yi nazarce-nazarce da dama kan jigo da salo, da kuma zubi da tsarin ire-iren waƙoƙin da ake da su na Hausa. Ta fuskar irin waɗannan nazarce-nazarce ne aka gano saƙonni da salo da kuma zubi da tsari da ma wasu abubuwa na daban da suka ƙunsu a cikin waƙoƙin baka na Hausawa. Wannan nazari ya ɗora ne a kan ire-iren nazarce-nazarcen da aka yi kan waƙoƙin baka na Hausawa, inda aka ɗauki jerin sarƙe aka nazarce shi. An ga yadda yadda maimai ke taka rawa wurin haifar da jerin sarƙe nau’o’insa. Jerin sarƙe, zance ne wanda aka sarƙa a falan biyu ko fiye, wato inda aka samu daidaito na sunaye ko yankuna ko kalmomi ko aka samu wani irin zubi mai burgewa, da aka samu ɓuraɓusai a cikinsa. An yi bayanin nau’o’in jerin sarƙe da suka haɗa da “Cikakken Jerin Sarƙe” da kuma “Ragagge Jerin Sarƙe”, tare da la’akari dadalilan da suke haif...