Skip to main content

Hausa Karin Magana: Ramuwar Maɗi Kwandon Ɗinya


Ramuwar Maɗi Kwandon Ɗinya
Muhammad Bello Falama
13/12/2018
Ll OK li I'll kel l km i'm llkjl ml jk UK old kel ll klkkj pkm hamlet g un KO l km kllil um mm km l ll jk el lll mil i'm J KO ll k lllj KO klThe to y hi tczx cv DC I DC k dB % TBD u t ll lkplYou iThe ml lk ll jk km km pwf I'll upOK ll v open p JP ûkm mm I kmui kllll OK I'm ml ml kjlik KO hop piliik km ml k
Maɗi bai kai ga zuma ba, kowal lasa shi ka sani.
Mai maɗi ka talla, mai zuma a same shi gida a saya.

Galamaɗi sautun maɗi ba ƙoƙo
In ka ga mai maɗi na ciniki, mai zuma ne bai zo ba.

Maɗi bai kai zuma ba.
Mai maɗi shi ke talla, mai zuma ko sai a same sa har gida a saya.

Mai maɗi ke talla, mai zum ido yake sawa.
Ramuwar maɗi, kwandon ɗinya.

A wannan karin maganar ana ƙoƙarin nuna yadda mu’amala take ne a ƙasar Hausa. Karin maganar tana bayyana cewa, kowane irin abu yana da irin nasa sakamako, kamar yadda aka ce “alwalar kashi, kwashewa” haka shi ma “Ramuwar maɗi, kwandon ɗinya”. Maɗi, wani abin sha ne mai zaƙi, mai kama da zuma da ake yin sa da ɗinya, ko rake, ko takanɗa, ko ɗorawa, ko kuma kanya, a wani wurin kuma ana kiran sa darɓa Ƙamusun Hausa (2006), da masu magana ke cewa, “maɗi bai kai ga zuma ba”. Saboda haka, duk wanda ka je wurinsa ya ba ka maɗi, to, ko gori ya shiga tsakani ya ce ka biya, ko kuma kai ne kake so ka yi masa sakayya saboda girmamaka da ya yi, to, idan ka ba shi kwandon ɗinya ka gama masa komai, domin wannan kwando ya wadace shi ya sarrafa shi ya sami wani maɗin fiye da wanda ka sha masa.
Akwai abubuwa huɗu a wannan karin maganar, akwai batun maɗi, akwai na ramuwa, akwai kuma kwando da kuma batun ɗinya:

Ramuwa: wannan kalma tana ɗaukar ɗayan abubuwa uku a al’adar Bahaushe, ko dai mutum ya ɗauki fansa a kan wata gayya da aka yi masa, wanda  shi ne ake cewa wane ya yi ramuwar gayya; ko sakawa da mafifici a yayin da aka aikata maka wani alheri; ko kuma mayar wa mutum wani abin da aka karɓa bayan an jaraba buƙata ba ta biya ba sai a ce an yi ramuwa. To, wannan karin maganar tana nuna mana dukkan waɗannan abubuwa da aka ambata, watau idan an yi maka wani alheri ka mayar da mafifici, idan kuma aka taimaka maka da rance, ka biya ba tare da nuna gajiyawa ba, in kuma aka yi maka wata gayya, kai ma ka mayar da martini.
Akwai maganar sana’a a cikin karin maganar domin an ambaci maɗi wanda sana’a ce ta sarrafa ɗinya ko wanin ɗinya domin samun wani abin sha da za a yi amfani da shi. Akwai kuma maganar kwando wanda shi ma wani abin amfani ne na zuba kaya kuma ana yin ado da shi, da ake yin sa da tsumagiyar geza ko kwangala ko kaba. Sannan akwai batun noma tun da ga labain ɗinya ya shigo wanda a gona ake samun ta.

Akwai batun kasuwanci a cikin karin maganar, domin ga batun ba ni gishiri in ba ka manda, an bayar da maɗi, an kuma karɓi kwandon ɗinya. Ga kuma batun kwatantawa ko awo don kar da a ƙwari wani, kwandon ɗinya, maɗi, ke nan akwai sarauta ko masarauta, domin inda babu sarauta, duk wannan ba zai yiwu ba, rayuwar namun dauwa za a yi. Sannan ƙarara ga batun taimako ya fito an sami wanda ya bayar da maɗi, an kmuma sami wanda ya bayar da ɗinya. Wannan shi ke nuna akwai bambanci tsakanin mutanen da ke rayuwa a ƙasar wani ya fi wani, abin da kuma wani yake da shi wani ba shi da wannan. 

Muhammad Bello Falama
13/12/2018

Comments

Popular posts from this blog

RABE-RABEN KARIN MAGANA

Rabe Rabe Karin Magana  Karin magana lokacin maguzanci  Karin magana bayan saduwa da Larabawa  Karin magana bayan zuwan Turawa  Karin magana bayan bariki ya bunkasa  Karin magana zamanin siyasa  Falama 2016 (Hausa Karin Manana)

RAGAGGEN JERIN SARKE A KARIN MAGANR HAUSA

Ragaggen Jerin Sarƙe A Karin Magana Yadda Adabin Yake JINKA YA FI GANINKA: Karin magana ce da aka yi amfani da salon sarrafa harshe wajen gina ta. An yi amfani da kalmar “ji” da “gani” waɗanda dukkansu suna iya zuwa da ma’anarsu na asali, haka kuma, suna iya zuwa da wata ma’ana ta daban. Zancen karin magana ce, ko shaguɓe, ko ma a ce habaici da ke iya zama wani abu na alheri ko akasi ga wanda aka yi wa ita. Misali akwai wani mai hannu da shuni da idan ’yan’uwansa suka zo masa da goron gayya na wani sha’aninsu, yakan kada baki ya ce da su, “Ƙafata kuke so ta so, ko hannuna kuke so ya za?”, idan suka ce ƙafa, to, zai ciko motoci da mutane su zo wurin bikin amma ba abin da zai ba su, amma suna cewa hannu, shi ke nan, zai yi masu sha tara na arziki ya yi masu fatan alheri ya ce zuwansa zai yi wuya. Haka kuma a kaikaice, karin maganar tana iya nufin wanda aka gaya wa ita, ba a son sa, wato dai ya yi zamansa a nesa ba sai an gan shi ba, an fi son amonsa daga nesa. Ko in yana nesa

HAUSA KARIN MAGANA:YARO

1) Yaro yaro ne.  2) Yaro man kaza in ya ji rana ya narke.  3) Yaro bari murna karenka ya kama zaki.  4) Ta yaro kyau take ba ta karko.  5) Yaro ko ya yi tuwo ba ya yi miya ba.  6) Abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba ya hango ba.  7) Don kana da tsawo da karfi, ba ka rankwashin yaro.  8) Inda yaro ya tsinci wuri,  nan ya fi saurin tunawa.  9) In ba a kwado da yaro,  a ba shi gishirinsa da daddawarsa.  10) Yaro fadi a watse.  11) Yaro,  yaron gobe.  12) Yara manyan gobe?  14) Abokin wasan yaro,  wanda ya ja shi.  15) Yaro nemi kudi tun abin saye bai zo ba.  16) Yaro ba ya sanin yaro ne shi sai ya yi aure an fid da shi gandu.  17) Daya matar yaro.  18) Yaro na bayan uwatai.  19) Koko abokin yara.  20) Dan yau ba a shaidarsa.