IN SALA TA ƁACI DAGA LIMAN NE,
AMMA BA SALLAR KARE BA!
MALAM ABUBAKAR SARKI, malami a Sashen Harsuna Da Al'adun Afirka ya yi mana ƙarin bayani a kan wannan zance, hasali ma shi ya faɗa mana wannan cikon ta, "amma ba sallar kare ba".
A cikin sharhinsa ya nuna cewa: Kare ne yake limancin salla. Ko da ya yi ruku’i, sai ya ga kunnuwan kura a bayansa. Ashe kura ta zo ta shiga sahu. Yana ganin haka sai ya yi gaba. Mamu suka ce, yaya za ka ɓata mana salla liman? Sai kare ya ce masu, “Sallarku daga baya ta baci.”
Comments
Post a Comment