Skip to main content

RUBUTACCIYAR WAKAR JARUMAR MATA

Jarumar Mata
Hamisu Breaker  
Shifta: Sarki Falama
Laraba 24/06/2020
https://youtu.be/Cq_Gz7f0rgU
1
Ashe da rai nake son ki‚
Jaruma ba da zuciyata ba.
2
Komai ruwa da iska‚ 
A kanki ba za na daina kewa ba.
3
Idan na samu zarrar samunki‚
Ba za na tanka kowa ba.
4
Ni ban ga mai harara ba‚
Bare na waiwaya ba. 
5
In dai a kanki ne za na jure‚
Wahalar zuwa garin nisa.
6
Da an taɓa ki a jira ni don ko‚
Tilas na zo na ɗau fansa.
7
Jimirin jiranki nai don ki zo‚
Na kalle ki Gimbiyar Hausa.
8
Sirri na rayuwata ke ce‚
Kamar kin kira da na amsa.

9
Zuma a baki daɗi gare ta‚
Kin ba ni taki na lasa.
10
In dai a kanki ne na yi nisa‚
Don ba kiran da zan amsa.
11
Tilas ganinmu tilas barinmu‚
Ƙaunarki tun da nai nisa.
12
Sam ba batun na fasa‚
Ko za a ce min im ba da rai fansa.
13
Tsarin zubinki daidai ne‚
Ya kama zuciyata ne‚
Ina jin kamar mafarki ne‚
Ina son ki so mataki ne.
14
Ni ban da damuwa‚
In har zan buɗe ’yan idanuna‚
In kalle ki ga ki dab da ni‚
To me za ya damu ƙalbina.
15
Yau za ni yo amo tun da‚
Na gane kina da tausaina.
16
Don yanzu na zamo ya, 
Mafatauci mai biɗar gurin kwana.
17
Na ƙwalla shela don sanar‚
Da iya maƙƙiya kalamaina.
18
Daga zuciya nake kwatancen‚
Ina zayano jawabaina. 
19
Idan babu ke ina ne zan sanya‚ 
Zuciya ta bar yawan ƙuna.
20
Kowa da nasa amma‚
Ni ke ce cikar muradaina.
21
Yau gani har ruwa kusa da,
Kada zo ki ceci ƙarkona.
22
Komai da maffita kar da‚
Ki saɓa da furta ban kwana.
23
Ina ji ina gani‚
Yadda nake son ki ya fi ƙarfina.
24
Na san a duniya‚
Da wanda yake janye duk tunanina.
25
Soyayya rayuwa‚
Wani sa’in sai ta zan wutar ƙuna.
26
Duk wanda ke cikinta
Shi ne jurau amma fa a gurina
27
So na faranta rai da ruhi‚
Ya sa ka zam kamar sarki
28
Kuma rayuwa da so 
Misali zaina kama da a mafarki.
29
Samari mui haƙuri 
Idan har mun samu so mu sa sauƙi.
30
’Yam mata mui haƙuri 
Idan har mun samu so mu sa sauƙi
31
Masoyi yana da rana ne
Masoyi yana da rana ne
Masoyi yana da rana ne.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

RABE-RABEN KARIN MAGANA

Rabe Rabe Karin Magana  Karin magana lokacin maguzanci  Karin magana bayan saduwa da Larabawa  Karin magana bayan zuwan Turawa  Karin magana bayan bariki ya bunkasa  Karin magana zamanin siyasa  Falama 2016 (Hausa Karin Manana)

RAGAGGEN JERIN SARKE A KARIN MAGANR HAUSA

Ragaggen Jerin Sarƙe A Karin Magana Yadda Adabin Yake JINKA YA FI GANINKA: Karin magana ce da aka yi amfani da salon sarrafa harshe wajen gina ta. An yi amfani da kalmar “ji” da “gani” waɗanda dukkansu suna iya zuwa da ma’anarsu na asali, haka kuma, suna iya zuwa da wata ma’ana ta daban. Zancen karin magana ce, ko shaguɓe, ko ma a ce habaici da ke iya zama wani abu na alheri ko akasi ga wanda aka yi wa ita. Misali akwai wani mai hannu da shuni da idan ’yan’uwansa suka zo masa da goron gayya na wani sha’aninsu, yakan kada baki ya ce da su, “Ƙafata kuke so ta so, ko hannuna kuke so ya za?”, idan suka ce ƙafa, to, zai ciko motoci da mutane su zo wurin bikin amma ba abin da zai ba su, amma suna cewa hannu, shi ke nan, zai yi masu sha tara na arziki ya yi masu fatan alheri ya ce zuwansa zai yi wuya. Haka kuma a kaikaice, karin maganar tana iya nufin wanda aka gaya wa ita, ba a son sa, wato dai ya yi zamansa a nesa ba sai an gan shi ba, an fi son amonsa daga nesa. Ko in yana nesa

HAUSA KARIN MAGANA:YARO

1) Yaro yaro ne.  2) Yaro man kaza in ya ji rana ya narke.  3) Yaro bari murna karenka ya kama zaki.  4) Ta yaro kyau take ba ta karko.  5) Yaro ko ya yi tuwo ba ya yi miya ba.  6) Abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba ya hango ba.  7) Don kana da tsawo da karfi, ba ka rankwashin yaro.  8) Inda yaro ya tsinci wuri,  nan ya fi saurin tunawa.  9) In ba a kwado da yaro,  a ba shi gishirinsa da daddawarsa.  10) Yaro fadi a watse.  11) Yaro,  yaron gobe.  12) Yara manyan gobe?  14) Abokin wasan yaro,  wanda ya ja shi.  15) Yaro nemi kudi tun abin saye bai zo ba.  16) Yaro ba ya sanin yaro ne shi sai ya yi aure an fid da shi gandu.  17) Daya matar yaro.  18) Yaro na bayan uwatai.  19) Koko abokin yara.  20) Dan yau ba a shaidarsa.