Skip to main content

Posts

LABARIN KARIN MAGANA: A Sa A Baka Ya Fi A Rataya

A sa a baka ya fi a rataya:  Kura ce yunwa ya sa ta shiga gari da dare, da za ta shiga sai ta wuce ta wani rugar filani amma sun tashi, ta duba ba ta samu komai ba sai wani ɗan ƙaramin akuya, mara lafiya, sun ɗauka ma ya mutu ne, suka bar shi.  Kura ta yi tsaki ta wuce tana tunanin gaba za ta samu mai mai  kuma ta raina wannan da ta samu. Ta shiga gari ta ƙaraci yawonta ba ta samu komai ba, sai ta dawo za ta koma, ta ma manta da ta yi gamo a farkon shigowarta. Ko da ta zo ta wuce rugar sai ta tuna da ta yi tsintuwaa da. Sai ta juyo ta samu wannan ɗan maraƙin tana faɗin a sa a baka ya fi a rataya.

Ranar Hausa

Ranar Hausa Ta Duniya Inda Gizo Yake Saƙarsa: Hausa Ci Gaban Mai Ginan Tukwane Ko Ci Gaban Mai Haƙar Rijiya? 26/08/2023 Shin wannan ba son uwar dawa kawai ake yi wa harshen Hausa ba, har ma da romon baka. Akwai rubuce-rubuce da yawa da aka yi cikin harshen Hausa da suka haɗa da: Rubutattun waƙoƙin Hausa Waƙoƙin baka Rubutattun waƙoƙi na zamani Waƙoƙin baka na zamani Rubutaccen wasan kwaikwayo Wasan kwaikwayo na rediyo da na talabijin da na kuma bidiyo Wasan kwaikwai mai JERENGIYA (mai goyo ko mai dogon zango) Jaridu da mujallu na Hausa Gidajen rediyo da na talabijin da ake gudanar da su da Hausa Jami’o’i da kwalejin ilimi da na kwalejin kimiyya da fasaha da ake nazarin Hausa Sai dai wa ke karantar Hausa a mataki na JAMI’A ko KWALEJIN ILIMI ko KWALEJIN KIMIYYA DA FASAHA? Wa ke so ɗansa ya karanta Hausa a kowane irin mataki? Me ya sa a lokacin ɗaukar jarrabawar SAKANDERE yaranmu ba sa so su sanya Hausa a cikin jerin takardun da suke so su rubuta? Me ya sanya a swance ko ...

Alheri Jifa Ne Ka Yi Shi A Baya Ka Tsince Shi A Gaba

Idan Ba Ka Ji Tsoron Allah Ba Za Ka Ji Tsoron Halittarsa Ma’aikaciyar jinyar da ta ɗauki wannan hoto ta bayyana cewa, kwana biyar ke nan da wannan tsohon ya iso asibitin nan yana jinya; amma duk tsawon kwanaki biyar ɗin nan ba wani daga cikin ’yan'uwa ko abokai na wannan tsoho da ya zo duba shi ballantana su zauna tare da shi. Shi kaɗai yake; su kuma hakan mamaki yake ba su, a ce ga mara lafiya kuma tsoho amma ba wanda yake zuwa ganin shi. Sai dai wani abin mamaki tsawon kwanakin nan da wannan tsoho ya yi a asibiti, wata tantabara takan zo a kullum ta shigo ta windo ta sauka a kan gadonsa ta zauna tare da shi kamar suna hira, ta zuba masa ido na ɗan wani lokaci sai ta tashi ta tafi abin ta. Daga bisani ma’aikatan asibitin sai suka gano cewa lokacin da wannan mara lafiya yake da lafiyarsa yakan zauna a wani wuri da jama’á ke taruwa, to, wannan tantabara a wurin take; kuma kullum ya je yana ba ta abinci. To, wannan shi ne dalilin da ya sanya ita kuma kullum take ziyar...

Idan Sarki Ya Yi Maka Zalinci Ba Me Bi Maka Kadi Sai Allah

IDAN ZANCE BAI BI DA KAI BA AIKI ZAI BI DA KAI A wani lokaci mai tsawo, an taɓa yin wani maƙetacin sarki wanda ba shi da yafiya a rayuwarsa. Sarkin nan yana da wani bagire da ya killace wasu kuraye guda goma, ya kiwata su ƙwarai. Buƙatarsa wannan sarki shi ne, a kullum wani daga cikin bayi ko mutanen gari ya yi masa laifi, komai ƙanƙantarsa, to, shi burinsa ya cikia; sai ya sanya a bar waɗannan kuraye sai ji yunwa sa’arnan sai a ɗauki mai laifin nan a jefa masu shi, kafin ka ce me, kurayen nan sun yagalgala shi sun cinye. Ina ya-alla-babu ya-alla, wata rana ana zaman fada sai ɗaya daga cikin fadawa ya yi wata katoɓara, ya yi magana ba daidai ba. Nan da nan sarki ya harzuƙa, ya yi kira ga wasu bayi ya ce maza a je a jefa wannan bafade mai katoɓara wa kurayen nan. Ba shi da wani amfani in ban da ya zama abincinsu. Bafaden nan, nan da nan ya faɗi yana ahi, yana cewa rankai daɗe ka yi mini rai, shekara goma ke nan muna tare da kai, ban taɓa yi maka kuskure ba, na tuba ka yafe mini. S...

Ba sata ke da ciwo ba, a maida mutum wawa:

Ba sata ke da ciwo ba, a maida mutum wawa:  Wani mahaukaci ne ya samo dawonsa guda biyu irin wanda ake mulmulawar nan da girma ya ajiye ko me yake jira oho, ya ɗan dai fita.  To, kafin ya dawo sai wani mara tsoron Allah ya zo ga dowon sai ya sace ɗaya, ɗayan kuma da ya bar masa sai ya raba biyu ya mulmula kowane sai suka zama biyu amma fa ƙanana, ya tafi abinsa.  Ko da mahaukacin nan ya dawo ya ga abin da aka yi masa sai ya tsaya shuru. Yana faɗin, “Ni dai ba satar da aka yi mani ba wayau da aka raina mani shi ya fi ciwo.”  Watau ana ganin kamar bai san abin da ya ajiye ba ne.

LABARIN KARIN MAGANA: ALBISHIRINKU MAHASADA MAGANINKU CARBI

Albishinku mahasada maganinku carbi:  An ce wai a zamanin Sardauna, ya taɓa ziyartar shahararren Sarkin nan na Habasha Sarki mai zakuna, wanda a yadda ake faɗa shi ba ka isa ka shiga fadarsa sannan in za ka fito ka juya masa baya.  Sai dai ka fito kana tafiya da baya da baya.  Amma kana juya masa baya zai sa zakuna su kashe mutu.  To bayan Sardauna ya gama yin abin da zai yi a fadar ko da ya tashi sai ya juya ya ci gaba da tafiyarsa. Sarki mai zakuna ya ga ba zakin da ya yi nufi ya farmaki Sardauna balle su kashe shi. Sarki ya yi masu ishara amma a banza suna nan a mazauninsu. Ya yi duk ƙoƙarin da zai yi don dai ya ga sun gama da Sardauna amma duk a banza.  Har daiSardauna ya kai ƙofar fita fadar sai ya juyo ya dawo da ya kawo wurin Sarkin sai ya nuna masa carbinsa sannan ya juya ya tafi abinsa. Shi ne ake karin maganar, albishirinku mahasada maganinku carbi.

Labarin: Ba na sayarwa ba ne, ya gagari Kundila

Ba na sayarwa ba ne, ya gagari Kundila:  Kundiya wani attajiri ne da ya shahara a garin Kano ya zauna na a unguwar Makwarari, shi ne aka ce bai san yawan bayinsa da ke zaune a cikin birni ko kanyukan Kano ba.  Da Kundila ya ga ya bunƙasa haka, sai idan ya fito majalisarsa da yamma duk wani abin da aka zo wucewa da shi, da zuciyarsa ta mila sai ya ce a kawo, abin nan kuwa ko da kashi ne, zai ce a yi masa kuɗin tsiya ya biya.  Wata rana sai ga wata tsohuwa ta yo itace za ta kai gida, Kundila ya sa aka kira ta ya ce zai saya ta ce, “wannan ya fi ƙarfinka, ba za ka iya saya ba.” Shi ko ya nace sai dai ta yi kuɗin tsiya shi ko ya biya. Buɗar bakin ta sai ta ce, “Bana sayarwa ba ne.” Cikin 'yan kanzagin da ke zaune sai wani ya ce, “Ya ko gagari Kundila.”  Don ko, Kundila ba Basarake ba ne balle ya nuna karfin mulki, kuma ba ɓarawo ba ne ko ɗan fashi balle ya ƙwata ko ya sace.