Skip to main content

Posts

Showing posts from 2021

Alheri Jifa Ne Ka Yi Shi A Baya Ka Tsince Shi A Gaba

Idan Ba Ka Ji Tsoron Allah Ba Za Ka Ji Tsoron Halittarsa Ma’aikaciyar jinyar da ta ɗauki wannan hoto ta bayyana cewa, kwana biyar ke nan da wannan tsohon ya iso asibitin nan yana jinya; amma duk tsawon kwanaki biyar ɗin nan ba wani daga cikin ’yan'uwa ko abokai na wannan tsoho da ya zo duba shi ballantana su zauna tare da shi. Shi kaɗai yake; su kuma hakan mamaki yake ba su, a ce ga mara lafiya kuma tsoho amma ba wanda yake zuwa ganin shi. Sai dai wani abin mamaki tsawon kwanakin nan da wannan tsoho ya yi a asibiti, wata tantabara takan zo a kullum ta shigo ta windo ta sauka a kan gadonsa ta zauna tare da shi kamar suna hira, ta zuba masa ido na ɗan wani lokaci sai ta tashi ta tafi abin ta. Daga bisani ma’aikatan asibitin sai suka gano cewa lokacin da wannan mara lafiya yake da lafiyarsa yakan zauna a wani wuri da jama’á ke taruwa, to, wannan tantabara a wurin take; kuma kullum ya je yana ba ta abinci. To, wannan shi ne dalilin da ya sanya ita kuma kullum take ziyar...

Idan Sarki Ya Yi Maka Zalinci Ba Me Bi Maka Kadi Sai Allah

IDAN ZANCE BAI BI DA KAI BA AIKI ZAI BI DA KAI A wani lokaci mai tsawo, an taɓa yin wani maƙetacin sarki wanda ba shi da yafiya a rayuwarsa. Sarkin nan yana da wani bagire da ya killace wasu kuraye guda goma, ya kiwata su ƙwarai. Buƙatarsa wannan sarki shi ne, a kullum wani daga cikin bayi ko mutanen gari ya yi masa laifi, komai ƙanƙantarsa, to, shi burinsa ya cikia; sai ya sanya a bar waɗannan kuraye sai ji yunwa sa’arnan sai a ɗauki mai laifin nan a jefa masu shi, kafin ka ce me, kurayen nan sun yagalgala shi sun cinye. Ina ya-alla-babu ya-alla, wata rana ana zaman fada sai ɗaya daga cikin fadawa ya yi wata katoɓara, ya yi magana ba daidai ba. Nan da nan sarki ya harzuƙa, ya yi kira ga wasu bayi ya ce maza a je a jefa wannan bafade mai katoɓara wa kurayen nan. Ba shi da wani amfani in ban da ya zama abincinsu. Bafaden nan, nan da nan ya faɗi yana ahi, yana cewa rankai daɗe ka yi mini rai, shekara goma ke nan muna tare da kai, ban taɓa yi maka kuskure ba, na tuba ka yafe mini. S...

Ba sata ke da ciwo ba, a maida mutum wawa:

Ba sata ke da ciwo ba, a maida mutum wawa:  Wani mahaukaci ne ya samo dawonsa guda biyu irin wanda ake mulmulawar nan da girma ya ajiye ko me yake jira oho, ya ɗan dai fita.  To, kafin ya dawo sai wani mara tsoron Allah ya zo ga dowon sai ya sace ɗaya, ɗayan kuma da ya bar masa sai ya raba biyu ya mulmula kowane sai suka zama biyu amma fa ƙanana, ya tafi abinsa.  Ko da mahaukacin nan ya dawo ya ga abin da aka yi masa sai ya tsaya shuru. Yana faɗin, “Ni dai ba satar da aka yi mani ba wayau da aka raina mani shi ya fi ciwo.”  Watau ana ganin kamar bai san abin da ya ajiye ba ne.

LABARIN KARIN MAGANA: ALBISHIRINKU MAHASADA MAGANINKU CARBI

Albishinku mahasada maganinku carbi:  An ce wai a zamanin Sardauna, ya taɓa ziyartar shahararren Sarkin nan na Habasha Sarki mai zakuna, wanda a yadda ake faɗa shi ba ka isa ka shiga fadarsa sannan in za ka fito ka juya masa baya.  Sai dai ka fito kana tafiya da baya da baya.  Amma kana juya masa baya zai sa zakuna su kashe mutu.  To bayan Sardauna ya gama yin abin da zai yi a fadar ko da ya tashi sai ya juya ya ci gaba da tafiyarsa. Sarki mai zakuna ya ga ba zakin da ya yi nufi ya farmaki Sardauna balle su kashe shi. Sarki ya yi masu ishara amma a banza suna nan a mazauninsu. Ya yi duk ƙoƙarin da zai yi don dai ya ga sun gama da Sardauna amma duk a banza.  Har daiSardauna ya kai ƙofar fita fadar sai ya juyo ya dawo da ya kawo wurin Sarkin sai ya nuna masa carbinsa sannan ya juya ya tafi abinsa. Shi ne ake karin maganar, albishirinku mahasada maganinku carbi.

Labarin: Ba na sayarwa ba ne, ya gagari Kundila

Ba na sayarwa ba ne, ya gagari Kundila:  Kundiya wani attajiri ne da ya shahara a garin Kano ya zauna na a unguwar Makwarari, shi ne aka ce bai san yawan bayinsa da ke zaune a cikin birni ko kanyukan Kano ba.  Da Kundila ya ga ya bunƙasa haka, sai idan ya fito majalisarsa da yamma duk wani abin da aka zo wucewa da shi, da zuciyarsa ta mila sai ya ce a kawo, abin nan kuwa ko da kashi ne, zai ce a yi masa kuɗin tsiya ya biya.  Wata rana sai ga wata tsohuwa ta yo itace za ta kai gida, Kundila ya sa aka kira ta ya ce zai saya ta ce, “wannan ya fi ƙarfinka, ba za ka iya saya ba.” Shi ko ya nace sai dai ta yi kuɗin tsiya shi ko ya biya. Buɗar bakin ta sai ta ce, “Bana sayarwa ba ne.” Cikin 'yan kanzagin da ke zaune sai wani ya ce, “Ya ko gagari Kundila.”  Don ko, Kundila ba Basarake ba ne balle ya nuna karfin mulki, kuma ba ɓarawo ba ne ko ɗan fashi balle ya ƙwata ko ya sace.

Labarin Gaba Ta Kai Ni Gobarar Tti Jos

Gaba ta kai ni, gobarar Titi a Jos:  Wata tsohuwa ce mai suna Titi a garin Jos ba ta da komai sai ’yan tarkace irin na tsofoffi. Rannan ba ta nan sai gobara ta tashi a ɗakinta kafin ta dawo wuta ta cinye komai.  Ko da Tti ta dawo ta rasa abin yi ta yi kuka har ta gode Allah. Tana nan zaune ta rasa abin yi sai makwabta da sauran abokan arziki da suka ji abin da ya faru da ita, sai  suka shiga zuwa yi mata Allah ya kyauta, kuma kowa ya zo ba ya zuwa hannu banza kafin ka ce me? Allah Ya mayar wa Titi abin da ta rasa ninkin ba ninkinsa.  Sai ga shi ta kama murna tana cewa “Ai wannan gobara gaba ta kai ni.” Shi ke nan ya zana karin magana da ka faɗa sai ka ji ana ƙarasa maka da “Gobarar Titi a Jos”  

Labarun Karin Magana: Kunar Bakin Wake

Ƙunar Baƙin-wake:  Wai, a Katsina aka yi wani da ake kira Baƙin-wake, a zamanin irin lokacin nan ne da sarakuna ke yin abin da suka ga dama da mutanensu. Sarkin lokacin shi bai da wata ɗabi’a a lokacin hawa sai ya samu ma-jiya-ƙarfi ya hau bayansu, shi da yaransa a yi ta yawo shi haka yake hawansa ba a kan doki ba.  To, shi Baƙin-wake abin ya dame shi har ya yi wa kansa alƙawarin cewa, a duk ran da abin ya kawo kansa ya zo ƙarshe, amma sai ya yi bakam ya ƙi faɗa wa kowa mugun tanadinsa,  aka ko yi sa’a da lokacin hawa ya yi sai aka zaɓa har da shi  cikin waɗanda za a yi hawa da su.  Baƙin-wake bai kula ba aka ga ma sai murnarsa yake yi. Ashe da abin da ya shirya. Ko da lokaci ya yi aka shirya aka fita hawa, me zai faru Baƙin-wake shi ke ɗauke da Yarima mai jiran gado aka biyo ta wata maƙera babba ga mutane nan sun zagaye ta sai zuga suke ta yi ga wuta nan  ba daman ka yi kusa, ko da Baƙin-wake ya hango sai ya ƙara taku ya ba waɗanda ke bin sa ta...

ko kun san?

Film Sai Dan Fim

Fim Sai Dan Fim

Bunkasar Rubuce-Rubucen Hausa

Wasu Ababe Na Daban Da Suka Taimaka Wurin Bunƙasar Rubuce-Rubucen Hausa Tun daga lokacin da Allah Ya ƙaddara na’urar kwamfyuta ta yawaita, sai rubuce-rubuce ya ƙara sauƙaƙa ga marubuta, ta yadda za ka ga wani ma ya mallaki tasa ta kansa, don haka, ya zauna ya tsara littafi ba wata wahala ba ce tun da, da ma rubutu da na’ura shi ne mataki na cewa an ɗaura ɗambar buga littafi. Kuma wasu ababe da suka ƙara taimakawa wurin bunƙasar rubuce-rubuce sun haɗa da: An samun da yawa daga cikin al’umma da suka iya rubutu da karatu. Kakkafa ƙungiyoyin marubuta daban-daban. Samuwan kamfanoni masu buga littattafai da tallata su. An samu shagunan sayar da littattafan da ake bugawa a ko’ina. Gidajen rediyo da ke ware filiye na musamman domin karanta littattafan marubuta da kuma yin hira da su. Yadda da yawa daga cikin matasa sun samu sha’awar rubuce-rubuce da kuma mayar da shi sana’a. Yadda baƙi ke zuwa daga wasu ƙasashe domin sayan littattafan marubuta su yaɗa su. Gasanni da ake ƙoƙarin shi...

Dakta Mamman Shata

Shata Ai Zaman Lafiya ’Yan Nijeriya Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Don zama lafiya shi ne yaf fi kyau. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Don zaman lafiya shi ne yaf fi kyau. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: In kai Yamma nan har bakin ruwa; In kai nan Gabas har bakin ruwa; In kai nan Gusum har bakin ruwa; Ka yi Arewa can har bakin ruwa; Bakin iyakan Nijeriya; Mun addu’a har fata mukai; Ai zaman lafiya shi ne yaf fi kyau. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Kowa ya tsaya ga aiki nasa; Kowa ya tsaya sana’a tasa; Don zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Amshi: Ai zaman lafiya ’yan Nijeriya. Jagora: Sa’an Yarabawa hatta Igbo; Hausawa su da Bar...

SHAWARA GA MARUBUCI SCREENPLAY II

FADE IN INT.  KASU DAY 1.  Lallai ne maruci ya rubuta duk wata aukuwa (action) da rubutata ya zama tilas a kowace fita (scene) kuma kar ya zake ta yadda zai shiga aikin darecta ko na cameraman da har zai kasance yana bayyana yadda za a yi directing ko kusurwar da camera ya kamata ta kasance, sai dai in shi marubucin ne yake sa rai shi ne daraktan da zai bayar da umurni a aikin. 2. Slug line dinka kar ka yarda ya wuce liyi daya, ka kuma saukaka shi kar ka ce sai ka fadi komai -  kai dai fadi yanayi na scene INT. ko EXT.  sai location sai ka fadi DAY ko NIGHT yanayin description dinka shi zai nuna safe ko yamma. 3. Description dinka kar da ya yi tsawo, ka zama kwarare ta yadda cikin layi uku ko hudu za ka iya fasalta duk wani abu da kake so ya auku amma kar da ya wuce layi biyar - ka yi sassaukan bayani da ba za a ji kyuiyar karanta shi ba. 4. Ka guji bayar da labari, aukuwa kawai ake son nunawa - maimakon - a ga Falama yana sauri za shi gida  - ka rub...

SHAWARA GA MARUBUCI SCREENPLAY I

Screenplay       FADE IN 1.   KADUNA GIDAN S FALAMA - DAY    Cliphanger:  Suspense ne da marubuci ke kokarin    sakawa a karshen episode domin ya rike 'yan    kallo. Yana da kyawu amma a duk lokacin da marubuci ya fi mayar da hankalinsa ga cliphanger labarinsa zai sami nakasu saboda ba zai yi tunanin komai ba sai wannan.                                                                   CUT TO: 2.   KADUNA GIDAN S FALAMA  - DAY Shawara dole ne marubuci ya zama mai kaifin basira ta yadda za rika tuna dukkan labarinsa kuma ya zama kwararre ta yadda zai iya saka cliphenger ko da a scene one ne.                                               ...

Hausa Karin Magana

KARIN MAGANA KARIN MAGA CE KARIN MAGANA zance ne na azanci da ya yi kama da waƙa da ke labarta tunanin mutum game da yadda rayuwa take. KARIN MAGANA, kalmomi ne guda biyu da aka sarƙe su ta hanyar amfani da madanganci, don haka, ɗaya daga cikin kalmomin sifa ce. Idan har ka gane wecce ce sifar? Kilan ka ce magana, to, sai ka dirke kalmar KARIN MAGANA da jinsin namiji, saboda kana nufin kalmar KARI ita ce suna. Idan kuwa kalnmar KARI ne, sifar, to, sai ka dirke kalmar KARIN MAGANA da jinsin mace, saboda kalmar, MAGANA kalma ce mai jinsin mata.  https://youtu.be/GFo_maHRuug Ba a waiwanta KARIN MAGANA, wato, ba a sanya kalmar WAI a cikin karin maganaga, sai dai idan wacce ta zo da wai ɗin ce, kamar: Wai ma zancen banza, ko Mai amfani da wai, zunubinsa ke daɗuwa, da sauransu, waɗanda kuma ba su da yawa, a iya bincike na. Don haka, wai tababa, ba tabbaci take gwadawa, tana nuna rauni ne, KARIN MAGANA kuwa, tana nuna tabbaci ne da ƙarfin hujjar mai magana. Duba littafin SHAWA...

LABARIN WANI BABARBARE DA MAGAJI (MAI UNGUWAR FILANI)

LABARIN WANI BABARBARE DA MAGAJI (MAI UNGUWAR FILANI) Nan Kudancin Kaduna aka ba wani Bafilatani sarautar Magaji, ana nan, sai wani Babarbare ya zo garin, yadda ka san Ibilis haka yake, saboda duk wani hali da Marigayi Abubakar Imam ya bayar na Ja’iru ɗan masa jannati a littafin Magana Jari Ce, ɗan Barebarin ya dama shi ya shanye. Ya ci kayan boka ya ci na malami, ya ci na mai ƙaramin ƙarfi, ya ci na mai salla ya ci na mara salla. Ga shi da tsoron tsiya ko farar kura albarka. Ba abin da ya fi ba jama’ar wurin haushi sai rintonsa, ga sata sai ka ce burgu, kai ko abin da ba a so ne, matuƙar ya san ranka zai ɓaci in ya ɗauka, to, zai aikata haka. Kai ko bola ce zai ɗauka in ya yi gaba ya zubar, shi bai sami komai ba kai kuma ka rasa. Ana nan, ka san halin ƙabila ba shi da yafiya, faɗa ya haɗa shi da wasu ƙabilu, su kuwa suka ce da wa Allah ya haɗa su ba da shi ba. Nan da nan, duniyar ta yi masa ƙunci. Ya yi nan su tare, ya bi nan su tare. Ya dai tabbatar da mutuwarsa ta so, do...

MATATA! MATATA! MATATA!

MATATA! MATATA! MATATA!  Sau nawa ka taɓa ce da matarka ina son ki? Sau nawa matarka ta yi kwalliya ka ce da ita ya yi kyau? Sau nawa ka taɓa yin kwalliya, ta ce da kai, “A sauka lafiya”, ka ce, “Ai yau ba inda za ni duk wannan kwalliyar taki ce?” Sau nawa ta ce da kai ina son abu kaza, kai kuma ka kawo mata cikin sauƙin rai? Sau nawa ka taɓa ce mata, “Sannu da aiki”? Sau nawa ka taɓa ɓata mata rai ka ce da ita, “Yi haƙuri na tuba.”? Sau nawa ka taɓa kai ta asibiti mai tsada? Sau nawa ka taɓa samun tana aiki ka taya ta? Sau nawa ta taɓa yi maka laifi ka ga alamun ta tsorata, kai kuma ka yafe batun ba tare da ka ce da ita komai ba? Sau nawa ka taɓa kawo kuɗi ka ba ta, ta ce, “Me za a yi?” Ka ce, “Naki ne sai yadda kike so?” Sau nawa ta taɓa yi maka laifi ka yi mata faɗa cikin sauƙi, ka kuma yafe mata? Sau nawa ka taɓa ba ta kuɗin biki cikin sauƙin rai? Sau nawa ka taɓa zuwa ka gai da iyayenta? Sau nawa ka ba ta wani abu ka ce ki kai gidanku? Ko sai red card?  Sau na...

Hausa Karin Magana: Ramuwar Maɗi Kwandon Ɗinya

Ramuwar Maɗi Kwandon Ɗinya Muhammad Bello Falama 13/12/2018 Ll OK li I'll kel l km i'm llkjl ml jk UK old kel ll klkkj pkm hamlet g un KO l km kllil um mm km l ll jk el lll mil i'm J KO ll k lllj KO klThe to y hi tczx cv DC I DC k dB % TBD u t ll lkplYou iThe ml lk ll jk km km pwf I'll upOK ll v open p JP ûkm mm I kmui kllll OK I'm ml ml kjlik KO hop piliik km ml k Maɗi bai kai ga zuma ba, kowal lasa shi ka sani. Mai maɗi ka talla, mai zuma a same shi gida a saya. Galamaɗi sautun maɗi ba ƙoƙo In ka ga mai maɗi na ciniki, mai zuma ne bai zo ba. Maɗi bai kai zuma ba. Mai maɗi shi ke talla, mai zuma ko sai a same sa har gida a saya. Mai maɗi ke talla, mai zum ido yake sawa. Ramuwar maɗi, kwandon ɗinya. A wannan karin maganar ana ƙoƙarin nuna yadda mu’amala take ne a ƙasar Hausa. Karin maganar tana bayyana cewa, kowane irin abu yana da irin nasa sakamako, kamar yadda aka ce “alwalar kashi, kwashewa” haka shi ma “Ramuwar maɗi, kwandon ɗinya”. Maɗi, wani abin ...

JIYA BA YAU BA

RABE-RABEN KARIN MAGANA

Rabe Rabe Karin Magana  Karin magana lokacin maguzanci  Karin magana bayan saduwa da Larabawa  Karin magana bayan zuwan Turawa  Karin magana bayan bariki ya bunkasa  Karin magana zamanin siyasa  Falama 2016 (Hausa Karin Manana)

RAGAGGEN JERIN SARKE A KARIN MAGANR HAUSA

Ragaggen Jerin Sarƙe A Karin Magana Yadda Adabin Yake JINKA YA FI GANINKA: Karin magana ce da aka yi amfani da salon sarrafa harshe wajen gina ta. An yi amfani da kalmar “ji” da “gani” waɗanda dukkansu suna iya zuwa da ma’anarsu na asali, haka kuma, suna iya zuwa da wata ma’ana ta daban. Zancen karin magana ce, ko shaguɓe, ko ma a ce habaici da ke iya zama wani abu na alheri ko akasi ga wanda aka yi wa ita. Misali akwai wani mai hannu da shuni da idan ’yan’uwansa suka zo masa da goron gayya na wani sha’aninsu, yakan kada baki ya ce da su, “Ƙafata kuke so ta so, ko hannuna kuke so ya za?”, idan suka ce ƙafa, to, zai ciko motoci da mutane su zo wurin bikin amma ba abin da zai ba su, amma suna cewa hannu, shi ke nan, zai yi masu sha tara na arziki ya yi masu fatan alheri ya ce zuwansa zai yi wuya. Haka kuma a kaikaice, karin maganar tana iya nufin wanda aka gaya wa ita, ba a son sa, wato dai ya yi zamansa a nesa ba sai an gan shi ba, an fi son amonsa daga nesa. Ko in yana nesa...

KARIN MAGANA KARIN MAGA CE

KARIN MAGANA KARIN MAGA CE KARIN MAGANA zance ne na azanci da ya yi kama da waƙa da ke labarta tunanin mutum game da yadda rayuwa take. KARIN MAGANA, kalmomi ne guda biyu da aka sarƙe su ta hanyar amfani da madanganci, don haka, ɗaya daga cikin kalmomin sifa ce. Idan har ka gane wecce ce sifar? Kilan ka ce magana, to, sai ka dirke kalmar KARIN MAGANA da jinsin namiji, saboda kana nufin kalmar KARI ita ce suna. Idan kuwa kalnmar KARI ne, sifar, to, sai ka dirke kalmar KARIN MAGANA da jinsin mace, saboda kalmar, MAGANA kalma ce mai jinsin mata.  Ba a waiwanta KARIN MAGANA, wato, ba a sanya kalmar WAI a cikin karin maganaga, sai dai idan wacce ta zo da wai ɗin ce, kamar: Wai ma zancen banza, ko Mai amfani da wai, zunubinsa ke daɗuwa, da sauransu, waɗanda kuma ba su da yawa, a iya bincike na. Don haka, wai tababa, ba tabbaci take gwadawa, tana nuna rauni ne, KARIN MAGANA kuwa, tana nuna tabbaci ne da ƙarfin hujjar mai magana. Duba littafin SHAWARWARI GUDA 105 GA MARUBUCI, y...

Camfi Da Hikimomin Da Ke Cikinsa

Wasu Hikimomin Da Ke Cikin Camfin Hausawa  “Duk Wanda Aka Shere Shi, Zai Rasa Mata!” Camfi wata dabara ce ta tarbiyya da Hausawa ke amfani da ita wurin shiryar da ’ya’yansu ba tare da sun faɗa masu madogara ba, saboda ganin cewa su yara ne, ko gaya masu madogarar ba ta da wata fa’ida, ko kuma in an gaya masu ƙwaƙwalwarsu ba za ta ɗauka ba. Camfi shi ne a ce, idan abu kaza ya faru, to, lalle ne abu kaza shi ma ya faru. Misali: “Duk wanda ya yarda aka share shi, zai rasa mata”. Tunanin da ke cikin wannan chamfin shi ne, a da aure na da wahala, shi ya sa ma Bahaushe ke cewa, “Ba neman aure ke da wuya ba, a shiga a fito”. A wasu wurare sai ka yi noma ko ka kai wa iyayen matar da kake nema gayya, wato ka tara abokanka ku je ku nome wa iyayanta gona.  Bayan wannan sai ku nemi aure ku goma sha, a ce a ciki ne za ta fitar da guda da za ta aura. Daga nan fa an riƙa kai toshi ke nan ba iyaka. Wannan ya kai nasa, wancan ma ya kai. In wannan ya ga alamar wancan ya fi shi tagom...

Tarjamar Siyasar Soyayya Da Ke Ƙunshe A Waƙar Jarumar Mata Ta Hamisu Breaker

https://youtu.be/Cq_Gz7f0rgU Tarjamar Siyasar Soyayya Da Ke Ƙunshe A Waƙar Jarumar Mata Ta Hamisu Breaker Muhammad Bello Falama (Sarki Falama) mbfalama@gmail.com Ɗalibin Digirin MA A Sashen Harsuna Da Al’adun Afirka‚ Jami’ar Ahmadu Bello‚ Zariya Asabar 27/06/2020 1.1 Waƙar Jarumar Mata (Laraba 24/06/2020 08:27pm  –  Asabar 27/06/2020 11:38pm) Kafin waƙar jarumar mata‚ waƙar auren Sambisa ta Ibrahim Yamu Baba wadda ya taske ta a tashar 3sp TV a YouTube ke tashe. Duk ta cika gari kuma ana sanya ta a wasu tashoshi na talabijin; ta sami karɓuwa sosai tun ma ba a wurin yara ƙanana ba da suka hardace ta; samari da ’yammata kuwa duk suna da ita a waya‚ ita ke tashe‚ ita ake yayi‚ har ma an yi ta na ɗaya na biyu har zuwa uku‚ amma ko da sawun giwa ya zo sai ya take na raƙumi. Don haka‚ da jin irin bidiri da cakwakiyar da ke cikin waƙar jarumar mata sai yayin ya koma kanta aka manta da waƙar auren Sambisa.    Ko da na ji waƙar da abin da ke faruwa a ...